Abin da ya sa zan sake tsayawa takarar Shugaban kasa – Buhari

Tsohon Shugaban mulkin soja, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya ce shekara 15 da Jam’iyyar PDP ta shafe tana mulkin kasar nan ba tare da wata alkibla ba ce ya sa zai sake tsaywa takarar Shugaban kasa a wannan karo, inda ya ce nan da mako guda zai bayyana niyyarsa ga jama’ar kasar nan. Janar […]

Abin da ya sa zan sake tsayawa takarar Shugaban kasa – Buhari
Abin da ya sa zan sake tsayawa takarar Shugaban kasa – Buhari

Tsohon Shugaban mulkin soja, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya ce shekara 15 da Jam’iyyar PDP ta shafe tana mulkin kasar nan ba tare da wata alkibla ba ce ya sa zai sake tsaywa takarar Shugaban kasa a wannan karo, inda ya ce nan da mako guda zai bayyana niyyarsa ga jama’ar kasar nan.
Janar Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga kungiyoyin magoya bayansa a Abuja.
Janar Buhari ya bayyana mulkin Jam’iyyar PDP na shekara 15 a matsayin marar alkibla, kuma ya bukaci magoya bayansa su kauce wa batanci da bakaken maganganu a kan abokan takararsa na Jam’iyyar APC.
Janar Buhari ya ce, “Na kudiri zan bayyana aniyata a ranar 8 ga Oktoba, kuma ina fatan samun ci gaban goyon baya da sadaukarwa daga gare ku. Sai dai zan so na yi muku nuni cewa in har kuna son goyon bayan ya yi ma’ana, sai kun isar da shi ga jam’iyya da dukkan wadanda jam’iyyar ta tsayar.”
Ya ce Jam’iyyar APC ce zabin da Najeriya ta dade tana jira, kuma ya ce sun kuduri aniyar kawo sauyi kan yadda abubuwa ke gudana a kasar nan.
Ya soki mulki PDP, inda ya ce a shekara 15 da ta yi a gadon mulki “al’amuran tsaro sun yi mugun tabarbarewa, rashin bin doka da oda sun yi tashin gwauron zabo ga tsabagen cin hanci da rashawa da kuma gaza gudanar da mulki yadda ya kamata,” inji shi.
Janar Buhari ya bukaci magoya bayansa su mayar da hankali wajen kawo sauyi kan yadda ake gudanar da kasar nan, “Aikin da ke gabanmu a yau babba ne, kuma mafi muhimanci mu karbe mulki daga wadanda suke wasa da shi,” inji shi.
Tun farkon a jawabin Babban Sakataren kungiyar Buhari 2015 Support Group Center Ibrahim Bello Dauda ya bukaci Janar din ya fito takara a zaben badi, inda ya ce ’yan Najeriya suna da yakini a kansa.
Cikin wadanda suka halarci zdaman akwai jiga-jigan APC da suka hada da Kanar Hameed Ali da Janar John Shagaya da tsohon Gwamnan Bayelsa Timipre Silba.
Ana sa ran Janar Buhari wanda Jam’iyyar PDP ta fi gani a matsayin barazana ya fatata a zaben fidda gwani da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, kila kuma da Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Shugaban Majalisar Tarayya, Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha.