Abin da ya sa nake kewar Legas

Hausawa na cewa ‘Duk wanda ya tuna bana, bai ji dadin bara ba’. To amma ni jin dadin bara shi ya sa nake tuna bana, saboda irin rayuwar da na yi a jihar Legas ya sa ba zan taba mantawa da ita ba har abada saboda dalilai masu yawa da suka kunshi bangaren zamantakewa da […]

Abin da ya sa nake kewar Legas
Abin da ya sa nake kewar Legas

Hausawa na cewa ‘Duk wanda ya tuna bana, bai ji dadin bara ba’. To amma ni jin dadin bara shi ya sa nake tuna bana, saboda irin rayuwar da na yi a jihar Legas ya sa ba zan taba mantawa da ita ba har abada saboda dalilai masu yawa da suka kunshi bangaren zamantakewa da tattalin arziki da siyasa da al’adu da kuma harkokin addini.
A lokacin da aka mayar da ni Legas ’yan’uwa da abokan arziki sun yi ta yi mani jaje kamar wanda aka yi wa mutuwa ko kamar aka tura fagen yaki.
Wannan ya sanya na rika tunani iri-iri kan abin da zan je na tarar a can. Kodayake ba shi ne karo na farko da na taba zuwa Legas ba amma dai ban taba zama a cikinta ba na tsawon lokaci. Ina sauka a filin saukar jiragen saman Murtala Muhammed da ke Ikeja sai na ga ya fi filin saukar jiragen saman jiharmu ta Kano da na Abuja. Saboda yadda na ga mutane suna zirga-zirga. Jirage na tashi wasu kuma na sauka babu kakkautawa.
Ba kamar sauran jama’a ba da suka tsani Legas saboda wasu dalilai nasu, ni ra’ayina ya sha bamban da nasu. Kodayake da dama daga cikin su suna cewa sun fi son Abuja a kan Legas saboda rashin cunkoson da Abuja take da shi na mutane da abubuwan hawa. Suna cewa cunkoson ababen hawa kawai ya isa mutum ya tsani Legas. Don a cewarsu duk inda mutum yake son ya je a garin Abuja zai tafi kai tsaye ba tare da wata matsala ba.
Amma ni a ganina Legas wani gari ne wanda ya kebanta da abubuwa masu yawa. Shi ya sa ni a wurina Legas da Abuja wasu garuruwa ne guda biyu da suka sha bamban da juna ta fuskoki da yawa.
Garin Legas wuri ne da mutum zai shakata musamman ma a ranakun karshen makon. Akwai wurare iri-iri kamar bakin teku da wuraren taba-ka-lashe da tande-tande da manya-manyan shagunan sayar da kayayyaki da otel-otel masu karamin kudi da masu tsada. Akwai wuraren raye-raye na zamani da na al’adun gargajiya da ke gudanar da wasanni a kullum. Ai su mutanen da ke zaune a Abuja ba su ne suke korafin cewa garin ba shi da dadi lokacin ranakun karshen makon ba. Amma duk da haka ma’aikata da yawa na tafiya hutun karshen makon zuwa garuruwansu. Watakila mazaunan su ce Abuja ma akwai wuraren shakatawa da otel-otel, to amma a inda gizo yake saka shi ne yaya arharsu ko tsadarsu take.
Zan ci gaba da kewar Legas saboda irin abinci da suke da shi na gargajiya da na zamani. Kamar tuwan Amala da miyar Ewedu da naman Akuya da suke kira ‘Agufe’ ga shinkafar gargajiya da suke kira ‘Ofada Rice’ mai dan karen yaji da miyar kalwa, ga ganda da kifi iri-iri kuma a farashi mai sauki. A Legas za ka iya samun abincin naira dari da nama amma hakan da wuya a Abuja. Ko tasha ka je ba za ka iya samun abincin kasa da naira dari ba. Dangane da gidajen haya kuwa, A legas a iya samun gida daidai da kudinka amma hakan da wuya a Abuja kai ko da gidajen gwarawa ma ka je sai ka ga ya yi tsada idan ka kwatanta da na Legas.
Wani abu da ba zan manta da shi ba a rayuwar Legas shi ne na sufuri. Duk inda za ka je za ka samu motar bas da take bi ta hanyar wurin kan farashi mai rahusa amma a Abuja akwai wurare da yawa da idan za ka je sai dai ka dauki shatar mota don ba ko ina motocin bas ko keke Napep suke shiga ba.
Wasu da yawa za su yi mamaki idan aka ce a Legas ana addini sau da kafa. Ba kamar sauran wurare ba. A Lgeas za ka ga masallaci da coci suna makwabtaka da juna. Kuma ba za ka taba jin an yi rikicin addini ba. Don a Legas za ka ga a gida daya akwai musulmi da kirista kuma ba a wani tashin hankali. Akwai masallatai da yawa da ake yin karatuttutuka. Wato ita rayuwar Legas rayuwa ce guda biyu da ta shegantaka da ta bin Allah sai wacce ka za fa.
Wani abu da zai sa na rika tunawa da Legas shi ne yadda ake auratayya tsakanin kabilu daban-daban da kuma aron al’adu. Za ka bahaushe ya auri bayarabiya ko bayarabiya ta auri bahaushe. Akwai Hausawan ma da za ka ga kusan sun juye sun koma yarabawa ko kuma ka ga bayarabe ya juye ya koma bahaushe.
Hakazalika duk wanda ya zauna a Legas zai zama mai kazar-kazar da kuzari da aiki tukuru. Saboda dan jaridan da yake marar kwazo da matsoraci ba zai iya aiki a Legas ba. Saboda wuri ne na mutane wayayyayu da wayo da dabara. A Legas ne idan za ka yi hira da mutum sai ka biya shi. Ko kuma wani abu zai faru amma sai a samu wasu su rika karbar kudi daga hannun mutane kafin su bari mutum ya kalla. Inda rayuwar Legas ta bambanta da ta sauran wurare shi ne babu yadda za ka samu abu cikin sauki a Legas.
Saboda haka zaman Legas na sanyawa mutum ya zama mai neman na kansa mai zurfin tunani mai ba da muhimamanci ga harkar tsaro. Saboda a Legas ne idan aka kulle gidan da kake haya to ba za a bude ba sai gari ya waye, ko kuma idan aka kulle kofar unguwa ba za a bude maka ba har sai gari ya waye. A Legas za ka biya kudin masu gadi da kudin shara da kudin ruwa da kudin wuta akan kari. Kuma Legas har yanzu duba-gari suna yin aiki kuma gwamnati ta ba su karfi sosai inda a sauran wurare an ma daima labarin duba-gari. Duk da irin kalubalen da ke garin, Legas za ta ci gaba da kasancewa a cikin raina har Abadan abada.