Abin da ya sa Shugaban Gabon raba wa matasa gadonsa
A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba, ya ce zai raba wa matasan kasar gadon da ya gada daga mahaifinsa – wanda ya jagoranci kasar fiye da tsawon shekara 40, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.Ya kuma ce za a bai wa gwamnatin kasar kadarorin da […]
A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba, ya ce zai raba wa matasan kasar gadon da ya gada daga mahaifinsa – wanda ya jagoranci kasar fiye da tsawon shekara 40, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Ya kuma ce za a bai wa gwamnatin kasar kadarorin da suka zama mallakin mahaifinsa Umar Bongo, wadanda biyu suke a birnin Paris, daya a Gabon. Har ila yau, ya ce zai yi hakan ne saboda martaba mahaifin wanda ya rasu a shekarar 2009.
Shugaban ya yi sanarwa ne lokacin bikin cika shekara 55 da samun ’yancin kasar daga hannun Turawan kasar Faransa.
Dukiyar da Mista Bongo ya bari dai ta kai miliyoyin daloli.
Masu shari’a dai a kasar Faransa suna bincike kan kadarorin da shugabannin Afirka suke saya a kasar, wanda ya hada da na Mista Bongo.
Wata kungiyar yaki da karbar hanci da rashawa ta ce da dukiyoyin gwamnati aka sayi irin wadannan manyan kadarorin.