Abin da ya sa nake daukar nauyin gyaran fanfo – Ali Rimi

Alhaji Muhammad Ali Rimi wani mutum ne mai kimanin shekaru 40 a duniya. A wannan tattaunawar da Aminiya, dan asalin karamar hukumar Rimi da ke Jihar Katsina, ya bayyana abin da ya sa yake taimakon al’umma ta fuskar shawo kan matsalar ruwan sha da wasu yankunan jihar ke fuskanta ta hanyar gyara duk wani kan […]

Abin da ya sa nake daukar nauyin gyaran fanfo – Ali Rimi
Abin da ya sa nake daukar nauyin gyaran fanfo – Ali Rimi

Alhaji Muhammad Ali Rimi wani mutum ne mai kimanin shekaru 40 a duniya. A wannan tattaunawar da Aminiya, dan asalin karamar hukumar Rimi da ke Jihar Katsina, ya bayyana abin da ya sa yake taimakon al’umma ta fuskar shawo kan matsalar ruwan sha da wasu yankunan jihar ke fuskanta ta hanyar gyara duk wani kan fanfon da ya lalace kyauta. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?
Muhammad Ali:  Da farko dai sunana Muhammad Ali Rimi. An haife ni a shekarar 1975, a unguwar Magangama da ke garin Rimi. Na yi firamare a makarantar da ake kira ‘kaura Abdulkadir’,daga nan na wuce makarantar Sakandare da ke Batagarawa. To bayan na gama waccan sakandaren na kuma yi aikin mota na shekara daya kafin jarrabawarmu ta fito. Kwatsam sai ga demokradiyya ta sake dawo wa,sai kuwa na tsaya takarar  kansila a tsohuwar  jam’iyyar APP, na kuma samu nasara. Sai dai ban hau kujerar ba saboda PDP ta shigar da kara. Saboda rikicin cikin gidan jam’iyyarmu ya sa ba a ba ni takardar kira daga kotu ba a kan karar da aka shigar har sai bayan da kotu ta yanke hukunci a kan karbar kujerar daga wajena ni da wani dan karamar hukumar Mani. Hakan kuma ya faru saboda ban amsa kiran kotu ba. Har daukaka karar da muka yi zuwa Kaduna ba a dai yi nasara ba. To ganin kada a zauna haka nan sai na tafi makarantar kimiya da fasaha ta Hassan Usman, inda na yi karatu a fannin shari’a.
Har ila yau, na yanke shawarar taimakawa ‘yan uwana talakawa musamman gyaran kawunan fanfo da suka lalace ya samo asali daga wani tunani da na yi. Akwai  wata rana ne na koma gida sai na tuna da irin wahalar da muka rika sha a lokacin da muke yara ta nemo ruwan sha da na amfanin gida. A wancan lokaci ana iya tafiyar kusan kilomita biyu wajen neman ruwa,ko kuma a kwashe yini guda wajen jiran ruwan. To unguwarmu Magangami an sanya fanfo amma ya lalace. Waccan wahalar neman ruwan na tuna,kawai sai na ji inje inyi amfani da dan abinda Allah Ya ba ni in gyara fanfan nan,saboda masu bukatar ruwan nan suna da yawa. Kuma tabbas suna shan wahala wajen neman ruwan a yanzu. Hakan kuma aka yi,washegari na nemo masu aiki na biya su aka gyara. To kuma kasan abu na jama’a, idan wani ya kula wani babu ruwan shi. In takaita maka,na gyara wannan fanfo akalla ya kai sau tara. To ganin haka fa, sai ‘yan gawo suka zo suka roke ni da in taimaka su ma in gyara masu na su da ya lalace. Bayan na gyara wannan shi ma fiye da daya,sai kuma wani kan fanfon da ke bayan gidan Inusa Rimi. Daga nan kuma sai na ga irin halin da wannan firamare da na yi take ciki na irin yadda wani sashe na rufin wasu ajujuwan suke. Ni na sayi kwanon rofin aka gyara. Akwai ma mutanen Tsamiya su ma sun nemi gudunmuwa ta gyaran saboda za a sake akalla fiye da takwas na kuma ba su. Akwai garin Kanyar Uban-Daba da ke cikin gundumar Tsagero da a yanzu haka nike cikin shirin gyarawa.
Aminiya: To ba ka tunanin mutane za su ce kana yin wannan ne don siyasa?
Muhammadu Ali: Har ka ba ni dariya. Hakika akwai masu wannan tunanin domin wasu ma har magana suka yi mani kai tsaye ta cewa,tun da na taba tsayawa takara har sau biyu kuma ina ci,yanzu suna kira gare ni da in sake tsayawa kuma ma in nemi kujerar shugaban karamar hukuma. Amsar kawai da na ba su ita ce, wannan kuma yana nan hannun jama’a,domin yanzu jama’a suke zabar wa kansu shugabannin da suke so. Hukunci na nan wajensu, ni dai nawa shi ne, in taimaki wanda na san zan iya taimako walau ya nema ko ni in ga dacewar yin hakan. Kuma da rana daya ban taba fargabar ko don abin da Allah Ya ba ni ba zai ragu ko ya kare. Kuma a nawa tunanin, ba wai neman wani matsayi zai sa ka taimaki jama’arka ba. Yi don Allah shi ne kuma zai saka maka. Anan ne ma nake so in yi amfani da wannan dama in yi kira ga jama’ar kasar nan baki daya,ba wai sai ‘yan siyasa ba. A’a duk wani mai hali da ya fito ya bayar da tasa irin gudunmuwar don ci gaban ko da yankin da ya fito ne, maimakon kowane lokaci mu ce sai gwamnati ta yi mana.