‘Abin da ya sa na tuba daga bangar siyasa’
Wannan matashi da ke zaune a Unguwar Rimi, Kaduna kuma tsohon dan bangar siyasa da aka fi sani da ’Yan-shara ya bayyana wa Aminiya dalilan da ya sa ya tuba daga bangar: Mene ne sunanka?Sunana Aminu Umar, amma an fi sanina da dan-Amana, ina zaune ne a Unguwar Rimi, Kaduna. Mece ce sana’arka?Ni dai na […]
Wannan matashi da ke zaune a Unguwar Rimi, Kaduna kuma tsohon dan bangar siyasa da aka fi sani da ’Yan-shara ya bayyana wa Aminiya dalilan da ya sa ya tuba daga bangar:
Mene ne sunanka?
Sunana Aminu Umar, amma an fi sanina da dan-Amana, ina zaune ne a Unguwar Rimi, Kaduna.
Mece ce sana’arka?
Ni dai na kammala makarantar sakandare amma ba ni da aikin yi takamaimai, domin an koyar da mu karatu ne ba a koyar da mu sana’ar hannu ba. Shi kuma aikin gwmanati sai da wani mai tsaya maka ba wanda ya cancanta ba. Kuma wanda yake da takardar sakandare ai a matsayin akawu zai fara aiki in har ya samu mai tallafa masa. Sannan ba zai wuce matsayin akwun nan ba har ya yi ritaya, sannan ya shiga wahalar jiran gawon-shanu wato jiran fansho. Don haka nake kira ga gwamnati ta taimaka ta tallafa wa matasa domin rashin aikin ne ke kawo matsala a cikin garin Kaduna da kasa baki daya inda sunaye ake samun eriya-boys da ’yan-daba da ’yan-shara da’yan-kalare da ’yan Ecomog da sauransu. Yawanci in an kamala makaranta ba abin yi ga wadanda suka ci jarabawar gaba amma ba su da halin ci gaba da karatu mai tsada a kasar nan shi ne ummul-haba’isin shiga wadannan harkoki. Yawan matasa da ba su samu ci gaba in sun kammala makarantar sakandare shi yake tusnduma su shiga harkar amfani da makamai don bangar siyasa. Domin an ce da babu gara ba dadi. Shi yake sa zaman banza a layi, fadace-fadace da sauran miyagun abubawa da shi kansa mai aikata su ba a son ransa yake ba. Idan kowa na da aikin yi, ba wanda zai yi zaman banza. Saboda manya da kananan shugabanni sun danne mu, ba sa yin adalci, ba su san kowa ba sai kansu da ’ya’yansu.
Da gaske ne ana ba da abin sa maye kafin a fita kamfe?
kwarai kuwa ana bayar da kayan maye iri-iri don a gusar da hankali har ake kaiwa ga aikata mugun abu.
Yanzu ka farka ka daina bangar siyasa, me za ka ce ga matasan da ba su tuba ba?
kwarai kuwa domin na yi tunani na ga in ba lokacin zabe ne ya zo ba, ba a neman matasa. Su kuma ba su ganuwa balle su ba da “fansho” wato kudi. In zabe ya zo sai a nemi matasa domin su yi sharar-hanya suna dauke da makamai da sanduna sannan da an ci zabe an watsar da su ke nan. Don haka ina kira ga matasa su farka, duk matashi ya tashi ya rika zuwa makaranta yana koyon sana’a domin yin hakan ya fi domin ci gaban kansa. Sannan duk wanda ya san mun yi masa aiki ko wadansu matasa sun yi masa aiki, to ya waiwaya ya biya “fansho” ko ya koya musu sana’a sannan ya ba su jari don su zama na kwarai.
Me ya sa kake kiran su daina yin bangar siyasar ko an ci moriyar ganga ne an yarda kwaure?
Na lura cewa abokaina da tsautsayi ya fada musu suka samu rauni lokacin kamfe an tafi an bar su ba lafiya suna jinya ba gudunmawar kudin asibiti ko na magani ko na abinci ballantana uwa-uba na tuwo kain ko ruwan fiya-wata ruwan leda da za su sha babu. Domin duk dan siyasa yana gayyatar matasa ne yaran masu neman abin sawa a bakin salati wato talakawa su yi masa sharar-hanya su kewaye shi lokacin kamfe, ba sa zuwa da iyalansu wato matansu da ’ya’yansu maza ko mata. Don haka na farka na ce ni dai na dawo daga rakiyar bangar siyasa ko ’yan-shara kamar yadda ake fadi a Kaduna.
Kana da kira ga gwamnati da masu hali don kawar da wannan aikin assha?
Gwamnati ta koyar da yara sana’o’i tun suna makaranta, wanda suka kammala makaranta a koya musu sana’a. Sannan duk wanda ya iya sana’a, a ba shi kayan yin sana’ar, in kuma da hali a samar da babban wuri na koyar da sana’o’i da ba su wurin da za su yi sana’a da wutar lantarki don su baje kolin kayan. Ka ga an zaunar da su wuri guda kuma an samu lafiya.
Mene ne kiranka ga masu sa matasan yin banga?
Su biya fansho ga matsan da suka yi aiki da su. Sannan su daina amfani da yara suna saya musu kayan maye ba gaira ba sabar. Kuma ina kira ga matasa su cinye duk kudin da aka ba su don su je su yi banga sannan su ki zuwa taron siyasar. Sannan in an ce su mayar da kudin da suka karba, su ce sai in wanda yake takara ya kawo yaransa a sa su a gaba, su ma sun sha abin mayen da suke saye don a je da su su yi bangar. Wannan ne kadai zai kawo karshen bangar siyasar. Ni dai na daina na shiga harkar neman na kaina.