Abin da ya sa shugaban APC murabus
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga muƙaminsa saboda shirin tsige shi da wasu makusantan shugaban ƙasa ke yi. A yammacin Lahadi ne tsohon gwamnan na jihar Nassarawa ya aike da takardar ajiye muƙaminsa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila. Sanata Abdullahi Adamu wanda ya zama shugaban APC […]
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga muƙaminsa saboda shirin tsige shi da wasu makusantan shugaban ƙasa ke yi.
A yammacin Lahadi ne tsohon gwamnan na jihar Nassarawa ya aike da takardar ajiye muƙaminsa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.
Sanata Abdullahi Adamu wanda ya zama shugaban APC a watan Maris 2022 ya yi murabus ɗin ne lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke halartar taron AU a Kenya.
Majalisar Wakilai: Gwamnonin APC sun goyi bayan takarar Abbas
An ceto Shugaban APC da aka sace a Ekiti
Wani makusancin tsohon shugaban APC ya shaidawa Aminiya cewa ya sauka daga kujerarsa ne saboda an shirye tsige shi a taron ƙolin jam’iyyar da za a gudanar ranar Talata da Laraba.
Ya ce “wasu makusantan shugaban ƙasa guda biyu ne suka fara tattara sa hannun mahalarta taron domin amincewa a tsige shi.
“Ko da ya samu labari sai ya yi murabus domin kaucewa wulaƙanci.”
Sanata Abdullahi Adamu dai ya goyi bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawal lokacin zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar APC.
Bayan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara kuma sun ci gaba da samun takun saƙa tsakaninsu.
A baya bayan nan ma sun samu jayaya game da shugabancin wakilan jam’iyyar a Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.