Abin da ya sa shari”ar Shema ta tsaya

Kasawar da mai bayar da shaida na farko ya yi mai suna Ibrahim Dabo na gabatar da muhimman rahoton kwamitin da ya binciki al’amuran kananan hukumomin jihar Katsina a shekarar 2015 ya janyo kotun da dage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shema.   Dabo ya kasa gabatar da gamsashshiyar amsa inda […]

Abin da ya sa shari”ar Shema ta tsaya

Kasawar da mai bayar da shaida na farko ya yi mai suna Ibrahim Dabo na gabatar da muhimman rahoton kwamitin da ya binciki al’amuran kananan hukumomin jihar Katsina a shekarar 2015 ya janyo kotun da dage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shema.
 
Dabo ya kasa gabatar da gamsashshiyar amsa inda hakan ya janyo lauyansa ya nemi sake sanya wata rana don gabatar da cikakken rahoto ga kotun.
 
Sai dai lauyan Shema, Joseph Daudu bai yi watsi da bukatarsa ba inda hakan ya sanya alkalin kotun, Mai Shari’a Maikaita Bako ya dage shari’ar zuwa ranar 30 da 31 ga watan Mayun shekarar 2018.