Abin da ya sa na taso daga gadon asibiti na zabi Buhari – Pasali
Alhaji Danladi Garba Pasali shi ne Shugaban Kungiyar Yakin Zaben Shugaban Kasa Muhammad Buhari ta Buhari Campaign Organization na Kasa. Ya bayyana dalilin da ya sanya ya taso daga kan gadon asibitin da yake jinyar harbin da barayi suka yi masa, ya je ya zabi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar da gabata: […]
Alhaji Danladi Garba Pasali shi ne Shugaban Kungiyar Yakin Zaben Shugaban Kasa Muhammad Buhari ta Buhari Campaign Organization na Kasa. Ya bayyana dalilin da ya sanya ya taso daga kan gadon asibitin da yake jinyar harbin da barayi suka yi masa, ya je ya zabi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar da gabata:
Me ye ya faru game da rashin lafiya da kake yi?
Ainihin abin da ya faru shi ne a ranar Laraba 13 ga Fabarairu, mun shirya za mu bude wata cibiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a nan garin Jos. Wannan cibiya za ta kasance wuri ne, da za a tara bayanan ayyukan Shugaba Buhari. Ta yadda duk wanda yake son ya san ayyukan da Shugaba Buhari ya yi, cikin shekara uku da watanni da ya yi yana mulkin kasar nan, zai iya zuwa wajen ya duba.
Kuma mun shirya a wannan rana Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ne zai jagoranci bude cibiyar.
Don haka na yi sammako na taso daga Abuja da misalin karfe 6 na safe, domin in halarci wannan taro. Mun zo daidai kauyen Bade da ke Jihar Kaduna, sai muka ga wata mota kirar Jeep tana bin mu a baya. Kafin mu farga sai muka ga an bude mana wuta, daga cikin wannan mota. Suka harbe ni a kafa har harsashi ya huda kafar ya fita. Shi kuma direbana suka ji masa raunuka a wurere da dama a jikinsa. Nan take na ga ya suma kuma motar tana gudu. Na rike kan motar, a haka har muka yi tafiyar kilomita daya da rabi. Da motar ta tsaya, sai na nemi taimako daga irin direbobin kananan motocin nan na Bectra da suke wucewa, suka tsaya suka taimaka mana. Aka dauke mu aka kai wani asibiti a Kwoi da ke Jihar Kaduna. Suka ba mu taimakon gaggawa, shi yaron nawa da yake ya fi ni jin raunuka, aka tafi da shi zuwa wani babban asibiti a Keffi da ke Nasarawa. Ni kuma na ce a taho da ni Jos, kuma har yanzu zancen nan da nake yi ina kwance a asibiti.
A ranar da aka gudanar da zaben Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa mun samu labarin cewa an dauko ka daga gadon asibiti, ka je ka jefa kuri’a, me ya karfafa maka gwiwar yin haka?
Wato kai ka san wannan gwagwarmaya kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, gwawarmaya ce da muka fara tun shekara 3 da suka gabata. Domin mun yarda da akida da rayuwarsa. Domin shi mutum ne mai gaskiya da rikon amana.
Don haka ganin cewa wannan zabe yana da muhimmanci ga al’ummar Najeriya, domin a shekara 3 da Buhari ya yi mulkin Najeriya, ya yi yaki da masu cin hanci da rashawa da ’yan ta’adda kuma ya canja akalar ’yan Najeriya daga maganar dogaro da man fetur, zuwa ga harkokin noma da sauran abubuwan da za su taimaka mana.
Shi ne ya sa na ga cewa tunda ina cikin hayyacina, sai na kira babban likitan asibitin da nake kwance, na roki a sani a mota a kai ni in je in yi zabe. Shi ne suka ba ni motar asibitin da ma’aikatansu, aka kai ni wajen da nake yin zabe na yi zabe na zabi shugaba Muhammadu Buhari.
Domin a gaskiya idan ban yi wannan zabe ba, hankalina ba zai kwanta ba. Saboda a wannan gwagwarmaya da muke yi a cikin jihohi 36 da muke da su a Najeriya, babu jihar da ba mu bude ofishi ba. Don haka na je na yi wannan zabe kuma na zauna a wajen, har kusan awa biyu na tabbatar cewa Shugaba Buhari ya lashe wannan unguwa baki daya. Domin zuwana wajen ya karfafa wa mutanen unguwar gwiwa, ganin halin da nake ciki. Don haka mutane kowa ya tashi ya shiga layi ya yi zabe.
Bayan da aka gama zaben aka kirga kuri’ar Shugaba Buhari ya samu kuri’a 776 ita kuma Jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 8 kawai. Daga nan na koma asibitin na ci gaba da yin jinya.
Ganin yadda miliyoyin ’yan Najeriya suka fito wajen zabeN, duk da cewa daga farko an dage da mako daya, me kake ganin ya sanya ’yan Najeriya ba su yi sanyi ba, wajen fitowa?
Ai kamar yadda na fada maka ne tunda farko, duk dan Najeriya dan halal idan ya yi tunanin halin da Najeriya ta shiga a da inda aka rika kashe bayin Allah da sunan Boko Haram da kwashe dukiyoyin kasar nan. Aka jefa kasar ta shiga cikin mawuyacin hali. Ya zama wajibi ya mara wa Shugaba Buhari baya.
Bari in fada maka wani al’amari tunda ake siyasa a Najeriya ba a taba zaben Shugaba ba tare da ya ba da wani abu ba, sai a kansa. Shugaba Buhari bai ba wa kowa komai ba, amma duk da haka jama’a suna sonsa suna kaunarsa.
Mutanen Najeriya suna kaunar Buhari ne saboda sun san cewa mutum ne mai gaskiya kuma ya zo ya kafa harsashin gaskiya a Najeriya, don haka dole a tsaya a goya masa baya domin a tabbatar da gaskiyar ta tsaya a Najeriya.
Saboda rashin gaskiya a kasa ne ke kawo fitinu da rashin aikin yi da kashe- kashen kabilanci da addini.
Yaya ka ga yadda Hukumar INEC ta gudanar da zaben?
Wato wannan zabe kusan duk duniya kowa ya amince kuma kowa ya yaba wa Hukumar INEC kan yadda ta gudanar da wannan zabe mai adalci. Domin idan ka duba sakamakon zaben za ka ga babu wata tazara mai yawa tsakanin wadanda suka yi takarar.
Amma irin zaben da PDP take yi a da, zama kawai suke yi suna rubuta sakamakon zabe. Duk masu lura da zabe daga kasashen waje sun yaba. Domin an yi zabe babu tashin hankali babu fitina an bar kowa ya zabi abin da yake so.
A matsayinka na jigo a yakin zaben Shugaba Buhari me za ka ce kan sake zabensa da aka yi?
Dama mu ba mu taba yin kasa a gwiwa ba. Domin tuni mun yi imanin cewa Buhari zai sake cin zaben nan. Domin mutum ne mai gaskiya da rikon amana. Don haka ban taba kasa yin barci ko na kwana daya ba, kan wannan takara da Buhari ya sake fitowa. Domin na san ba zai taba yiwuwa a hada Buhari da Atiku a takara ba, sannan a ce za a zabi Atiku. Kuma ya kamata jama’a su sani ba an kammala zaben ba ke nan, domin akwai masu ra’ayin cewa su Buhari kawai za su zaba. Don haka muna kira ga jama’a su fito su zabi gwamnoni da ’yan majalisun jihohi. Domin idan Buhari bai samu ma’aikata ko abokan aiki ba, ba zai iya aiki shi kadai ba. Don haka mu kara daura damara mu fito mu zabi gwamnoninmu da ’yan majalisunmu na jihohi.
Wasu daga cikin zababbun sanatoci da
Hukumar INEC ta sanar
Kwara Central
Ibrahim Y. Oloriegbe (APC) 123,808 – Winner
Bukola Saraki (PDP) 68,994
Kwara South
Lola Ashiru (APC) 89, 704 – Winner
Rafiu Ibrahim (PDP) 45,176
Kwara North
Umar Sadik (APC) 98170 – Winner
Zakari Mohammed (PDP) 33, 364
Benue South
Abba Moro (PDP) 85,162 – Winner
Steben Lawani (APC)47,972
Benue South
Abba Moro (PDP) 85,162 – Winner
Steben Lawani (APC)47,972
Kogi West
Dino Melaye (PDP) 85, 395 – Winner
Smart Adeyemi (APC) 66,901
Kogi Central
Yakubu Oseni (APC) 76,120- Winner
Natasha Akpoti (SDP) 48,326
Borno South
- Ali Ndume (APC) 301,312 – Winner
Kulda Sarunmari (PDP) 84,692
Jigawa North
Ibrahim H. Hadeija (APC) 184,185 – Winner
Ubale Shittu (PDP) 103,039
Jigawa North-West
Danladi Sankara (APC) 286,655 – Winner
Nasiru Roni (PDP) 120,314
Jigawa Central
Sabo Nakudu (APC) 224,543 – Winner
Mustapha Sule Lamido (PDP) 143,611
Edo North
Francis Alimekhena (APC) 117,783 – Winner
Abubakar Momoh (PDP) 80,752
Abia North
Orji Uzor Kalu (APC) 30,580 – Winner
Mao Ohuabunwa (PDP) 21,940
Kano Central
Ibrahim Shekarau (APC) 506,271
Aliyu Sani Madaki (PDP) 267,778
Kano South
Kabiru Gaya (APC) 319,004 – Winner
Abdullahi Sani Rogo (PDP) 217,529
Kano North
Jibrin Barau (APC) 286,419 – Winner
Ahmad Bichi (PDP) 155,638
Kano North
Jibrin Barau (APC) 286,419 – Winner
Ahmad Bichi_ (PDP) 155,638
Nasarawa West
Abdullahi Adamu (APC) 115,298 – Winner
Bala Ahmed Aliyu (PDP) 85,615
Nasarawa North
Umaru T. Almakura (APC) 113,156 – Winner
Suleiman Adokwe (PDP) 104,595
Oyo South
Kola Balogun (PDP) 105,720 – Winner
Abiola Ajimobi (APC) 92,218
Gombe Central
Danjuma Goje (APC) 110,116 – Winner
Nasiru Abubakar Nono (PDP) 39,155
Gombe North
Saidu Ahmed Alkali (APC) 152,546 – Winner
Hassan Dankwambo (PDP) 88,016
Gombe South
Amos Bulus (APC) 80,549 – Winner
Binta Bello (PDP) 63,312
Kaduna South
Danjuma La’ah (PDP) 268,287 – Winner
Bala Banted (APC) 133,923
Kebbi South
Bala Ibn Na’allah (APC) 136,187 – Winner
Benjamin Wikki (PDP) 62,733
Osun West
Lere Oriolowo (APC) 102147 – Winner
Lere Oyewumi (PDP) 97,294
Niger North
Aliyu Sabi Abdullahi (APC) 161,420 – Winner
Muhammad Sani Duba (PDP) 77,109
Table UKEOMA MODESTUS
Wasu daga cikin zababbun sanatoci da
Hukumar INEC ta sanar
East
Sani Musa (APC) 229,415 – Winner
Ishaku Ibrahim (PDP) 116,143
Niger South
Bima M. Enagi (APC) 160,614 – Winner
Shehu Baba Agaie (PDP) 90,978
Yobe South
Ibrahim M. Bomo (APC)118,729 – Winner
Mohammed Hassan (PDP) 89,049
Yobe North
Ahmad Lawan (APC) 144,099 – Winner
Sheriff Abdullahi (PDP) 53,443
Yobe East
Ibrahim Geidam (APC) 139,277 – Winner
Abba Gana Tata (PDP) 18,059
Ondo Central
Ayo Akinyelure (PDP) 67,994_ – Winner
Tayo Alasoadura (APC) 58,092
Wasu daga cikin zababbun sanatoci da
Hukumar INEC ta sanar
Imo west
Rochas Okorocha (APC) 97,762 – Winner
Jones Onyereri (PDP) 63,117
Akwa Ibom South
Akon Eyakenyi (PDP) 122,412 – Winner
Nelson Effiong (APC) 44,053
Katsina Central
Kabir Barkiya (APC) 340,800 – Winner
Hamisu Gambo Danlawan (PDP) 124,372
Katsina North
Ahmad Babba Kaita (APC) 339,438 – Winner
Mani Nasarawa (PDP) 127,52
Katsina South
Bello Mandiya (APC) 433,139 – Winner
Imam Shehu Inuwa (PDP) 158,081
Ogun Central
Ibikunle Amosun (APC) 88,110 – Winner
Titi Oseni-Gomez (ADC) 37,101
Ekiti South
Dayo Adeyeye (APC) 77,621 – Winner
Biodun Olujimi (PDP) 53,741
Ekiti Central
Opeyemi Bamidele (APC)94,297 – Winner
Obafemi Adewale (PDP) 46, 707
Ekiti North
Olubunmi Adetunbi (APC) 60,689 – Winner
Duro Faseyi (PDP) 49,209
Adamawa North
Ishaku Cliff (PDP) 43,117 – Winner
Binta Masi Garba (APC) 16,219
Adamawa Central
Aishatu Dahiru (APC) 188,526 – Winner
Mohammed Chubado (PDP) 96, 530
Osun Central
Ajibola Bashiru (APC) 132,821 – Winner
Ganiyu Olaoluwa 106,779
Ebonyi North
Sam Egwu (PDP) 80,711 – Winner
Mathias Adum (APC) 38,374
Ebonyi Central
Obinna Ogba (PDP) 62,452 – Winner
Julius Ali-Ucha (APC) 46,676
Ebonyi South
Michael Ama Nnachi (PDP) 103,751 – Winner
Prince Nweze Onu (APC) 19,663
Akwa Ibom North-East
Bassey Albert (PDP) 147,731- Winner
Bassey Etim (APC) 60, 930.
Anambra Central
Uche Ekwunife (PDP) 18,412 – Winner
Bictor Umeh (APGA) 14,403
Osun East
Adenigba Fadahunsi (PDP) 114,893 – Winner
Ajibola Famurewa (APC) 105,720
Lagos West
Solomon Olamilekan (APC) 23,189 – Winner
Mr Gbadebo Rhodes (PDP) 16,248
Lagos Central
Oluremi Tinubu (APC) 131,735 – Winner
Onitiri Dabid (PDP) 89,107