Abin da ya sa Shata ba ya cin kasuwa – Yalwan Shata
Hajiya Fatima Mamman Shata wadda aka fi sani da Yalwan Shata, ita ce matar marigayi Dokta Mamman Shata Katsina ta hudu. Ta tattauna da Aminiya a gidanta da ke Kaduna, kwanakin baya, inda ta yi bayanin rayuwar marigayin da sauran batutuwa. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ko za ki ba mu takaitaccen tarihinki? Yalwan […]
Hajiya Fatima Mamman Shata wadda aka fi sani da Yalwan Shata, ita ce matar marigayi Dokta Mamman Shata Katsina ta hudu. Ta tattauna da Aminiya a gidanta da ke Kaduna, kwanakin baya, inda ta yi bayanin rayuwar marigayin da sauran batutuwa. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ko za ki ba mu takaitaccen tarihinki?
Yalwan Shata: Sunana Hajiya Fatima Mamman Shata, amma an fi sanina da Yalwan Shata. Wannan sunan ya samuo asali ne saboda dimbin alherin da aka samu lokacin haihuwa ta. Dalilin da ya sa ke nan mahaifiyata ta sanya mini sunan Yalwa. Mu uku aka haifa, maza biyu, ni ce cikon ta ukun. An haife ni ne a garin Funtuwa na Jihar Katsina. Sunan mahaifina Alhaji Ibrahim Mai-Tawakkali.
Aminiya: Yaya haduwarku da Shata ta kasance?
Yalwan Shata: Ba hada mu aka yi da Shata ba. Lokacin da Iyayena suke safara, Shata na hawa doki ya je gidan attajirai domin ya yi masu waka. Lokacin masu hali na da jakan sulallan kudi, wato jaka ta attajirai da ake sa tsabar kudi.
Wata rana ina gida an dawo Sallar Idi, sai Shata ya zo gidanmu yana yi wa babana waka, sai aka ban kudi na kai masa. Shata ya san gidanmu saboda mahaifinsa mutumin mahaifina ne domin sun zauna guri guda a garin Musawa.
Bayan na fara girma ne, wata rana mun fita wasa da kwawayena sai ya ganni, ya kira ni, sai na ruga gida. Sai ya zo ya samu mahaifina ya bayyana masa cewa ya ganni, kuma yana so na. Ta haka aka fara a yi, ba a yi ba, har muka yi aure.
Aminiya: Ke ce matar Shata ta nawa?
Yalwan Shata: Ni ce matarsa ta hudu.
Aminiya: Wace irin waka yake yi wa mahaifinki a wancan lokacin?
Yalwan Shata: Yana cewa ne: “…Mai Tawakkali, Baban Sada… A dauki kanwan baki, a ba dabbobin baki.”
Aminiya: Ya zamanki da kishiyoyi ya kasance?
Yalwan Shata: Akwai kuruciya lokacin nan. Yadda ake yi shi ne idan aka kawo amarya, ana kai ta wajen uwargida ne domin a mika mata ita a hannunta. Daga nan sai a kewaya da ita sauran dakuna a ce ga amana nan. Kai kuma sai a ce maka ka yi biyayya ga na gaba da kai.
Aminiya: Shata na cewa “…Dadi muka ji muka zauna gari…” ko ya taba gaya miki dalilin wannan wakar?
Yalwan Shata: Eh. A lokacin da yake Kano, rayuwa ta ci karo da hassada domin yana bako, bai yi gado ba, amma ya gagara, saboda ya danne ‘yan gado. A yanzu an yi imani da addini, amma a da abin babu kyau. Ana so a dauki ransa, sai ya bar Kano, ya dawo Funtuwa. Ya zauna kamar nan aka haife shi.
Aminiya: Akwai wani abin mamaki da ya taba gaya miki?
Yalwan Shata: Tun da nake da Shata, ban taba ganin ranar da ya sha wani rubutu. Ko sanya wata laya, ko guru ba. Idan almajirai suka zo sai ya kira mu ya ce ga rubutu an yi, amma ga shi, ku sha. Ba ya koransu, ba ya wulakanta su, amma shi dai ba zai sha ba. Kuma komai dare kamar karfe 2:00 sai ya aiko dan Maraya Jos, ya ce je ka dauko mini Yalwa.
Aminiya: Meye dalilin da ya sa Shata ya dauki Sarkin Daura a matsayin Ubangida?
Yalwan Shata: A gaskiya tsakanin Sarkin Daura Muhammadu Bashar da Shata sai Allah. Shata ya maida shi Uba. Yana cewa. Dukiyarsa kamar tasa ce.
Aminiya: ’Ya’yanku nawa da shi?
Yalwan Shata: ’Ya’yanmu uku. Akwai Bilkisu wadda take aiki a Bankin ba da Rancen Gina Gidaje na kasa (FMB), sai Nura da kuma Umma (matar Kanar Bala Mande).
Aminiya: Yaya dangantakar Shata da sauran makada take?
Yalwan Shata: dan Kwairo Maradun na zuwa gidan Shata ya yi waka idan ana biki, Shata ya dauko kyauta ya ba shi da sauran makada.
Aminiya: Kwana nawa yake idan ya je farauta?
Yalwan Shata: Kwana biyu ko uku. Ko ya je da yara masu taimaka masa, ko shi kadai. Ya taba zuwa dajin Ruggu inda har ya harbo gwanki. Shata mutum ne mara tsoro.
Aminiya: Ko kin san yawan ’ya’yan Shata?
Yalwan Shata: A gaskiya suna da yawa.
Aminiya: Me ye ya sa Shata bai taba yi wa iyalansa waka ba?
Yalwan Shata: A’a . Ya taba ambatar daya. Wato a wakar ’Yar Auta inda yake cewa. “…Kana da Binta a dakinka, ina da Binta a dakina, a inda Bawa ya tsere mini, da Shata bashi da ‘yar auta….’ Bintar da ya ambata a wannan wakar tana daya daga cikin matansa. Amma ba ya sa ’ya’ya ko mata a wakarsa.
Aminiya: Meye alakar Shata da dan Maraya Jos?
Yalwan Shata: dan Maraya Jos ya dauki Shata a matsayin uba ne. Idan suka hadu a wani gari wurin wasa na Talabijin ko na Rediyo da sauransu, sai mawaka su rika kawo gaisuwa. dan maraya ya taba zuwa ya buga gida da karfe biyun dare ya ce “Baba ne ya ce in zo in dauke ki, in kai ki wurinsa”. Lokacin duniya na kwance. Wanda in yanzu ne wa zai bude gida?
Aminiya: Shin gayyato Barmani Coge kuke yi domin ta zo ta yi waka idan ana biki a gidan Shata?
Yalwan Shata: Gaya masa muke za a yi gayyata na bikin mata a cikin gida. Kuma tana zuwa gidan kodayaushe, saboda ita mutum ce mai ban dariya. Kuma ta sha samunsa, su yi ta hira ta ba shi dariya.
Aminiya: Shin Shata yana zuwa Musawa kuwa?
Yalwan Shata: Yana da gida da gona da lambu wanda ya sa kadoji duka a Musawa, muna zuwa hutu can. Ba a yin wata uku ba mu je ba. Inda yake cewa “mun yi murnar zuwa Shata bana ya mayar da kada Musawa.” Kadojin suna da yawa. Amma babba ya dauko sannan ya mayar. Abin mamaki, da sun ji muryarsa sai su fito. Babban kuma sai ya fito ya zo ya zauna kusa da Shata.
Aminiya: Shin Shata na da yayye da kanne kuwa?
Yalwan Shata: Yana da yayye kodayake sun mutu, amma kanne na nan, sai dai ba ciki daya suke ba.
Aminiya: Ina kunkurun Shata yake yanzu?
Yalwan Shata: Na san yana da katon kunkuru, amma yanzu ban san ko yana nan ba. Ka san tarbiyya irin ta da ba ka tambeye-tambaye.
Aminiya: Wace wakarsa kika fi so?
Yalwan Shata: Bakandamiya da ta wakar Sarkin Daura. Inda yake cewa “…Bashar bari duba girmansu, …bari duba kankantarsu, binciki littafi, ka shiga cikin ofis, ka shiga shirin mulkin Daurawa, ka shiga shirin mulki ka yi gyara.”
Na taba tambayarsa, sai ya ce ai lokacin da aka ba Bashar Sarkin Daura, yana karami ne. Akwai kawunne da yayyi da kuma kanne. Sai ya ce idan ya dubi girmansu ko kankantarsu ba zai yi komai ba.
Aminiya: Me ye dalilin da ya sa ke da wani shahararren mutum kuka raka shi garin Ikko?
Yalwan Shata: Ni da Shago dan Dambe ne. Domin an je ne karbar lambar girmamawa ta kasa domin wakokin gina kasa da sauransu. Bikin ya gudana ne lokacin mulkin Shugaba Obasanjo na farko. Kuma mun sauka ne a otel din Federal Palace.
Aminiya: Me ye sirrin da ya sa Shata yake zuwa taro a makare?
Yalwan Shata: Ka san haka yake idan aka gayyece shi biki sai ya je a makare, ya kuma ce a fara ba sauran mawaka fage su yi wasa, su yi waka, sannan shi ya yi. Yana da kwarjini domin idan shi ya fara zai handame komai.
Aminiya: Me ya sa Shata ba ya cin kasuwa?
Yalwan Shata: Ina jin Shata yana daya daga cikin mutane da basa cin kasuwa a Arewa. Saboda idan wani ya ce ga Shata, sai mutane su taru, wato sai kasuwar ta fashe, a tattake kayan wasu. Dalilin da ya sa ba ya cin kasuwa ke nan.
Aminiya: Me ya kawo rabuwarku?
Yalwan Shata: Allah ne ya kawo. Ya yi ya yi kar mu rabu, amma muka rabu.
Aminiya: An shiga tsakaninku ne?
Yalwan Shata: kaddara ce da kuma lokacin rabuwar da ya yi.
Aminiya: Wane shawara za ki ba mawakan yanzu?
Yalwan Shata: Yanzu ba a ba mawaka dama a filin talabijin ko rediyo mai hoto su yi waka, domin yana kara wa mutun karsashi ko ba kai ake yi wa waka ba. Su kuma mawaka ba su da kima kamar su Shata, domin sun aro al’adu da ba namu ba.
Aminiya: A matsayinki na jagorar mata, mene ra’ayin ki game da zaben 2015?
Yalwan Shata: ’Yan siyasa su san cewa Allah ke ba da mulki. Kada su ba yara kayan maye, domin su yi banga, a yi lafiya, a gama lafiya.