Abin da ya sa zamu sama wa Atiku kuri’a miliyan 10 – Isah Mohammed

Shugaban Kungiyar Magoya bayan dan Takarar Shugaban Kasa na Jamiyyar PDP, Atiku Abubakar  na kasa mai suna ‘Grassroots Network 4 Atiku (GN4A) 2019’, Barrista Isah Mohammed ya ce sun kudiri aniyar samar wa Atiku kuri’a miliyan 10 ne domin ganin ya samu nasarar cinye zaben 2019. Barista Isa ya bayyana haka ne lokacin da yake […]

Abin da ya sa zamu sama wa Atiku kuri’a miliyan 10 – Isah Mohammed

Shugaban Kungiyar Magoya bayan dan Takarar Shugaban Kasa na Jamiyyar PDP, Atiku Abubakar  na kasa mai suna ‘Grassroots Network 4 Atiku (GN4A) 2019’, Barrista Isah Mohammed ya ce sun kudiri aniyar samar wa Atiku kuri’a miliyan 10 ne domin ganin ya samu nasarar cinye zaben 2019.

Barista Isa ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai da suka kira a Bauchi, ya ce da ikon Allah za su samar wa Atiku Abubakar  kuri’a har miliyan 10 wanda  yin haka na daga cikin matakan da za su ba shi nasarar lashe zaben Shugaban Kasa a 2019.

Shugaban ya ce kungiyar tana kan tuntubar miliyoyin jama’a da ke da katin jefa kuri’a domin jawo hankalinsu don su zabi Atiku kuma ta wannan fuska sun samu tuntubar mutane fiye da miliyan uku a sassa daban-daban da ke fadin kasar nan kuma sun amince za su zabi Atiku a 2019, “Muna kuma kan tattaunawa da sauran har sai mun samu adadin da muke so na miliyan 10,” inji shi.

Ya ce “Muna kan shiga dukan lunguna da sakon Najeriya da nufin samar wa Atiku da mutum miliyan 10 da za su zabe shi, domin kawar da matsalar da gwamnatin Buhari ke haifarwa na kunci da talauci da tsadar rayuwa da suke addabar al’ummar kasar nan.”

Da yake tsokaci kan hana wa wadansu ’yan Najeriya fita kasar waje su 50 da gwamnatin Buhari ta yi, Barista Isa wanda tsohon alkali ne ya ce wannan doka ta saba wa shari’a da dokokin Najeriya domin lamari ne da zai tauye wa ’yancin tafiye-tafiye da tsarin mulkin 1999 ya tanadar musu.

Ya ce, “Abin takaici a cikin jerin wadanda Gwamnatin Tarayya ta sake sunayensu har da matattu, wannan mataki na hana tafiye-tafiye da gwamnati ta dauko ya fito da manufarta fili cewa ba ta mutunta doka, domin tana daukar matakan da suka saba wa doka kan abokan hamayyarta a siyasa wanda wannan karan-tsaye ne ga dokokin kasa.”

Barista Isa ya ce a sama da shekara uku Gwamnatin Tarayya ta ki mutunta umarnin kotuna kan sakin Kanar Sambo Dasuki da Sheikh Ibrahim Zakzaky wadanda kotun ta bayar da umarnin a sake su tun da jimawa amma gwamnatin Buhari ta ki, yana mai cewa babu abin da hakan ke janyo wa kasar illa koma-baya.

Ya ce “Muna mulki ne na dimokuradiyya, don haka ’yan Najeriya suna da cikakken ikon zabin shugabannin da suke so suka kuma amince da su, ba wai a tilasta su sai su zabi wanda ba su suke muradi ba.”

Shugaban ya yi zargin cewa akwai tabarbarewar al’amura a Najeriya , “Sashin ilimi ya tabarbare, lafiya ma haka, ga kuma matsananciyar yunwa da fatara da gwamnatin Buhari ta jefa ’yan Nijeriya a ciki don haka jama’a suna neman mafaka, ga ta kuma sun samu a wajen Atiku don haka 2019 Atiku ne za a yi,” inji shi.

Barista Isa ya zargi Gwamnatin Tarayya da rashin adalci wajen fakewa da yaki da cin hanci da rashawa domin hukunta ’yan adawarta na siyasa wanda yin haka ya saba wa dimokuradiyya.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa