Abin da ya sa na zabi aikin jarida a rayuwata — Halima Djimrao
Aikin jarida aiki ne mai daraja da girma a cikin al’umma.
Hajiya Halima Djimrao tsohuwar ma’aikaciyar Muryar Amurka ce da a yanzu take aiki da sashen Podcast na Aminiya.
A zantawarta da wakilinmu, ta bayyana yadda ta taso da gwagwarmayar da ta sha da burin da tasa a gaba:
Tarihinki
To, ni dai sunana Halima Djimirao, ni ’yar asalin Jamhuriyar Nijar ce, an haife ni a garin Maine-Soroa a yankin Diffa a ranar 27 ga watan Yulin 1965.
Yanzu shekaruna 56 a duniya kuma Allah Ya azurta ni da ’ya’ya biyu maza, Hassan Farouk Kane mai shekara 22 da Ismael Almamy Kane mai shekara 18.
Na taso a gidan yawa, wato iyayena mata hudu ne, ina da ’yan uwa maza da mata, wadanda muke uwa daya, da kuma wadanda mahaifinmu ne daya. Mun fi arba’in a gidanmu.
Yadda kika yi karatu
Na yi karatu daga firamare zuwa jami’a a Yamai, Babban Birnin Jamhuriyar Nijar, sannan na je Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife inda na ci gaba da karatu har matakin digiri na biyu. Na karanta Ingilishi.
Yadda kika fara aiki zuwa matakin da kike
Na fara aikin jarida tun a shekarun 1990, na fara ne da rubutu a Jaridar Amfani, bayan wani lokaci da aka bude rediyo sai na fara gwadawa kadankadan, sai rediyon ta rinjayi jaridar, har ma na daina rubutun gaba daya.
Daga Amfani na samu tafiya gidan rediyon Muryar Amurka, kasancewar akwai alakar aikin hadin gwiwa tsakanin VOA da Amfani.
Kalubale da kika fuskanta
A rayuwa, mutum ba zai ce babu kalubale ba, ba za a rasa ba komai kankantarsa.
Ita rayuwar ma kanta kalubale ce mai zaman kanta, ballantana kuma a kara da zama da jama’a da kuma aiki da jama’a.
Zan iya cewa babban kalubalen da na fuskanta shi ne samun kaina a wata bakuwar kasar da komai nata ya bambanta da tawa kasar, gaskiya na ci kwakwa, kafin in saba da zaman Amurka, kafin in fara jin dadin zaman kasar na dauki lokaci mai tsawo.
Nasarorin da kika samu
Gaskiya, galibi in an yi min tambaya a kan nasarori, ban san me zan fada ba, amma ina ganin zan iya cewa, a ganina, babu nasarar da ta wuce lafiya da wadatar zuci, sai kuma aikin da na yi a Muryar Amurka har tsawon shekara 20 tare da mutane daban-daban.
Na yi ritaya don radin kaina, kuma na rabu lafiya da abokan aiki, ina ganin wannan nasara ce babba. Kuma an samu daukaka daidai gwargwado, Alhamdulillah.
Shekaru kusan talati ana damawa da mutum a harkar aikin yada labarai, ai nasara ce da ba ma zan iya misaltawa ba.
Me ya sa kika zabi aikin jarida?
Ina ga hakan, wato zabin aikin jarida ba zai rasa nasaba da akidar gwagwarmaya ba tun a jami’a. Gwagwarmayar fada da rashin gaskiya da yaki da rashin adalci da kuma son taimakon marar karfi.
Zan iya karawa da cewa na zabi aikin ne don al’umma ta amfana da ni ta hanyar fadakarwa da ilimantarwa da ma koyarwa da kuma sanar da mutane abubuwan da ba su sani ba da ba su bayanan da ka iya taimaka musu su kyautata rayuwarsu, ko kuma su samu wani canji a rayuwarsu. Aikin jarida wata mabubbuga ce ta koyar da ilimummuka iri-iri.
Aikin jarida aiki ne mai daraja da girma a cikin al’umma.
Kin cim ma burinki na rayuwa ko akwai saura?
Alhamdulillahi, gaskiya babu saura, alhamdulillahi.
Yanzu sai dai shirin Lahira kuma, na fara tattara komatsaina ina shirin komawa ga Allah da fatan gamawa lafiya da duniya da cikawa da imani.
Wane abu ne kika fi alfahari da shi a aikin da kika dade kina yi?
Allah Ya taimake ni, na tsare mutuncina, na tsare mutuncin aikina, na raba kaina da kwadayin abin duniya. Ban yarda in yi wani abu da ka iya zubar min da mutunci ba ko gurbata min da’ar aiki ko kuma bata min sunana.
Duk lokacin da na tuna wannan , ina jin dadi, kuma nakan kara gode wa Allah, kuma kullum ina rokon Allah Ya taimake ni, in dore a kan wannan turba har mutuwa.
Yaya kike ganin matasa masu tasowa a yanzu?
A gaskiya matasa masu tasowa na lura suna fama da rawar kai da kuma gajen hakuri. Suna so su girma nan da nan, yadda na karanci matasa, gaggawa da rashin hakuri ke hana su cim ma burinsu.
Nakan fada musu cewa su yi hakuri, kuma duk wanda suka ga ya yi nasara a rayuwa, to sai dai ya yi hakuri, sai da ya jure wa abubuwa da yawa.
Wace shawara za ki ba su game da rayuwa?
Su zama masu hakuri. Su zama masu wadatar zuci.
Su daina saurin kai kansu inda Allah bai kai su ba. Babu abin da gaggawa da rashin hakuri suke haifar wa mutum, sai nadama da da-na-sani. Su zama masu gaskiya da rikon amana.
Game da sabon aikinki, mene ne Podcast?
Shi dai Podcast, ba wani sabon abu ba ne a kasashen Turai. A kasashenmu na Afirka ne sai yanzu aka fara mayar da hankali a kai.
Kusan shekara 17 ke nan ko 18 da bullar Podcast a Amurka, wato tun wajejen shekarun 2003 zuwa 2004.
Podcast, za a iya cewa wata hanya ce ta zamani ta sadarwa, ko isar da sako ga masu saurare.
A takaice dai rediyo ne na tafi-dagidanka wanda ya zo daidai da zamanin da muke ciki. Wadansu na cewa rediyo ta Intanet.
Rediyo ne a saukake idan mutum yana da Intanet.
Kasancewar Hausawa suna sauraron rediyo, yaya kike ganin za su fahimci rediyon Intanet?
Sosai ma kuwa za su fahimta, sun ma fahimci abin da ake nufi da shi. Hausawa wayayyun mutane ne, ba gidadawa ba ne, babu abin da ba su sani ba na zamani.
Sun san mene ne Podcast ko rediyo ta Intanet, tun da suna sauraron shiryeshiryen da muke yi na Hausa, wato “Daga Laraba” na makomako da kuma “Najeriya A Yau” a ranakun mako. Akwai kuma na Ingilishi “The Bearing” duk mako da kuma “Nigeria Daily” kuma a ranakin mako.
Yaya ake sauraron Podcast?
Ana sauraron Podcast ne ta kwamfuta ko wayar salula ko IPad da makamantansu.
In dai mutum yana da Intanet zai iya sauraro. Kuma ana hada shirin Podcast ne kamar yadda ake hada shirin rediyo, kawai dai bambancinsu, shi shirin Podcast ta Intanet ake sakinsa, kuma yana nan koyaushe mutum ya tashi zai iya zuwa ya sauke ko ya saurara, sabanin shirin rediyo wanda dole ka saurara a lokacin da ake yi, idan ya wuce shi ke nan.
Ga misali ana iya sauraron shirye-shiryenmu na “Daga Laraba” da “Najeriya a Yau” ta shafin Aminiya ta Intanet wato, aminiya.dailytrust.com ko ta facebook.com/aminiyatrust.
Ko ta Buzzsprout ko TuneIn Radio ko Spotify ko kuma Googlepodcasts.
Wadanne kasashe kike je?
Alhamdulillah, gaskiya ba laifi na dan zazzaga, daidai gwargwado na yi tafiye-tafiye; na je Ghana da Togo da Jamhuryar Benin da Mali da Senegal da Najeriya da Moroko da Amurka da Kanada da Faransa da Holland da Turkiyya da Saudiyya.
Wace kasa kike da burin komawa?
Saudiyya, Makka da Madina.
Yaya kike ganin aikin jarida a jiya da yau?
Yanzu aikin jarida ya fi sauki, samun labarai da tantancewa da tabbatar da sahihancinsu ba wuya yanzu, saboda ci gaban zamani, da bunkasar kayan aiki, amma a lokacin da na fara, aikin jarida ya fi wahala, Intanat bai wadata ba, shi ma aikin rediyo yanzu komai ya fi sauki.
Yanzu gyara murya da tacewa da kwamfuta ake yi, ba kamar da ba. A da ana gyara rahoto da reza ko da salatap da sauransu.
Gaskiya da aikin ya fi wuya. Wanda ya yi aikin jarida a da, ba zai sha wahalar aiki yanzu ba. Gaskiya zamani ya kawo sauye-sauye da dama wadanda suka kawo saukin aikin jarida sosai, ba kamar da ba.