Abin da ya sa nake takarar Shugaban kasa a PDP –Tafawa-Balewa
Dokta Abduljalil Tafawa-Balewa, dan takarar shugabancin kasa ne a karkashin Jam’iyyar PDP. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana dalilan da suka sa yake kalubalantar Shugaba Goodluck Jonathan duk da cewa wasu ’yan jam’iyyarsu sun bayyana shugaban a matsayin dan takara daya tilo da zai yi takara a karkashin jam’iyyar. Me ya sa kake neman takarar […]
Dokta Abduljalil Tafawa-Balewa, dan takarar shugabancin kasa ne a karkashin Jam’iyyar PDP. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana dalilan da suka sa yake kalubalantar Shugaba Goodluck Jonathan duk da cewa wasu ’yan jam’iyyarsu sun bayyana shugaban a matsayin dan takara daya tilo da zai yi takara a karkashin jam’iyyar.
Me ya sa kake neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP?
Ina neman shugabancin kasar nan ne domin a matsayina na dan Najeriya, ina da damar yin hakan. Kuma ina neman kujerar ne saboda zan iya ciyar da kasar nan gaba.
Kana nufin cewa akwai wani abu da gwamnati da ke kan mulki yanzu ba ta yi ba, kuma kana fatan ka yi shi?
Ina ganin ya dace a samu sauyi akan matsalar wutar lantarki. Wannan wani abu ne da ake matukar bukata. Za a iya kallon hakan da wani hakki na dan Adam, wanda kowa yakamata ya amfana da shi. Idan babu wadatacciyyar wutar lantarki ba za a samu kafa masana’antu ba, ba za mu iya kiran kanmu masu tattalin arzikin da ke bunkasa ba.
bangaren ilimi kansa yana cikin wani mawuyacin hali. Kodayake gabanin wannan ya dace mu tattauna kan batun tsaro. Duka suna da alaka, idan babu wutar lantarki, masu zuba jari daga kasashen ketare ba za su zo nan ba domin zuba jarinsu, saboda yadda sai sun saka kudi masu yawa kafin su gudanar da ayyukansu. Zai yi tsada matuka ta yadda ribarsu za ta zama ba ta da yawa.
Yakamata a karfafa wa wasu yankuna na kasar nan gwiwa ta yadda za su kafa wasu masana’antu. Kowace jiha a kasar nan za ta iya tsayuwa da kafarta. Suna da isassun ma’adanai iri daban-daban da kuma dimbin jama’a wadanda suke bukatar horon da yakamata saboda fannin iliminmu ba ya ba su horon da ya dace.
Jam’iyyarku ta PDP ta tsayar da Shugaba Jonathan a matsayin dan takararta. Shin kana kalubalantar hakan ne da kake neman takara a jam’iyyar?
Najeriya kasa ce da take da jama’a fiye da miliyan 180.Saboda haka a ce wasu gungun jama’a sun tsayar da mutum guda a karkashin mulkin dimukradiyya, wannan neman fada ce kawai. Hakan yana zubar da kimar kundin tsarin mulki. Daga sunan jam’iyyarmu, dimukradiyya yakamata ne ya hada kan jama’a domin bayyana abin da suke bukata, amma ba wai wasu tsiraru su tattara jama’a guri guda ba saboda karkata daga tsarin da kuma mayar da kansu marasa amfani ga sauran jama’a da cutar da shugaban kasa.
Shugaban kasa mutumin kirki ne. Bana tunanin cewa yadda jam’iyyata take kallon dimukradiyya haka ne duk wani mutumin kwarai yake kallonta. Yadda sauranmu muka fahimceta da sauran tsiraru abu ne da ba za ka taba samu a ko ina a duniya ba.
Ina ganin ya dace na bai wa jama’ata zabi, kuma ya kamata a ce shugaban kasa ya gwada farin jininsa ta halartacciyyar hanya. Wadannan mutanen suna haka ne domin amfanin kansu da kuma wasu kananan yankunan da suka fito, amma ba suna magana ne da yawun baki dayan kasar nan.
Jam’iyyarku ta ce ta tsayar da shugaban ne saboda ta yi koyi da yadda ake yi a wasu kasashe. Ko ka amince da hakan?
A’a. Wannan abin takaici ne ta fuskoki da dama, saboda mutane da dama a fadin duniya suna sha’awar Najeriya. Watakila wadannan mutanen dai suna karanta tarihi ne a baibai, ko kuma ba sa fahimtar abin da suke karantawa, ko dubawa. Hakan bai taba faruwa ba a kowane lokaci a tarihi, ko da shugaba bai dade da darewa kan mulki ba.
Ya faru da Shugaba Obama da Uwargidan Shugaba Clinton. Akwai lokacin da wani sanatan kasar Amurka, Edward Kennedy ya kalubalanci Shugaba Carter. Kuma Mista Carter ya dora alhakin rashin nasararsa ga sanata. Wannan shi ne dimukradiyya, ba kama karya ba.
A wasu kasashe ana raba coci, ko masallaci, ko addini daga harkokin tafiyar da kasa. Amma mu ’yan siyasarmu sun hade komai, ko dai kabilanci, ko addini, ko sarauta. Sai dai sun samu hanyar hade komai kamar mai da ruwa saboda kawai ’yan kasa ba sa tilasta masu su fadi abubuwan da suke gudanarwa a cikin gwamnati. Fakaicewa da wadannan hujjoji cin fuska ne ga ’yan Najeriya, saboda da wuya ka samu a lokacin kamfe su fada wa jama’a abubuwan da suke su yi.
A wani lokaci a baya, an hana ka fom din takara, amma da aka ba ka, sai aka samu rahoton cewa ka janye wa Jonathan. Me ya faru?
Akwai masu fadanci a kasar nan fiye da kowace kasa a fadin duniyar nan. Na tabbatar cewa akwai masu fadanci a sauran kasashen duniya, amma mu mun dauki hakan a matsayin sana’a. Na tabbata cewa shugabannin jam’iyyarmu a kololuwa, wadanda aka fara da su da farko, sun fahimci dimukradiyya kuma hakan ya sa suka ba ni fom din takara.
Wani abu bako ya faru lokacin wani taron ’yan jarida. Inda na hadu da dattijo Dokta Edwin Clark. Na zauna kusa da shi, ya kasance wani mutum ne na kusa da ni da iyalina lokaci mai tsawo. Ya yi jawabi kan batutuwa da dama da ke faruwa a kasar nan, kuma lokacin da aka tambaye ni ko ina da abin fadi, sai na ce a’a, saboda ba taron ’yan jaridana ba ne; na Dokta E K Clark ne. Suka bukace ni na ce wani abu kan abin da ya ce. Duka abin da ya bayyana lokacin da nake wurin gaskiya ne. Kuma idan ka kalli faifan bidiyon, haka na bayyana, amma daga bisani sai na fara jin akasin abin da na fadi. Wannan ya sa tilas na fito na karyata wancan shashifadin.
Ba ni da wata tsana ga kowa. Shugaba Jonathan shi ne har yanzu shugaban kasar nan. Ina kaunar kasar nan da zuciya daya kuma ina girmama abubuwan da suka hadu suka hadata. Ina takara ne domin na ceto ta da kuma kwato mata kima, amma ba domin wani mutum guda ba.
Ta wace hanya ka samu kudin sayan fom din takara har Naira miliyan 22, kuma ta yaya za ka samu kudin gudanar da kamfe?
Fagen siyasar kasar nan ya dogara ne kacokan kan siyasar kudi.’Yan siyasa suna zuwa ne sau daya a shekara hudu tare da kananan kayayyaki kamar buhun shinkafa, ko kudi. Ba za su kara zuwa ba sai lokacin wani zaben. Saboda haka nake kokarin kwatanta siyasar me ka taba yi wa al’umma.
Abin da ya shafi kowa tilas ne sai ya samu amincewar kowa. Ina takarar neman zama shugaban Najeriya ne baki daya, amma ba shugaban wasu daga cikin gwamnoni ba, ko shugabannin kananan hukumomi, ko kuma kwamitin gudanarwar jam’iyya. Ina kamfe ne ga duka ’yan kasar nan, kuma ina bukatarsu da idan abin da nake roko daga garesu sun gamsu, to su goyi bayan takarata ta kowace hanya.
Yawancin fostocina da tallatani da ake yi, wasu jama’a ne da suka gamsu da ni suke gudanarwa. Ina da kungiyoyi daga sama har zuwa matakin mazabu wadanda suke buga wadannan fostocin. Ina samun goyon baya ne daga kasa kuma ina ci gaba da samun hakan.
Me ye ra’ayinka kan yadda gwamnati take tafiyar da harkokin tsaro?
Har sai a baya-bayan nan, da al’ummar kasar nan tare da maharba suka shiga ciki, ba ma samun sakamako mai ma’ana sosai. Kodayake, sojojin kasar nan suna da martaba a idon duniya, inda suke shiga gaba wajen wanzar da zaman lafiya.
Batun gaskiya Musulmi da Kirista sun kasance suna rayuwa ba kawai a yankin Arewa-maso Gabas ba, amma a baki dayan yankin Arewa. Ina ganin idan muka so abin da aka yi wa tsagerun Nija-Delta, hatta su kansu al’umma za su fatattake su. Saboda haka yakamata a fito da wani gagarumin tsari. kasar nan ba ta da tsari na adana bayanai mai kyau domin yawancin yankunan karkara sun dogara ne kan aikin gona, kuma su ne wadanda wannan aikin ba zai kai garesu ba. Ba tare da samun masaniya kan su waye suke kauracewa muhallansu ba. Kuma ba ma so sauran duniya ta fahimci cewa muna satar kuri’u ta hanyar hana masu zabe kada kuri’a, amma ta yaya za su iya kada kuri’a idan ba su yi rijista da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ba?