Abin da ya sa nake goyon bayan Buhari ya sake tsayawa takara – Janar Tarfa
Me ya burge ka, ka shiga aikin soja? Ni Janar Paul Tarfa, mutumin Garkida da ke jihar Adamawa, shekarana 76 yanzu. Kuma na shiga aikin soja ne a 1962 bayan na kammala sakandare domin in yi wa kasata aiki, sannan na yi ritaya bayan na shekara 26. Ana tunawa da kai a matsayin wanda […]
Me ya burge ka, ka shiga aikin soja?
Ni Janar Paul Tarfa, mutumin Garkida da ke jihar Adamawa, shekarana 76 yanzu. Kuma na shiga aikin soja ne a 1962 bayan na kammala sakandare domin in yi wa kasata aiki, sannan na yi ritaya bayan na shekara 26.
Ana tunawa da kai a matsayin wanda ya inganta ladabi a NDA, yaya ka yi aiki a NDA?
Girmamawa ce a tura hafsa a matsayin kwamanda a NDA. Domin sai mutumin da ya san aikin soja, yake da ilimi, ya san horarwa, ya kware a aiki. Na ji dadin zaman a wurin, don na ba da ’yar gudunmawata domin ci gaban wadanda ake horarwa.
Wane abu ka fi tunawa da ya faranta maka rai a NDA?
Suna da yawa, don lokacin NDA na tasowa sannan mun samar da hanyoyi masu kyau da dakunan kwana isassu da ruwa da dasa itatuwa, sannan na kula da inganta jin dadin hafsoshi da kurata.
Wadanne abubuwa ne ba ka ji dadinsu ba?
Babu, sai dai daliban wato kadet yara ne ko matasa, in ma an samu wani abin kaico, sai dai tsakanin hafsosi da kurata. Don mun yi kokarin sanya dalibai a kan turba ta kwarai. Kuma lallai ne hafsoshi su horar da dalibai abubuwan kwarai. Don haka ya sa na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, inda na kori wadansu marasa ladabi.
dalibanka sun zama Jana-Janar yanzu, yaya kake ji?
Ni ma a baya ai dalibi ne, in wadanda suka horar da mu suna da rai za su shaida haka. Mun fi wadanda suka horar da mu sannan wadansu da muka horar sun fi mu, domin ci gaban zamani, mun gode wa Allah. Muna ganin abin da suke yi a yanzu, suna kokari, kuma muna murna. Har gobe sojoji suna zuwa su yi gaisuwa su ce ka horar da mu, mun gode. Wannan ne daya daga cikin ribar zama Kwamandan NDA.
Me ya sa aka yi ta kuka lokacin da kake barin NDA?
Na ji dadin wannan tambaya. Daliili shi ne na sama wa jama’a musamman leburori aikin shara da gyaran fulawa da sauransu, kuma sun samu karuwa sosai, shi ya sa suka yi ta kuka don jimamin ko za a kore su daga aiki.
Ka yi Yakin Basasa me za ka ce kan yakin Boko Haram da ya shafi inda ka fito?
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki ne lokacin da mutanenmu suke kusan cire tsammani daga rayuwa. Domin an shiga gidana har sau uku a Garkida, an kashe dangina tara da suka hada da ’yar uwata da mijinta da ’ya’yansu biyu da dan uwana da ya rasa ’ya’ya biyar, an ci zarafin mutane, an kona gidaje, mutane sun watse zuwa daji, wadansu macizai sun sare su, ba makaranta, ba ruwa, ba abinci, ga cututtuka da sauran abubuwan assha. Amma Buhari ya zo ya sa dakarun da suka yi aiki mai kyau a cikin shekara uku an kori Boko Haram. Boko Haram illa ce ga Arewa maso Gabas da Najeriya. Yanzu muna zuwa coci-coci da masallatai babu tsangwama. Buhari yana kokarin tsayar da almundahana da garkuwa da mutane don neman fansa da sauran abubuwan assha. Lallai akwai matsaloli nan da can, sai dai ba kamar na gwamnatin da ta wuce ba. Don me wadansu za su ce kada ya kara neman mulki. Ban tsammaci Buhari ya hau mulki ne don ya warware dukan matsalolin kasar nan ba. Kuma kasar nan za ta ci gaba da fuskantar matsaloli koda bayan ya yi mulkin shekara takwas. Bai dace ana kwallo da ’yan wasa masu hazaka, a ce a sauya su da ’yan ba-ni-na-iya ba, yaya za a yi haka? Duk abin da mutane za su ce wannan ra’ayinsu ne. Ra’ayina shi ne Buhari yana yin aiki mai kyau, kuma lallai ne a bar shi ya ci gaba da aikin da yake yi, domin mulkin dimokuradiyya ake yi kuma ya taka rawar gani kwarai.
Me kake ganin za a yi da kudin da aka karbo daga barayin gwamnati?
Ina fata kudin da aka karbo daga wadannan manyan barayi a yi amfani da su muraran mutane su gani. A gina hanyoyi a duk fadin kasar nan, sannan a rubuta sunan wadanda aka kwato kudin daga hannunsu a gefen tituna don ya zama darasi ga na baya. Yin haka ya fi fadi a kafafen watsa labarai cewa an karbo kudi amma ba a ga abin da aka yi da su ba.
Mene shawararka ga Shugaba Buhari?
Shawarata ita ce, ya nada amintattun mutane domin kula da gina asibitoci da inganta su, wadansu mutane su kula da yin hanyoyi wadansu su kula da yin madatsun ruwa don noman rani domin mutane su kara son sa. Wannan ya fi a karbo kudi daga wurin barayin gwamnati, a bar su a asusun gwamnati gudun kada wasu gafiyoyin su kwashe su. Aiki da kudi ya fi ajiye su, ba na son Hukumar EFCC tana cewa an karbo kudi biliyoyi da tiriliyoyi amma ba a yi aiki da su ba.
Me za ka ce kan wasikun da Cif Obasanjo da Janar Babangida suka rubuta wa Buhari kan kada ya nemi tazarce?
Ya kamata Obasanjo ya gana da Shugaban kasa shi da shi. Kuma ina goyon bayan Buhari ya tsaya takara a karo na biyu, a bar masu zabe su yanke hukunci, idan sun gamsu su kara zabensa, in ba su gamsu ba su ki. Buhari ba zai magance dukan matsalolin kasar nan ba, koda zai yi shekara takwas, matsaloli ba karewa za su yi ba. Game da wasikar Babangida ga Buhari kuwa, ban karanta ta ba. Kuma da gangan na ki karanta ta. Duk wanda ya ce kada Buhari ya sake tsayawa ra’ayinsa ne, amma nawa ra’ayin shi ne ya sake tsayawa domin ci gaba. Lokacin da ya kammala sai wani ya karba daga. Amma bai kamata wani ya ce masa ya tafi ba.