Abin da ya sa nake farautar ‘yan Boko Haram – Zara JTF

Aminiya ta samu tattaunawa da mace mai suna Hajiya Zara JTF wadda ta ce tana cikin sahun farko na matan da suka sadaukar da kansu ga aikin sa-kai da ake kira Sibiliyan JTF a Jihar Borno don yakar Boko Haram. Hajiya Zara JTF wadda a yanzu ta dawo garin Damaturu da wannan aiki na kato-da-gora […]

Abin da ya sa nake farautar ‘yan Boko Haram – Zara JTF

Aminiya ta samu tattaunawa da mace mai suna Hajiya Zara JTF wadda ta ce tana cikin sahun farko na matan da suka sadaukar da kansu ga aikin sa-kai da ake kira Sibiliyan JTF a Jihar Borno don yakar Boko Haram. Hajiya Zara JTF wadda a yanzu ta dawo garin Damaturu da wannan aiki na kato-da-gora ta ce ta shiga wannan aiki ne sakamakon kashe mijinta da ’ya’yanta da ’yan Boko Haram suka yi:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?
Hajiya Zara: To, ni dai sunana Hajiya Zara da aka fi sani da Zara JTF a yanzu, kuma ni haifaffiyar kauyen Kukareta ne a karamar Hukumar Damaturu a Jihar Yobe amma aure ya kai ni garin Benishek a Jihar Borno. Da ’yan Boko Haram suka kashe mijina da ’ya’yana suka tarwatsa garin shi ne na koma Maiduguri.
Aminiya: Shekarunki nawa a yanzu?
Hajiya Zara: To da yake lokacin da aka haife ni ba karatun boko ake yi a gidanmu ba, amma kuma akalla ba zan gaza shekara 67 ba.
Aminiya: Me ya jawo hankalinki kika shiga wannan aiki na kato-da-gora da aka fi sani da Sibiliyan JTF alhali kina mace da shekarunta suka yi nisa?
Hajiya Zara: A hakikanin gaskiya duk da ina mace kuma gyatuma babban abin da ya sa ni daukar gora don yakar ’yan ta’adda da ake musu lakabi da Boko Haram shi ne jin zafin kashe mijina da ’ya’yana da ’yan Boko Haram din suka yi yayin harin da suka kai garinmu na Benishek. Wannan shi ya harzuka ni na yanke shawarar shiga wannan aiki na Sibiliyan JTF don daukar fansa kuma ko yanzu alhamdulillah!
Aminiya: Kamar yaya?
Hajiya Zara: Ah! Dole ne in ce haka mana, domin kuwa na shiga wannan kungiya da farko don ramuwar gayya kuma shiga ta ya sa na ba da muhimmiyar gudunmawa wajen cafke da yawa daga cikin wadannan ’yan ta’adda tare da hallaka da yawa daga cikinsu. Kuma har gobe ba zan yi kasa a gwiwa ba, sai na ga babu sauran masu numfashi a cikinsu.
Aminiya: A baya kin ce kashe mijinki da ’ya’yanki ya sa kika shiga aikin Sibiliyan JTF, a gabanki ne aka kashe su, kuma yaya ke kika tsira?
Hajiya Zara: Lokacin da aka kashe su a gida ne kuma ni ma ina gidan nan (sai ta fashe da kuka), daga nan ni ma sai na fice na bi jama’a zuwa daji don tsira daga bisani ne na koma Maiduguri.
Aminiya: To wane siddabaru kike da shi kina mace wajen gogayya da maza kuma matasa masu jini a jika wajen tunkarar mayakan Boko Haram da ke dauke da miyagun makamai na zamani ke kuma bindigar
gargajiya ke hannunki?
Hajiya Zara: A gaskiya ba wani siddabaru da nake da shi ba, illa neman taimako daga Allah da kuma dan abin da ba a rasa ba na shiga malamai don neman kariya daga miyagu, kuma ma ai duk da ina mace hakan bai hana min gogayya a tsakanin ’ya’yana da yayye da kanne ba, inda an yi gumu da yawa tare da gamayyar sojoji da mu ’yan gora da kuma ’yan ta’addan Boko Haram a bangare guda.
Aminiya: Ko za ki iya fada mana da ina da ina kuka yi gumu da Boko Haram?
Hajiya Zara: Alal hakika mun yi gumurzu da Boko Haram a wurare da dama a cikin garin Maiduguri da manyan sansanoninsu da ke dajin Alagarno kuma duk mun samu sa’a a kansu, don haka sai godiya ga Allah.
Aminiya: To ga shi a yanzu kin baro Maiduguri kin dawo Damaturu da zama me ya jawo haka?
Hajiya Zara: Ba komai ya san na dawo Damaturu ba illa kishi, kasancewar ni ’yar Jihar Yobe ce don haka sai na ga mahaifata ma na bukatar gudunmawata a wannan lokaci wannan shi ne dalili.
Aminiya: Tunda kika dawo Damaturu kin yi wani yunkuri da ya shafi wannan aiki naki?
Hajiya Zara: kwarai kuwa don tun dawo ta Damaturu na yi maganin ’yan kananan barayin da ke addabar unguwar da nake ta Gwange don ba na barci ni da wasu matasa masu kishin kasa muke zagawa da su kuma cikin hakan na kama wasu batagari da hannuna na damka su a hannun jami’an tsaro. Hakan nan bayan fashewar bam na Ranar Sallah da hannuna na kama wata mace goye da bam a bayanta na damka ta ga hannun jami’an JTF.
Aminiya: Ke ba ki tsoron makami ko bam ya tashi da ke yayin damke masu dauke da shi kamar yadda kika ce kin yi?
Hajiya Zara: Haka ne a zahirin gaskiya ban yi tsammani in ina wuri wani abu wai shi bam ko bindiga za ta tashi ba ballantana wata barna ta samu. Kai in Allah Ya so da wuya wani makami ya yi tasiri a kaina.
Aminiya: Ko akwai wani kira da kike da shi ga al’umma da kuma gwamnati dangane wannan aiki naki?
Hajiya Zara: To rokona ga jama’a shi ne su ci ga da addu’ar Allah Ya ba da sa’a ga jami’an tsaro da mu ’yan sa-kai a kan ’yan ta’addan Boko Haram kuma ina roko ga gwamnatin Jihar Yobe da ta samar mana
da makamai masu inganci tare da motar da za mu rika daukar matasa ’yan sa-kai da za su taya ni wannan aiki na yakar ’yan ta’adda, in gwamnati ta yi haka ta yi min komai.