Abin da ya sa nake hada harkar waka da neman ilimi – Mawaki Ahmad Nagudu

Aminiya ta samu tattaunawa da fitaccen mawaki Ahmad Umar wanda aka fi sani da Ahmad Nagudu da ke waka a Jihar Legas. Mawakin ya bayyana dalilan da suka sanya ya koma makaranta, inda a yanzu yake karatunsa a Kwalejin Koyar Da Al’amuran Shari’a da ke Jihar Kano. Ko wane ne Ahmad Nagudu? Ni dai an […]

Abin da ya sa nake hada harkar waka da neman ilimi – Mawaki Ahmad Nagudu
Abin da ya sa nake hada harkar waka da neman ilimi – Mawaki Ahmad Nagudu

Aminiya ta samu tattaunawa da fitaccen mawaki Ahmad Umar wanda aka fi sani da Ahmad Nagudu da ke waka a Jihar Legas. Mawakin ya bayyana dalilan da suka sanya ya koma makaranta, inda a yanzu yake karatunsa a Kwalejin Koyar Da Al’amuran Shari’a da ke Jihar Kano.

Ko wane ne Ahmad Nagudu?

Ni dai an haife ni a unguwar Agege da ke cikin Jihar Legas. A nan na yi makarantar firamare da sakandare, kusan a nan na yi wayo. Iyayena ’yan asalin Jihar Kano ne da ke Arewacin Najeriya. Ita rayuwa babu yadda ba ta zuwa. Haka Allah Ya so amma duk da haka na gode wa Allah da Ya raya ni har na kai ga wannan lokaci.
Shin har yanzu kana gudanar da wakokin Hausa kamar yadda aka sanka?
kwarai kuwa har yanzu ina ci gaba da gudanar da wakokin Hausa amma da yake na koma karatu a yanzu shi ya sa ba a faye jin duriya ta ba. Ina hada waka ne da karatu. Nakan je makaranta sannan kuma idan na dawo na shiga harkokin wakokina. Ka san ita rayuwa haka take, Hausawa sun ce taba kidi, taba karatu. To haka nake yi, na je makaranta na kuma shiga studiyo na yi waka. Haka rayuwar take tafiya. Babu wanda aka bari kuma babu abin da aka fasa. Babu abin da za mu ce sai dai kawai Allah Ya yi mana jagora a cikin harkokinmu kuma ya yi mana albarka a rayuwarmu.
A wace makaranta kake karatu a halin yanzu?
Ina karatu a Aminu Kano School of Legal Studies da ke Kano, wato makarantar koyon aikin shari’a ta Jihar Kano da ke unguwar Gadon kaya da ke cikin birnin Kano. Ina karanta fannin Ingilishi da ilimin sanin yanayi (English/Geography). Ina aji na biyu kuma ina yin NCE ne wato bangaren da yake da alaka da malanta. Haka nake ta yin gwagwarmaya har lokacin da Allah zai kaddara mana lokacin da za mu kammala. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa komai yana tafiya daidai kuma da yardar Allah akwai alamun nasara a cikin lamarin. Don ga shi yanzu har mun kusa kammalawa.
Me ya sa ka yanke shawarar komawa karatu?
Gaskiya dalilin da ya sa na koma makaranta shi ne saboda muhimmancin da ilimi yake da shi a rayuwar dan Adam. Idan mutum ba shi da ilimi ya zama jahili. Saboda haka gani na yi duk abin da mutum zai yi a duniya dole sai da ilimi. Ilimi shi ne gishirin zaman duniya kuma shi ne ginshinkin rayuwa. Saboda haka ko da wakokin da nake yi idan ba ilimi babu yadda zan iya tsara waka. Sannan kuma idan na yi ilimi, basirata da hakazata da zalakata a fannin waka za su karu. Ka san ita waka ba kowa yake iya yin ta ba don jahili ba ya waka sai mai basira da ilimi. Kuma wani abu da na lura da shi dangane da muhimmancin ilimi shi ne zai ba ka damar ka yi mu’amala da mutane a saukake ba tare da wata matsala ba kuma zai sa ka zama wayayye mai hangen nesa. Akwai dalilai da dama wadanda a yanzu ba zan iya kawo su cikin kankanin lokaci ba amma dai wadanda na gaya maka su ne manya-manyan dalilan da suka sanya na koma karatu.
To, a yanzu wane kalubale kake fuskanta a karatunka da kuma sana’arka ta waka?
Gaskiya ina fuskantar kalubale masu yawa. Da farko akwai shi kansa kalubalen daurewa da kuma tsayawa da jajircewa a kan karatun. Don shi karatu yana da cin rai, sai ka yi da gaske idan ba haka ba sai a bar ka a baya. Sannan kuma ga kalubalen dawainiyar yau da gobe, kudin motar zuwa makaranta da kudin abinci da na littattafai da kudin makaranta da sauransu. Ga kuma kalubalen mu’amala da su kansu daliban da malaman da sauran jama’a masu zuwa yin harkoki cikin makarantar. A bangaren waka kuwa ina fuskantar kalubale daga wurin iyaye da kakanni da kuma ’yan uwana. Don da yawa daga cikinsu ba su son harkar wakar da nake yi. Sun fi son na bar ta. Ni kuma a gaskiya ina sha’awarta amma dai ina yin iya bakin kokarina na fahimtar da su kuma ina tabbatar maka da cewa da yardar Allah za su fahimta ba tare da wata matsala ba.
Ta yaya kake hada karatu da waka?
Ka san shi duk abin da kake yi idan ka yi tsari to babu shakka za ka ci ma nasara. Kuma ita waka ta zame mani jiki. Saboda haka yadda nake yi shi ne na ware lokacin karatu da lokacin yin waka. Idan na je makaranta na dawo sai na shiga sutudiyo na yi waka. Nakan yi waka da dare amma mafi yawan lokuta na fi samun damar yin waka ranakun karshen mako.
Mene ne burinka a nan gaba idan ka kammala karatu?
Burina shi ne idan na kammala karatu zan ci gaba da waka kuma za na koma makaranta na ci gaba da karatu. Domin shi ilimi shi ne rayuwa, ba ya karewa har zuwa karshen rayuwa. Saboda haka a lokacin da na kammala karatu zan inganta sana’ata ta waka tare da bunkasa ta. Ina da wakoki da dama da nake yin aiki a kansu amma na san da zarar na kammala karatu zan samu damar da zan fitar da su ba tare wata matsala ba.