Abin da ya sa nake son tunkude Jonathan – Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce yana neman kujerar Shugaban kasa ne a karkashin Jam’iyyar APC domin ceto ta daga mugun shugabanci na Shugaban kasa Goodluck Jonathan. Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin da yake gabatar da bukatarsa ta son tsayawa takara a […]

Abin da ya sa nake son tunkude Jonathan – Kwankwaso
Abin da ya sa nake son tunkude Jonathan – Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce yana neman kujerar Shugaban kasa ne a karkashin Jam’iyyar APC domin ceto ta daga mugun shugabanci na Shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin da yake gabatar da bukatarsa ta son tsayawa takara a filin taro na Old Parade Ground da ke Abuja, a gaban dubban jama’a ciki har da gwamnonin Jam’iyyar APC.
Gwamna Kwankwaso ya ce zai kawo sauyi wajen magance lalacewar da kasar nan take fuskanta. “Ba a taba karfafa kiraye-kirayen a ceto kasar nan a fili babu boye-boye irin yanzu ba. Kowane bangare na harkokin kasar nan yana dada tabarbarewa; an mayar da harkar mulki na kamun kafa da gazawa da nuna Gadara. Ba na da shakka a zuciyata cewa wannan tafiya mai wahala ce kuma tana cike da kalubale. Amma ban firgita da kalubalen ba. Wajibi ne mu ceto kasarmu, tilas mu fito don ceto kasar nan duk wahala. Tilas mu fuskanta tare da ganin bayan dukkan kalubalen duk yadda suka kai da barazana. Tabbas wajibi ne mu yi haka,” inji Kwankwaso.
Ya ce idan aka zabe shi, babban abin da zai fi mayar da hankali a kai shi ne dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane sako da lungun kasar nan, inda ya ce wajibi ne a kawar da hare-haren Boko Haram da na sauransu. Ya kara da cewa: “Wajibi ne kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu. Idan muka kafa gwamnati ba za mu lamunci zaman firgici ba. Rashin zaman lafiya na karuwa fiye da yadda hankali ke dauka. Abin mamaki mahara marasa kwarewa na ci gaba da kwace birane da garuruwa a Arewa maso Gabas. Darasin da na samu a matsauna na Ministan Tsaro da kuma Mashawarci na Musamman kan yankin Darfur da yaki ya daidaita da kuma Somaliya ya nuna min kare kasa da yaka tare da samun nasara a kan mahara zai samu ne kawai idan aka samar da kwararrun sojoji da ingantattun kayan yaki tare da karfafa musu gwiwa kuma da samar musu da hanyoyin samun bayanan sirri.”
Gwamna Kwankwaso ya ce: “Idan rashin kwarin gwiwa ya hadu da rashin kayan yaki, babu shakka mahara za su rika samun galaba. Kuma duk wata gwamnatin da ta san abin da take yi, wajibi ne ta dauki wannan batu da muhimmanci idan ta dauki kare rayuka da dukiyoyin jama’arta a matsayin babban nauyin da ke kanta. Mun fahimci haka sosai. Don haka wajibi ne mu yi aiki tare, a matsayin abokan hada hannu wajen kafa sabuwar gwamnatin APC domin cimma wannan.”
Kwankwaso ya ci gaba da cewa: “Burinmu na inganta tattalin arziki zai zamo romon baka idan ba za a tabbatar da tsaro da zaman lafiya wajen kai-kawon jama’a da kayayyaki ba. Dakatar da wadannan kashe-kashe ba wai yana bukatar wani gagarumin ilimin kimiyya ba ne. Samar da na’urorin leken asiri da watsa su yadda ya kamata da kuma samar musu da kwararru kuma jami’an da ake karfafa musu gwiwa zai iya samar da haka. Kuma tabbatar da cewa wadanda aka kama da hannu an gabatar da su gaban shari’a yana da muhimanci.”
Ya ce abu na biyu da zai fi ba muhimmanci, shi ne yaki da almundahana da rashawa wanda ya ce ya zamo kamar sankara a tsarin rayuwarmu.
Yayin da Gwamna Kwankwaso, ya soki Shugaba Jonathan da yin amfani da kabilanci da bambancin addini yana lullubewa da karewa da karfafa almundahana da rashawa a harkokin rayuwa, ya kuma soki gwamnatin PDP da yin balulluba wajen fitar da wasu kiyasi na karya don nuna cewa komai lafiya a kasar nan.