Ana Laluben Hanyar Sa Yara Miliyan 10 A Makaranta A Najeriya

Wata gidauniyar kasa-da-kasa mai cibiya a kasar Birtaniya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin Najeriya don shawo kan manyan matsalolin da ke hana yara miliyan 10.19 zuwa makaranta a kasar. Bayanai sun tabbatar da cewa  a kasashen nahiyar Afirka Kudu da Sahara, Najeriya  ta fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. A […]

Ana Laluben Hanyar Sa Yara Miliyan 10 A Makaranta A Najeriya

Kujeru a cikin aji a makarantar Bethel Baptist a Damishi, Jihar Kaduna inda ’yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai fiye da 100. (Hoto: Reuters). 

Wata gidauniyar kasa-da-kasa mai cibiya a kasar Birtaniya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin Najeriya don shawo kan manyan matsalolin da ke hana yara miliyan 10.19 zuwa makaranta a kasar.

Bayanai sun tabbatar da cewa  a kasashen nahiyar Afirka Kudu da Sahara, Najeriya  ta fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

A shirin Najeriya a Yau mun yi nazari a kan wannan matsala da yadda za a magance ta.