Abin da ya sa zan taimaki matan Najeriya – Dangote
Yanzu haka Alhaji Aliko Dangote ya fara ba da gudunmawar kudi ga mata abin da ya ce zai karade kananan hukumomin Najeriya 774, kuma ya fara ne da matan Jihar Kogi. Aminiya ta zanta da shi a Legas kafin ya wuce Kogi wurin ba da gudunmawar kamar haka: Aminiya: Ranka ya dade, ga shi za […]

Yanzu haka Alhaji Aliko Dangote ya fara ba da gudunmawar kudi ga mata abin da ya ce zai karade kananan hukumomin Najeriya 774, kuma ya fara ne da matan Jihar Kogi. Aminiya ta zanta da shi a Legas kafin ya wuce Kogi wurin ba da gudunmawar kamar haka:
Aminiya: Ranka ya dade, ga shi za ka tafi Jihar Kogi domin tallafa wa mata, me ya sa ka zabi mata alhali talauci bai san mace ba, bai san namiji ba?
Dangote: Abin da ya sa muka zabi mata shi ne kusan mata su ne jagororin gida, domin sau tari idan wani abu ya taso su ne ke fara karo da shi su da yara, su ne ke tabbatar da komai na gida na bisa tsari. wadannan su ne muka duba. Kuma idan ka lura za ka cewa mata sun fi tattali sai kuma muka sake duba cewa in kana so ka yaki talauci, idan ka agaza wa mata ana sa ran za ka samu nasara. Mun san su ma maza na fama da talauci, amma a yi tattalin abin gida sai mata, to ka ji dalilin da ya sa muka zabi mata kurum
Aminiya: Wannan tallafi kyauta ne ko rance za su biya cikin wani lokaci?
Dangote: A’a kyauta ne, kuma fatan shi ne cikin kankanen lokaci mu yi hakan a dukkan kananan hukumomi 774 da ke kasar nan, duk da yake mun yi haka a Kano. Kuma a bisa bincikenmu ya yi tasiri kwarai da gaske, domin kowace karamar hukuma a Jihar Kano an ba mata 1000 ne, kowace mac e an ba ta tallafin Naira dubu 10. A Kano ba tsaya ga mata kawai ba har da maza, kuma Naira miliyan 160 muka rarraba musu. Bayan mun yi na maza ne muka yi na mata inda mata dubu 44 suka amfana da shi. Haka kuma mun yi a Jihar Jigawa, to, yanzu za mu je mu yi a Jihar Kogi. To, kuma saboda halin da mutane suke ciki a jihohin Borno da Yobe da Taraba, mun yi a haka a jihohin kuma nasu ya fi na sauran jihohin musamman Jihar Borno domin kimanin Naira miliyan 500 muka ba su, Adamawa kuma Naira miliyan 300 da wani abu, Yobe Naira miliyan 360 gaba daya jihohin uku mun ba su sama da Naira miliyan dubu daya ne.
Aminiya: To, yallabai akwai wani shiri da aka yi ne, domin ganin wadanda aka ba tallafin sun yi amfani da shi yadda ya dace?
Dangote: Abin da muke yi shi ne, gwamnatocin jihohin su ne za su horar da su irin sana’ar da za su yi, idan an ba su tallafin, su za su ba da sunayen wadanda za su amfana, su za su kula da su. Duk da yake kyauta ne amma muna hada hannu da gwamnatociin jihohi domin tabbatar da sun yi amfani da kudin yadda ya kamata.
Aminiya: Ka ce shirin zai game Najeriya ne, bisa ga bayanin da ka yi kusan Arewacin Najeriya ne suke amfana da shi, yaushe shirin zai matsa zuwa sauran sassan Najeriya?
Dangote: Abin da ka fada gaskiya ne, yanzu idan ka duba shi ne bayan mun gama da jihohin Kano da Jigawa da Kogi, kamata ya yi a ce mun yi a jihohin Legas da Osun da Ogun. To, amma saboda halin da aka shiga a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, mutane suna cikin kunci da damuwa musamman na rashin fitar nan, sai muka yi shawarar cewa bari mu koma can mu yi tukunna kafin mu gangaro jihohin Kudu da na lissafa. Muna fata da zarar mun kammala na Jihar Kogi bayan mako biyu ko uku za mu yi na jihohin Legas da Ogun da Osun, daga nan sai mu yi a wasu jihohin Kudu maso Gabas.
Aminiya: To da yake jihohin Najeriya sun bambanta a girma da yawan jama’a, shin wannan tallafin daidai ake ba jihohin ko kuwa abin da ake bayarwa ma ya bambanta?
Dangote: Kowace muna yi a bisa karamar hukuma, misali ka ga Kano da Jigawa akwai bambanci, Jigawa na da kananan hukumomi 27 ne, Kano tana da kananan hukumomi 44, idan kuma ka dubi Borno tana da 27, Adamawa 21, don haka muna yi bisa la’akari da yawan kananan hukumomi. Misali ka ga Jihar Legas duk girmanta kananan hukumomi 20 take da su, to, amma saboda yawan jama’a Legas ba za mu ce mu ba ta daidai da jihohin da ke da yawan kananan hukumomi daidai da ita, kuma yau shekara 33 ina kasuwanci a Legas kusan duk abin da Allah Ya yi mini a nan Legas yake. Don haka ba yadda zan ba jihar daidai da sauran jihohi masu adadin kananan hukumomi daidai da ita kamar yadda na fada maka tun farko. Haka kuma idan ka dubi Jihar Borno ita ma saboda halin da jama’ar suka shiga maimakon mu dauki mata 1,000, sai muka dauki 1,500. Har ila yau shirin domin mata kawai, to amma a Jihar Borno sai muka sa matasa domin mun san cewa ana amfani da su wajen tada zaune-tsaye, sai muka duba muka ga cewa idan an samar musu abin yi za a dan samu saukin halin da aka shiga, sai muka sa su ciki amma ba wata jihar da muka sa maza ciki ban da jihar ta Borno.
Aminiya: Nawa wannan shirin zai ci a jimlance ko sai an gama za a san nawa aka kashe?
Dangote: Abin da ke nan shi ne, misali ka ga a wani wuri kamar Kano mun yi sau biyu, kamar irin su Yobe da Borno mun yi na matasa wanda babu shi a lissafin, kuma maimakon mata 1,000 da muka sa a tsarin farko sai muka canja zuwa 1,500. To ka ga ka ce mace dubu a kowace karamar hukuma ban da Kano da muka yi sau biyu, idan ka yi lissafi za mu kashe Naira biliyan bakwai zuwa takwas, amma idan ka hada da wadanda muka yi kari da wadanda za mu yi, wanda ba mu san da shi ba, nan gaba kafin mu kare ina ganin zai kai Naira biliyan 10.
Aminiya: Ka samar da Gidauniyar Dangote ce domin tallafa wa masu karamin karfi, kuma kana cikin kwamitin bunkasa tattalin arzikin Najeriya, yaya za ka kwatanta wannan gidauniya da wancan tsari na gwamnati domin ganin talaka ya amfana da shi?
Dangote: To ka san abin da gwamnati ke yi tsari daban ne, mu ma wanda muke yi tsari daban ne, amma muna duba yiwuwar haduwarsu. Misali gwamnati tana da shirye-shirye daban-daban da take yi wanda mu ma muna da kwatankwacinsa. Bari in ba ka misali, gwamnati ta ce tana so a samu aiki da yawa, ba ma irin Arewa, mu ma muka ce wannan na daya daga cikin irin abin da muke so jama’a su amfna da shi. Kamar shigo da sukari ka ga tun da muna wannan harkar, sai muka ce bai kamata a ce mu ci gaba da shigo da sukari daga waje ba, maimakon haka yanzu za mu sa wajen Naira biliyan 240 a Jihar Adamawa domin noman rake a Sabanna da kuma Taraba da Kwara da Jigawa da Kebbi. Za mu yi noman rake na tan miliyan daya da rabi, wannan adadi akwai wadanda za a ba su, su je su noma su dawo su sayar mana, wannan zai sa mutane sama da miliyan daya su samu aikin yi. Wannan ya fi ka dauki mutum aiki, domin za a samu mutum da iyalinsa ne a ce ku dauki eka ko hekta guda ku noma, mu za mu ba da wuri da kayan aikin har mu gwada musu yadda za su yi, mu za mu ba su taki, raken da za su noma idan sun gama sai mu ce su kawo mana mu saya. Ka ga wannan zai sa mutane su samu dukiya da wuri, domin ba abu mai kawo wa kasa kudi da wuri kamar noma, sabanin abin da mutane ke cewa wai noma sana’ar marar kudi ne. Ni ban yarda ba, noma na masu kudi kuma talaka ma na yi, ba wata hanya da ta fi saurin kawo wa kasa arziki da ta fi ta noma.
Aminiya: Mutane za su ce kana kwai-kwayar abin da masu kamfanonin hakar man fetur ke yi a yankin Neja-Delta ne ganin cewa kana da kamfanin yin siminti a Obajana a Jihar Kogi, me za ka ce?
Dangote: A’a ko kusa ba haka ba ne. Abin da muke yi shi ne abin da Bature ke kira Corporate Respnsibilities (gudunmawar kamfanoni ga jama’a), kuma muna wannan daban da wanda muke yi. Misali al’ummar Obajana lokacin da muka je ba su da wuta ba su da ruwa ba su da hanya ba su da makaranta, amma zuwanmu duk mun samar musu wadannan abubuwa. Akwai ma cikinsu da muka dauka muka gina musu gidaje 139, mun kashe wa al’ummar kusan Naira biliyan biyu. Haka idan ka je Ibeshe a Jihar Ogun inda muke da wani kamfanin siminti, za ka ga titin da muka yi musu na kankare ne ba ma kwalta ba, mun yi musu wajen kilomita 10, akwai kuma wanda za mu yi musu na kilomita 25, wannan kawai za mu kashe wajen Naira biliyan shida, to, wannan shi ne wanda kamfanonin mai ke yi. Wannan daban ne, amma kamar aikinmu na Gidauniya abubuwa daban-daban muke yi bayan kudi da muke bayarwa akwai abinci da muke bayarwa, akwai zakka da ake raba wa mutane saboda haka akwai kudi da yawa da muke rabawa na Gidauniyar, kuma muna da wani shiri tsakaninmu da Bankin Masana’antu wanda muka ware kudin da yawansu ya kai Naira miliyan 250 da za su rika ba talakawa rance tare da karbar kasha biyar na ruwa, amma ba cikin kudin da muka ba su ba, cikin nasu da suka hada da namu domin ya kara yawa kuma kashi biyar din a shekara ne, sabanin wancan da na yi maka bayani da farko.