Abin da ya sa na tabbatar da sarautar Sarkin yakin Yamma ga Mai kankan – Sarkin Sasa

Sardaunan Yamma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, ya ce ya tabbatar da nada Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan a matsayin Sarkin Yakin Jihohin Yamma ne domin a kawo karshen takaddama tsakaninsa da majalisar Sarkin Hausawan Agege, tare da kauce wa rabuwar kawunan ‘yan Arewa mazauna wannan sashe. Da yake fayyace matsayinsa a kan wannan al’amari cikin […]

Abin da ya sa na tabbatar da sarautar Sarkin yakin Yamma ga Mai kankan – Sarkin Sasa

Sardaunan Yamma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, ya ce ya tabbatar da nada Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan a matsayin Sarkin Yakin Jihohin Yamma ne domin a kawo karshen takaddama tsakaninsa da majalisar Sarkin Hausawan Agege, tare da kauce wa rabuwar kawunan ‘yan Arewa mazauna wannan sashe. Da yake fayyace matsayinsa a kan wannan al’amari cikin zantawa da Aminiya a fadarsa da ke Ibadan, Sarkin Sasa cewa ya yi, “da farko dai ina so ka sani cewa Allah (SWT) shi ne yake bayar da sarauta ga wanda yake so, kuma mafi yawancin jama’a suna sane da irin gudunmawar da marigayi Alhaji Salihu Maikankan, wato mahaifin wannan yaro (Isma’ila Maikankan) ya bayar a lokacin yana raye ta fannin harkokin kasuwancinsa, domin kyautata wa jama’a a Legas da bunkasa tattalin arzikin Najeriya da wasu kasashen Afrika”

“Saboda haka ban ga dalilin da zai hana mu bayar da sarautar ga wannan yaro (Isma’ila Maikankan) ya nema daga gare mu ba, domin ya samu kyakkyawar shaidar yin koyi da halayen mahaifinsa ta fannin taimakon jama’a da hadin kai da ci gabansu.”inji shi.

Sarkin na Sasa ya ci gaba da cewa, a lokacin da wasu Sarakunan Hausawan Legas suka ziyarci fadarsa dauke da sunan wani mutum daban da suke so a nada shi a matsayin Sarkin Yakin Yamma bai amince da wannan bukata ba domin yin haka yana iya haifar da fitina a tsakanin jama’a. “Na nemi su yafe masa laifin da ya yi masu shi kuma na umarce shi ya je ya ba su hakuri, wanda na tabbatar da ya yi hakan. Saboda haka ban ga dalilin hana shi wannan sarauta da muke ganin ya cancata ya same ta ba.”

A hirar Sarkin Sasa da Aminiya cewa ya yi “Alhaji Isma’ila Maikankan ya zo tare da dimbin jama’a domin a nada shi a kan wannan sarauta, bayan tabbatar masa da sarautar sai na tura shi ya je ya roke su su yafe masa abin da ya yi masu. Na hada shi da wasu ‘yan majalisa ta suka tafi tare zuwa fadar Sarkin Hausawan Agege domin na ga cewa shari’a ta amince da yin haka. Duk da yake babu wani kwakkwaran laifi da ya yi musu, amma Sarkin Hausawan Agege ya yafe masa ita kuma majalisarsa ta ki yarda.”

“Bayan aukuwar haka ne sai suka zo da jama’a masu yawa tare da wani mutum da rawaninsa da alkyabba a hannunsa da suke so a nada shi a matsayin Sarkin Yakin Yamma bayan na riga na bayar da wannan sarauta ga wannan yaro (Isma’ila Maikankan). Na gaya musu ban yarda ba domin ba zan yi magana in tayar da ita ba. Ina nan a kan bayanina na farko da na bayar da wannan sarauta ga Isma’ila Maikankan.”

“Na tambayi wanda suke so a nada a kan sarautar cewa me ya sa bai nemi wannan sarauta a tsawon shekaru 30 da muke tare ba. Sai bayan na bayar da sarautar ga wani daban, sannan za ka nemi a baka irin wannan matsayi? Ai ka ga idan muka amince da yin haka girma ya fadi, kuma mun kirkiro hanyar raba kawunan mutanenmu da haifar da fitina a tsakaninsu ke nan. Amma na gaya musu cewa a maimakon haka yana iya neman wata sarauta daban, inda a nan take suka amince da haka.”

“Ganin cewa an kawo karshen wannan takaddama, sai na tabbatar da sarautar Sarkin Bai na Jihohin Yamma ga wannan mutumi. Shi kuma Sarkin Hausawan Agege na amince da nada shi a matsayin mataimakin Sardaunan Yamma, wato mataimaki na. Sai Sarkin Hausawan Idi-Araba da na nada shi a matsayin Garkuwan Jihohin Yamma.”