Abin da ya sa PDP ta fadi zabe a Jihar Bauchi – Bala Mai’auduga
Alhaji Bala Abdullahi Mai’au-duga shi ne Daraktan Kamfe na dan takarar Sanatan Bauchi ta tsakiya da Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya nema a karkashin Jam’iyyar PDP. A tattaunawarsu da wakilinmu ya yi fashin baki game da dalilin da ya sa PDP ta fadi warwas a zaben gwamnoni da na majalisun tarayya da na […]
Alhaji Bala Abdullahi Mai’au-duga shi ne Daraktan Kamfe na dan takarar Sanatan Bauchi ta tsakiya da Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya nema a karkashin Jam’iyyar PDP. A tattaunawarsu da wakilinmu ya yi fashin baki game da dalilin da ya sa PDP ta fadi warwas a zaben gwamnoni da na majalisun tarayya da na jiha:
Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da yadda aka gudanar da zabe a Jihar Bauchi?
Bala Mai’auduga: Ina daya daga cikin wadanda suka fi kowa farin ciki bisa yadda aka gudanar da zaben lafiya ba tare da hayaniya ba, domin ba mu da wata jiha sai Bauchi idan jiharmu ta zauna lafiya tabbas za a samu ci gaba da bunkasar tattakin arzikin kasa. Mutane da dama sun yi ta addu’o’i na musamman domin ganin an yi zaben lafiya kuma Allah Ya amshi addu’o’inmu, saboda haka muna fatar alheri ga dukkan shugabannin da aka zaba tun daga kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da ’yan majalisar dattawa da na tarayya da na jihohi.
Aminiya: Kwanakin baya ka yi zargin cewa an cinye wasu miliyoyin kudi na PDP ina aka kwana?
Bala Mai’auduga: Hakika akwai wasu makuden kudi da wani mamba a Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi da ake zarginsa da sama da fadi da Naira miliyan 230 na jam’iyya, daga bisani an kafa kwamiti domin gudanar da bincike a kan batan kudin. Har zuwa lokacin da muke wannan tattaunawa muna ci gaba da gudanar da bincike domin gano wanda ya cinye wannan Naira miliyan 230.
Aminiya: Me kake ji ya kawo faduwar PDP a Jihar Bauchi?
Bala Mai’auduga: Abin da ya sa PDP ta fadi zabe a Jihar Bauchi shi ne rashin hadin kai a tsakanin jiga-jigan jam’iyyar da ke rike da manyan mukamai a Abuja. Wasu daga cikinsu suna hassada ga ’yan siyasar Bauchi da suke cikin gwamnatin Malam Isa Yuguda, kuma kowa ya san cewa Gwamna shi ne uban jam’iyya a jiharsa haka yake a dokokin jam’iyya. Shi ma Shugaban kasa yana sama da kowa a tsarin gudanarwa na PDP. Da ’yan siyasar Abuja sun hada kansu waje daya babu inda za a rasa Naira miliyan 230 na jam’iyya balle ta fadi a zabe a jihar nan. Abin da muka so a yi shi ne tunda tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya fito ne daga Bauchi ta Kudu inda ya yi mulki na tsawon shekara takwas Malam Isa Yuguda shi ma ya fito daga Bauchi ta Kudu ya yi shekara takwas, saboda haka muka tsaida Alhaji Muhammed Awwal Jatau daga Katagum a yankin Bauchi ta Arewa domin su ma su taba amma sai Allah Ya yi hukuncinsa. dan takararmu ya cancanta kamar kowa, amma Allah ne ya kawo guguwa a dandalin siyasar Najeriya kuma mu muka ce Allah Ya kawo mana sauyi na alheri a kasar nan. Idan Allah Ya kai mu a zaben shekara ta 2019 za mu sake fitar da dan takarar Gwamna daga yankin Katagum ko Misau. Wato Bauchi ta Arewa ko Bauchi ta Tsakiya.
Aminiya: Me za ka ce game da masu cewa ya kamata a tsige shugaban jam’iyyarku ta PDP Adamu Mu’azu?
Bala Mai’auduga: Zargi shi ne babban sunnar siyasa a Najeriya, dama idan guguwar sauyi ta kada kowa za ka ji yana zargin dan uwansa amma duk abubuwan da ake fada a kansa ba za mu ce babu gaskiya a ciki ba. Idan ya san cewa abubuwan da ake zarginsa gaskiya ne to ya kamata ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar. Kuma idan ya sauka jam’iyyar za ta ci gaba, za ta kuma zauna lafiya ina tabbatar maka da cewa babu wanda yake shirya masa makarkashiya daga Arewacin Najeriya.
Aminiya: Wasu manyan ayyuka gwamnatin PDP ta yi ga talakawan Jihar Bauchi zamanin Isa Yuguda?
Bala Mai’auduga: Kadan daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin PDP ta yi ga talakawan jihar a zamanin Malam Isa Yuguda, akwai filin jirgin sama na kasa-da kasa akwai jami’a mallakar jiha, an gina asibitin kwararru a cikin makarantar BACAS, ga hanyar Ningi zuwa Burra tare da tura dalibai zuwa kasashen waje domin karo ilimi, an kuma gyara kananun asibitoci sama da guda 120 a sassa daban-daban. Dukkan kananan hukumomin jihar guda 20 babu inda ba su amfana da gwamnatin PDP ba. Duk bayan wata uku gwamnatin jiha tana ba da tallafin kayayyakin abinci ga marayu da marasa galihu, malaman Tsangaya suna karbar Naira dubu biyar-biyar a duk karshen wata.’Yan kasuwa a lokacin da Malam Isa Yuguda ya kama aiki a shekara ta 2007 ya ba su bashin Naira miliyan 500 daga bisani ya yafe musu sauran kudaden. kungiyoyin addini suna samun tallafi duk karshen wata, Malam Isa Yuguda ya yi alheri ga al’ummar Jihar Bauchi, sun gagara saka masa alherin da ya yi musu a lokacin zabe, saboda haka za mu yi adawa sosai ga gwamnatin APC amma adawa mai amfani. Kuma za a jima ana tunawa da ayyukan Malam Isa Yuguda a Bauchi.
Aminiya: Bashin nawa ake bin gwamnatinku?
Bala Mai’auduga: Kai dan jarida bari na fada maka gaskiya babu gwamnatin da ba a bin ta bashi, sai dai na wata ya fi na wata saboda haka bashi hanji ne yana cikin kowa a Najeriya.
Aminiya: Da gaske ne ka yi kusan sauya sheka zuwa APC?
Bala Mai’auduga: A matsayina na jigo a PDP ina nan daram babu inda zan je domin ni ba dan jagaliyar siyasa ba ne, an jima ana fafatawa da ni a dandalin siyasar Jihar Bauchi kuma ba zan sauya sheka ba za mu ci gaba da yin adawa.
Aminiya: Mene ne sakonka ga ’yan jam’iyya da shugabannin PDP na Jihar Bauchi?
Bala Mai’auduga: Babban sakona ga ’yan jam’iyyarmu shi ne a ci gaba da yin hakuri, shekara hudu kamar kwana hudu ne kada mutum saboda talauci ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya. PDP za ta sake farfadowa nan da shekaru kadan masu zuwa. Sakona ga shugabannin PDP na wannan jiha shi ne mu yi hakuri mu hada kanmu waje daya kura-kuran da muka aikata a shekarun baya mu zo mu gyara domin PDP har gobe tana da tasiri.