Abin da ya sa ’yan gudun hijira suka nace zama a sansanonin Maiduguri

Sama da mutum dubu 500 da rikicin Boko Haram ya raba su da gidajensu ne suke gudun hijira a sansanoni daban-daban a birnin Maiduguri duk da cewa sojojin kasar nan sun kwato wasu garuruwa da ’yan Boko Haram suka kwace inda suka kori al’ummar garuruwan daga muhallansu. Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno sun yi […]

Abin da ya sa ’yan gudun hijira suka nace zama a sansanonin Maiduguri

Sama da mutum dubu 500 da rikicin Boko Haram ya raba su da gidajensu ne suke gudun hijira a sansanoni daban-daban a birnin Maiduguri duk da cewa sojojin kasar nan sun kwato wasu garuruwa da ’yan Boko Haram suka kwace inda suka kori al’ummar garuruwan daga muhallansu.

Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno sun yi ta kokarin samar wa irin wadannan mutane wurin zama, sannan duk da wannan kokari na gwamnati, wadansu da dama daga cikin ’yan gudun hijirar ba su samu matsuguni ba, inda suka tare a wurin ’yan uwa a cikin unguwanni.

Zuwan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta kuduri aniyar  kawo karshen ta’addancin ’yan Boko Haram, kuma duk da kalubalen da yakin ya rika cin karo da shi, za a iya cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.

A Jihar Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum ya sha alkawarin tabbatar da dukkan ’yan gudun hijira sun koma garuruwansu, sai dai duk da haka har zuwa yanzu mutane da dama suna zaune a sansanonin gudun hijirar.

Wani bincike da Aminiya ta gudanar, ta gano kusan kashi 40 ne kawai na ’yan gudun hijirar suka koma garuruwansu.

A ziyara da wakilinmu ya kai a wasu sansanonin ’yan gudun hijirar a birnin Maiduguri, ya gano cewa al’umomin kananan hukumomin Bama da Konduga da Gwoza da na garin Banki, sun kasa komawa garuruwansu bisa wasu dalilai da suka bayyana.

Malama Kyallu Shata daga garin Ashigashiya da ke iyaka da kasar Kamaru a Karamar Hukumar Gwoza ta ce ba za ta iya komawa gida ba saboda har yanzu babu tsaro a garinsu kuma ba a gina musu gidajensu ba. Ta ce ’yan Boko Haram sun fatattake su, inda ta rasa mijinta, wanda har zuwa yanzu kusan shekara shida babu labarinsa. Ta ce tana da ’ya’ya biyar kuma sana’ar girka abinci take yi a sansanin ’yan gudun hijirar, don ta samu abin da za ta rufa wa kanta da ’ya’yanta asiri.

Ta ce suna samun tallafi daga Kungiyar WFP, wacce take ba su abinci sau daya a wata, wanda ba ya isarsu, hakan ya sa take yin sana’a kuma take zama a sansanin Dalori, duk da cewa akasarin mutanen sansanin sun fito ne daga Karamar Hukumar Bama. Don haka ne ma gwamnati ba ta san da zamansu ba. Ta ce su ’yan Gwoza ba su fi mutum 10 ba kuma ta ce duk da garin Gwoza akwai sansanin ’yan gudun hijira amma ba za su koma ba sai an sake gina musu gidajensu kuma an samar da ingantatcen tsaro.

Shi kuwa Kaigama Adam da ke sansanin ’yan gudun hijira na Madinatu, wanda ya fito daga garin Banki da ke iyaka da Jamhuriyar Kamaru, a Karamar Hukumar Bama, ya ce sai da gudun hijira ya kai shi cikin Kamaru, ya bullo ta Mubi zuwa Yola a Jihar Adamawa, kafin Allah Ya kawo shi sansanin yau kusan shekara shida. Ya ce su babbar matsalar da ta hana su komawa garinsu Banki, ba rashin tsaro ba ne, illa gidajensu sun zama matsugunin ’yan gudun hijirar daruruwan mutanen da Boko Haram suka koro daga kauyukan da ke kewaye da garin Banki. Don haka shi kansa garin Banki ya zama sansanin ’yan gudun hijira.

Ya ce ko a yanzu gwamnati ta samar wa wadancan mutane wurin zama a shirye suke su koma gidajensu. Ya ce “Ba mu da wata matsala ta rashin tsaro, domin mu ba mu dauki gora ba don yaki da ’yan Boko Haram a 2014, don haka ba su da wata matsala da mu, ko sun zo, ba su taba kowa ko kashe wani, sai dai su debi kayan abinci da kayan bukatun yau da kullum su tafi. ’Yan gudun hijira daga kauyukan Darajamal da Kumshe da Gulumba da Kote da Bormoni, daga garuruwan kan iyaka ne yanzu haka suke zaune a gidajenmu.”

Kaigama Adam, wanda ya ce shi kafinta ne da ke ’yan gyare-gyaren kofofi da tebura da sauran aikin kafinta a sansan Dalori 1 da ke wajen birnin Maiduguri, domin ciyar da iyalansa da suka kunshi mata 2 da ’ya’ya 8, a sansanin ya ce aikin sake gina garin Banki da gwamnati ke yi, yana tafiyar hawainiya, domin yanzu haka aikin ya tsaya cik.

Ya ce yana daya daga cikin kafintocin da suka je aikin gina gidaje amma zuwa yanzu kusan wata shida ke nan aikin ya tsaya babu wani dalili. “Da har muna murna za mu koma gidajenmu amma yanzu murnarmu ta koma ciki. Don haka wannan matsuguni da muke zaune a nan Maiduguri ya zama dole ya kasance gida gare mu,” inji shi.

Aminiya ta gano cewa, duk da akwai sansanonin ’yan gudun hijira a kananan hukumomin da Boko Haram suka kwace a baya da sojoji suka sake kwatowa amma suna cike da mutane daga kauyukan da ke wadannan kananan hukumomi, wanda har yanzu ba gina irinsu a kauyuka ba. Hakan ya sa jama’ar da ke manyan garuruwan suka rasa inda za su koma, baya ga rukunin gidajen da gwamnati ta gina a wasu hedikwatocin kananan hukumomi.

“Akalla gidaje sama da dubu 20 aka gina a garin Bama amma akasarinsu ba su dace da tsarin zamanmu da rayuwarmu ba,” inji Abbagana Ibrahim, wani Dattijo a sansanin gudun hijira na Dalori 1; wanda ya fito daga Bama.

Ya ce akasarin ’yan gudun hijira sun zabi su ci gaba da zama a sansanonin da ke Maiduguri ne, domin babu ingantattun gidaje da za su koma a Bama, saboda ba za su koma su sake kasancewa a sansanin  gudun hijira ba. Ba su da abin yi, alhali a nan Maiduguri suna samun dan abin yi da suke kula da iyalansu ta hanyar kananan sana’oi.

Dattijo Abbagana Ibrahim, wanda yake da mata uku da ’ya’ya 10, ya koka cewa ba ya da wani abu da zai yi don taimakon kansa da ciyar da iyalansa da suke zaune a tsakanin ’yan uwansa ’yan gudun hijira. Ya ce a matsayinsa na manomi ba zai iya komawa Bama ba, domin babu yadda za a yi mutum ya yi tafiyar kilomita daya don zuwa gona saboda tsoron ’yan Boko Haram.

Mustapha Abubakar, shi ne Limamin Masallacin Sansanin ’Yan Gudun Hijira na Bakassi, wanda yake da mata biyu da ’ya’ya biyar, ya  ce ya fito ne daga kauyen Mairamri, a Karamar Hukumar Konduga, kuma ya shaida wa wakilinmu cewa kauyensu har yanzu babu tsaro, domin har yanzu ’yan Boko Haram suna ratsawa ta garin. Ya ce baya ga garin Konduga, babu wani yanki da za a iya cewa an samu tsaro a cikinsa, ballantana jama’a su koma su ci gaba da rayuwa kamar da a yankin..

“Koda an ce mu koma mu gina gidajenmu, ba za mu koma ba, domin babu tsaro kwata-kwata. Zamanmu a nan ya fi mana, duk da ba a gidajenmu muke ba, nan ya fi tsaro.Amma da zarar gwamnati da hukumomin tsaro sun ba mu tabbacin akwai isasshen tsaro a kauyukanmu, ba hadkwatar karamar hukuma ba, za mu yi ban-kwana da sansanin ’yan gudun hijira na Maiduguri, don komawa kauyukanmu. Amma zuwa yanzu dai nan shi ne gidanmu,” inji shi.

Sai dai akasarin sansanonin ’yan gudun hijirar da Aminiya ta ziyarta daga na Dalori 1 da 2 da na Bakassi da na Madinatu da Tatar, mafi yawan matasan da suke sansanonin suna yin sana’ar dinkin hula ce, mazansu da matansu.

Da Aminiya ta tuntubi Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Sake Ginawa da Tsugunar da Jama’a na Jihar Borno, Injiniya Mustapha Gubio, ya ce kada a dora wa Gwamnatin Jihar Borno laifi kan rashin samar da wadatattun gidaje ga ’yan gudun hijirar a kauyukansu ko kuma kusa da kauyukansu.

Ya ba da misali cewa sama da gidaje dubu 20 aka gina tun daga shekara 2017 ga ’yan gudun hijirar, inda tun daga wancan lokaci aka umarci ’yan gudun hijirar su koma garuruwansu, su shiga gidajen. “Amma abin takaici ko a makon jiya mun ziyarci wadancan gidaje, amma babu kowa a ciki. Haka lamarin yake a garin Gajiram, hedkwatar Karamar Hukumar Nganzai, inda aka gina sama da gidaje 1000, sai dai wadansu mutane daban ne suka shiga cikinsu.

Haka kawai suka ki komawa gidajensu, sun gwammace su ci gaba da zama a sansanonin ’yan gudun hijira na Maiduguri, don wani dalili da su suka sani,” inji Injiniya Gubio.

Ya ce idan suna maganar rashin tsaro ne, me za su ce ga wadanda suka koma garuruwansu tunda dadewa?

A jawabinsa a yayin gabatar da kasafin kudin badi, Gwamna Babagana Zulum ya sake nanata aniyarsa ta tabbatar da dukkan ’yan gudun hijira sun koma garuruwansu, ta hanyar sake gina musu gidaje na zamani da karin gina wasu dubban rukunan gidaje, a dukkan gundumomin sanatoci uku da ke Jihar Borno.