Abin da ya sa na yi shiru kan rikicin ’yan Shi’a – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi magana a kan rikicin ’yan Shi’a da sojojin Najeriya ba, sai ya samu rahoton binciken ’yan sanda da na gwamnatin Jihar Kaduna.Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba, lokacin tattaunawarsa ta musamman ta farko da aka watsa a gidajen talabijin da rediyoyin kasar nan.Shugaba […]

Abin da ya sa na yi shiru kan rikicin ’yan Shi’a – Buhari
Abin da ya sa na yi shiru kan rikicin ’yan Shi’a – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi magana a kan rikicin ’yan Shi’a da sojojin Najeriya ba, sai ya samu rahoton binciken ’yan sanda da na gwamnatin Jihar Kaduna.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba, lokacin tattaunawarsa ta musamman ta farko da aka watsa a gidajen talabijin da rediyoyin kasar nan.
Shugaba Buhari wanda ce, ba zai yiwu kungiyar Shi’a ta kafa gwamnati a cikin gwamnati ba, ya ce zai jira rahoton kwamitin binciken rikicin da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya kafa kafin ya dauki mataki a kai.
“Tabbas na san wani abu a kan lamarin, saboda na ji abin da ya faru. Lokacin da rikicin ya faru na rika tuntubar Gwamnan Jihar Kaduna; kun san ya faru ne a jiha daya daga cikin jihohi 36. Kuma abin sha’awa Shugaban kasar Iran ya yi mini magana a kan batun. Kuma na shaida masa cewa a matsayinmu na gwamnati muna da tsari. Lokacin da ya faru a daya daga cikin biranen jihar, Gwamna ya ziyarci wurin da kansa. Muna da tsari na bincike. Sojoji da lamarin ya shafa suna da tsarinsu na bincike. Kuma a matsayina na Shugaban Gwamnatin Tarayya wajibi ne in jira rahoto kafin in fito in yi magana.”
Shugaba Buhari ya kara da cewa: “Na bari sojoji da Gwamnatin Jihar Kaduna su mika rahotanninsu na bincike. ’Yan sanda da SSS duk da cewa lamarin bai shafe su kai-tsaye ba, su ma suna da nasu aiki da tsarin mulki ya ba su na gano abin da ya haddasa matsalar. Abin da na sani shi ne ko ’yan sanda ko sojoji ko hukumomin farar hula, idan aka samu asarar rayuka da lalata dukiya, akwai tsararriyar hanya ta gudanar da bincike; ta dogara da yadda matsalar ta kai. Idan ta yi matukar muni za a kafa kwamitin bincike na musamman… sannan a bukaci mutane daga kowane bangare su zo su bayar da shaida.”
“Ta yaya wata kungiya za ta kafa tata gwamnatin a cikin kasa? Ba na son in yi magana a kan batun sosai a yanzu. Ya fi dacewa in bari sai na ga rahoton binciken. Amma akwai abubuwa da dama da na gani, inda wasu kananan yara suke kokarin dukan kirjin wasu Janar-Janar, sun sanya shinge a hanya suna barazanar za su jefe su da duwatsu,” inji shi.
Game da ko hankalinsa ya tashi, Buhari ya ce: “Sosai ma, amma dole in lura da matsayina don haka na zuba ido.”
Kan ko ya damu game da yawan mutanen da aka rasa, ya ce: “Ba za ka dubi yawa kawai ba. Akwai bukatar a yi wa kowane bangare adalci, don haka wajibi ne mu jira sakamakon binciken, sannan ka shaida wa jama’a. Misali na ji wasu mutanen Zariya suna yi wa manema labarai bayani a Kaduna, ko ba haka ba ne? Kimanin kwana biyu zuwa uku da suka gabata sun kira manema labarai suka shaida musu wahalar da suke ciki cikin shekara biyar zuwa 10.”
“Don haka ina jiran rahoton kwamitin bincike daga Gwamnatin Jihar Kaduna, saboda rikicin ya faru ne a jihar, a daya daga cikin biranenta, kuma kungiyar tana can fiye da shekara 20 daga abin da na karanta a jaridu, sun mamaye manyan hanyoyin tarayya, wani lokaci daga Kano zuwa Kaduna. Wannan shi ne abin da na ji, amma abin takaicin ban taba ganin irin wannan abin bakin ciki ba.”
Da yake amsa tambaya kan ko suna da rahoton sirri kan inda ’yan matan Chibok suke, Shugaba Buhari ya ce, har zuwa yanzu babu wani rahoton sirri kan inda sama da ’yan matan makarantar Chibok 200 da ’yan Boko Haram suka sace a watan Afrilun shekarar 2014 suke. “Wannan shi ne abin da nake nema. Muna neman shugabannin ’yan Boko Haram na hakika da za su gamsar da mu cewa ’yan matan suna raye. Idan wani dan Boko Haram ya fito ya ce shi ne jagora kuma ya san inda ’yan matan Chibok suke ba za mu yi saurin gaskata shi ba. Irin bayanan da nake nema daga kasashen Nijar da Chadi da Kamaru, ina tabbatar muku batun ’yan matan Chibok na zukatanmu ne kawai saboda dalilai na tausayawa. Amma babu wani rahoton sirri kan inda wadannan ’yan mata suke ko kan halin da suke ciki, abin da muka hakkake daga bayanan sirrinmu shi ne (’yan Boko Haram) suna ta zarya da su ne ta yadda ba za a shammace su ba, har zuwa loacin da za a kwato ’yan matan, ba su ajiye su a wuri daya.”
Shugaban kasar ya ce, gwamnati a shirye take ta fara tattaunawa da wadanda aka tabbatar shugabannin Boko Haram ne, inda ya ce a baya an rika samun masu da’awar su shugabannin Boko Haram ne daban-daban.
“Har yanzu kofarmu bude take idan aka samu shugabannin Boko Haram na gaskiya, wadanda za su shaida mana cewa ga inda wadannan ’yan mata suke, a shirye muke mu tattauna da su ba tare da gindaya wasu sharudda ba. Mun sha fadin haka, amma a ina suke rike da ’yan matan Chibok, kada su dauka ba za mu iya kare sauran sassan Najeriya ba ne.”
 Game da dalilin da ba za a saki tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki da jagoran neman kasar Biyafara Nnamdi Kanu ba, Shugaba Buhari ya ce ba za a sake su ba ne saboda barnar da suka tafka ga kasar nan.
 “Idan kuka dubi barnar da wadannan mutane suka tafka ga kasar nan, za su iya karya beli. Duba tsohon Shugaban kasa (Jonathan) ya rubuta wa Gwamnan Babban Banki ya ce ya bayar da Naira biliyan 40 ga wane da wane, sannan ya bayar da asusun ajiya, sannan ka sake shi (Dasuki) ya je ya ga likitocinsa a Landan, yayin da kimanin mutum miliyan biyu suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira wasu ko iyayensu ba su sani ba. Sannan wannan da kuke kira Kanu ko kun san yana da fasfo biyu ne daya na Najeriya daya na Birtaniya; kuma ya zo kasar ne ba tare da ko daya ba? Ko kun san ya shigo da na’urori kasar nan yana watsa shirye-shiryen rediyon Biyafara? Wace irin gwamnati ce kuke jin za ta lamunci kyale irin wannan mutum. Akwai dabi’ar cin amanar kasa a tare da shi, kuma ina fata kotu za ta saurari shari’arsa.”
Shugaba Buhari ya kuma ce idan aka ci gaba da amfani da hijabi ana hallaka jama’a, ta yiwu a hana sanya hijabin. “Idan wannan lamari (harin kunar bakin wake) ya ci gaba, kuma aka gano hijabi ne matsalar, zai zamo gwamnati ba ta da zabi face ta dauki mataki a kai. Zai zamo mutane za su zabi tsakaninsa da tsaron lafiyasu,” inji Buhari.
Sai ya ce  a shirye yake ya kori duk ministansa da aka samu da almundahana ko cin hanci da rashawa.
Shugaba Buhari ya kuma ce ba ya goyon bayan a karya darajar Naira, inda ya ce: “Ni a kashin kaina ba na goyon bayan karya darajar Naira. Mun mika mulkin kasar nan tana zaune kalau a 1979, amma zuwa 1984 ba wanda ya san nawa ake bin Najeriya bashi. Lamarin yanzu ya dada tabarbarewa sakamakon faduwar darajar man fetur.”