Abin da ya sa na zabi zama furodusa —Danhajiya

Fitaccen furodusa a masana’antar Kannywood, Naziru Auwal wanda aka fi sani da Naziru Danhajiya, ya ce dole masu ruwa da tsaki a masana’antar su rika bincike da karo ilimi domin yin gogayya da takwarorinsu. Danhajiya ya bayyana hakan ne a zantawarsa da Aminiya, inda ya ce shi ya zabi zama furodusa ne maimakon darakta ko […]

Abin da ya sa na zabi zama furodusa —Danhajiya

Fitaccen furodusa a masana’antar Kannywood, Naziru Auwal wanda aka fi sani da Naziru Danhajiya, ya ce dole masu ruwa da tsaki a masana’antar su rika bincike da karo ilimi domin yin gogayya da takwarorinsu.

Danhajiya ya bayyana hakan ne a zantawarsa da Aminiya, inda ya ce shi ya zabi zama furodusa ne maimakon darakta ko jarumi domin hakan zai taimaka masa ya koyi zama da mutane.

“Yanzu abubuwa sun canja. Idan ba ka da ilimin zamani, nan gaba fim zai gagare ka.

“A da can mun dogara da faifan CD ne, amma yanzu kasuwar CD.

“Kuma kasuwancin ta wannan bangaren ba zai taba gyaruwa ba.

Da aka tambaye shi hanyoyin da za a bi kai ga gaci, Danhajiya sai ya ce, “Yanzu babu CD, don haka kawai salo za mu canja.

“Mu tsaya mu yi fim masu kyau a kai su sinimomi a haska, sannan mu yi amfani da wasu hanyoyin fasahar zamani ta intanet”, inji shi.

Da aka tambaye shi kan yadda ya zama furodusa maimakon darakta ko jarumi a masana’antar kasancewarsa matashi, sai ya ce, “Na fi son mashiryin fim domin za ka koyi ilimin zama da kowane irin mutum.

“Irin karatu da nake yi daban-daban game da harkar fim da kuma yadda kusan na fi shirya fina-finai da suka shafi matsalolin da suka addabe mutane kai-tsaye. Na shirya fina-finai irinsu Mansoor da Kar ki Manta Da ni da sauransu.”

A game da aikinsa na karshe da kuma wanda zai fito, sai ya ce, “Kar ki manta da ni ne fim din da na shirya na karshe, sai kuma Jarumta da zai fito kwanan nan. Fim din Jarumta zai kayatar matuka”.

Danhajiya ya kuma bayyana cewa shi ba mashiryin fim ba ne kawai, “Ni dan kasuwa ne. Ina noma da kasuwanci.”

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

Tags