Abin da ya sa na yi wa Buhari juyin mulki —IBB
Babangida, wanda shi ne babban hafsan sojin kasa a lokacin Buhari, ya taka rawar gani a juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Shehu Usman Shagari a 1983 da kuma na 1985 da ya kawo shi kan karagar mulki.

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (murabus) ya bayyana dalilin da ya hambarar da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a 1985.
Janar Babangida ya bayyana dalilin da gwamnatinsa ta karya darajar Naira da sauran sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta yi bayan kifar da Buhari.
Babangida, wanda shi ne babban hafsan sojin kasa a lokacin Buhari, ya taka rawar gani a juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Shehu Usman Shagari a 1983 da kuma na 1985 da ya kawo shi kan karagar mulki.
Ya ba da cikakken bayani game da abubuwan da suka faru a cikin littafin tarihin rayuwarsa da ya ƙaddamar a makon jiya.
- Har yanzu Najeriya na buƙatar shugabanni nagari – Sheikh Gumi
- NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri
Littafin na Babangida ya haifar da cece-kuce, game da muhimman batutuwan da suka dabaibaye mulkinsa na shekaru takwas, musamman soke zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni; kashe babban dan jarida, Dele Giwa; da kuma kashe Manjo Janar Mamman Vatsa bisa zargin yunkurin juyin mulki.
“Juyin mulkin 1985 ya zama dole.”
A babi na shida, Babangida ya ba da hujjar juyin mulkin da aka yi wa Janar Buhari a 1985. Ya bayyana cewa juyin mulkin martani ga korafe-korafen ’yan Najeriya da kuma tabarbarewar al’amurana kasar.
Ya ce, “A farkon shekarar 1985, ’yan Najeriya sun fara fargaba game da makomar kasarmu. Al’amarin ya kasance mai hadari kuma yana cike da munanan alamun a fili da hatsarin da ke yanzu.
“A bayyane yake ga shugabancin sojojin cewa aikin da muka yi da nufin ceto ƙasarmu a shekarar 1983 ya watse,” kamar yadda Janar Babangida ya rubuta.
Ya ce rashin daukar mataki zai kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin sojoji, wanda a ganinsa hakan zai haifar da mummunar illa ga kasar.
“Idan sojojin suka yi samu rabuwar kai, al’ummar za su bi sahu, kuma abin da zai biyo baya zai zama mai ban tsoro ne da ba za a iya tunani ba,” in ji shi.
A cewarsa, a shekarar 1983 sojoji sun hambarar da Shugaba Shagari ne cikin haɗin kai, amma sai aka fara samun rarrabuwar kawuna tsakaninsu.
“Sojoji, a matsayinsu na waɗanda aka sani da hadin kai, sai ga shi an fara samun guna-guni; down haka ya zama dole a yi wani abu don kada mu rasa kasar.
“Babban abin da na ji tsoro shi ne, rarrabuwar kawuna da ra’ayi a tsakanin sojoji na iya haifar da bangaranci a tsakaninsu. Idan kuma aka bari a ci gaba da samun gindin zama, to akwai hatsarin gaske.”
Ya zargi Buhari da mataimakinsa Birgediya Janar Tunde Idiagbon da mayar da mayar da sojoji saniyar ware, tare da daukar tsauraran matakan kama-karya wajen tafiyar da mulki.
“Sun dauki kansu kamar wasu waliyyai, inda suka kawo wa sojoji bakin jini a wurin al’ummar kasa. Suna take hakkin al’umma tare da cin zarafi babu kakkautawa,” in ji Babangida.
A cewarsa gwmanatin sojin Buhari ta yi mulki ne ta hanyar tsoratarwa maimakon sanya ’yan kyakkyawan fata a zukatan al’umma.
“Kamata ya yi mu Inganta rayuwarsu mu sa musu kyakkyawan fata cewa rayuwarsu za ta inganta. Amma maimakon haka sai aka yi ta kafa musu dokokin kama-karya.
“Sai aka wayi gari gwamnatin da aka kafa da niyyar cimma muradun bai-ɗaya na sojoji, ta koma ta wasu ’yan tsirarun mutane masu taurin kai,” in ji Babangida.
Taɓarɓarewar tattalin arziki
Ya bayyana cewa tsarin musayar kaya na gargajiya da Buhari ya koma amfani da shi ya kara kassara tattalin arzikin Najeriya.
Ya ƙara da cewa lalacewar tattalin arziki da guna-gunin ’yan kasa kan matsin rayuwa na daga cikin abin da suka sa su hambarar da Buhari.
Ya ce, “Kamar yawancin juyin mulkin soja, mun yi ne sakamakon yawan korafe-korafen jama’a. Talakawa sun shiga matsanancin matsin rayuwa, ga shi yanayin tattalin arziki sai kara ta’azzara suke yi a kulla-yaumin.
“Kayayyakin masarufi da sauran bukatun yau da kullum sai karanci suke kara yi.
“Sannan ku a komawa amfani da tsohuwar hanyar yin ciniki ta hanyar musayar kaya a kasuwancin kasa da kasa yana nufin cewa ba a kama hanyar kawo karshen matsalolin tattalin arziki a tsakanin al’umma ba.
Dokokin kama-karya, sun tauye ’yancin walwalar jama’a, ga kuma hukunci mai tsauri, in ji shi.