Abin da ya sa zan tsaya takarar sanata – Dan Malikin Gumel
Ka gabatar da kanka? Sunana Dokta Muhammed Musa Umar dan Malikin Gumel, Darakta Janar na Cibiyar Horar da ma’aikata ta Jihar Jigawa MDI kuma memba na Nigerian Institute of Strategic Studies. Mene ne gaskiyar maganar za ka tsaya takarar sanata? Gaskiya ne zan fito takara daga yankin da na fito, kuma zan fito takarar ne […]
Ka gabatar da kanka?
Sunana Dokta Muhammed Musa Umar dan Malikin Gumel, Darakta Janar na Cibiyar Horar da ma’aikata ta Jihar Jigawa MDI kuma memba na Nigerian Institute of Strategic Studies.
Mene ne gaskiyar maganar za ka tsaya takarar sanata?
Gaskiya ne zan fito takara daga yankin da na fito, kuma zan fito takarar ne a karkashin jam’iyyar APC saboda in kare bukatun da muradun jama’ata saboda har yanzu talakawan yankin da na fito wato Gumel da Kazaure da Ringim ba su san amfanin sanata ba a matakin siyasa da kuma a aikace ba. Zan tsaya takarar kujerar sanata mai wakiltar Gumel da Ringim da masarautar Kazaure, inda zan wakilci kananan Hukumomi 12 a Majalissar Dattawa daga wadannan masarautu uku.
Me ya sa kake son tsayawa takarar sanata duk da cewa yanzu haka sanatan dan garinku ne?
Abin da ya sa nake son tsayawa shi ne yadda ya gaza kuma bai tsinana wa jama’a komai ba, kuma tsawon wadannan shekaru ba mu da wakilai na kwarai a Majalissar Dattawa, saboda ita majalisa wuri ce da ke bukatar a yi magana da turanci, ba waje bane da za a je a yi barci. Su kuwa wadanda suka wakilcemu tsawon wannan lokaci ba sa iya yin magana a zaman majalissa koda da Hausa ne. Ba su taba gabatar da bukatun mutanen da suke wakilta ba daga kananan Hukumomi da suke wakilta ba. Shi ne ya sa na ga ya dace in fito domin in kwato mana ‘yancinmu kamar yadda sauran wakilai suke yi wajen kare muradun jama’arsu a Majalissar. Ba wai domin wata manufa ba ko hassada ko kyashi ba.
Ko kun samu sabani ne da sanata na yanzu da ya sa kake neman kujerarsa?
A,a, babu wani sabani, abokaina ne dukansu daga shi sanata Ojo har danladi Sankara mutane na ne, muna girmama juna da su, amma akwai dai bukatar a samu sauyi domin samu wanda ya san mulki da siyasa da gogewa wajen magana a cikin taron jama’a, domin ita siyasa aba ce da take da bukatar a yi magana. Ba fariya ba na san siyasa gwargwadon hali a zama na da gwamnoni, bayan haka kuma karatuna na digiri da na yin a yi ne a fannin ilimin harkokin siyasa, don haka ina gani idan na yi takarar Majalissar Dattawan, ilimi na da kwarewa ta za ta amfani jama’ar da zan wakilta da ita kanta Jihar Jigawa da Najeriya baki daya.
Ta wace fuska sanatocin da ka lissafa suka gaza?
Akwai abubuwa da ya kamata su yi ta fuskoki da dama amma ba su yi ba, kuma akwai abubuwa da ya kamata a yi wa talakawa amma ba a yi ba, an san aikin dan majalissa shi ne yin doka, amma duba da yanayin da kasa take ciki da irin halin da al’umma suke ciki ya zama dole su kansu wakilan su yi tunanin sama wa mutane madogara wanda za su dogara da kansu domin zai magance jagaliyar siyasa, kuma da dama ita ce take hana su zuwa kauyukansu.
Misali kamata ya yi daga zuwansu majalisa su gabatar da kudirin da zai sa Gwamnatin Tarayya ta bunkasa Kasuwar Maigatari wadda kasuwa ce da take kan iyakar kasa, hasalima kasuwar duniya ce da kasashen Afirka suke zuwa ake harkokin cinikayya. Inganta kasuwar zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin Najeriya da Jihar Jigawa domin arziki zai zo kusa da jama’a.
Kaga da a ce nike wakiltar yankin a matsayin sanata, zan yi iyakan kokarina na gabatar da kudiri domin a janyo layin dogo daga karamar Hukumar Gagarawa zuwa kasuwar duniya ta Maigatari kuma a gyara hanyoyin mota daga Maigatari zuwa Kano zuwa Hadejia zuwa kasuwar Gujungu
Ba yankinmu ba kawai, ita kanta tashar jirgin sama da gwamnatin jiha ta gina lokacin tsohuwar gwamnati in aka ce an inganta kasuwar duniyar ta Maigatari, harkoki za su bude saboda baki zasu rika shigowa suna fita ka ga matasa da dama za su samu abin yi.
Amma ba ka ganin watakila mutanenka sun fi son sha yanzu magani yanzu?
Kuma shi ne abu mai sauki domin na san halin da mutane na suke ciki, na san abu ne mai wahala, amma kuma abu ne mai sauki a wajen Gwamnatin Tarayya jawowa layin dogon daga Gagarawa zuwa kasuwar duniya da ke Maigatari wanda hakan zai inganta rayuwar mutane.
Yaya kake ganin rikicin manoma da Gwamnatin Jiha ?
Ko ina suna da irin tasu matsalar, ni dai a iya fahintata na lura akwai karancin bayani daga wasu wakilai da suke wakiltar yankinsu, wanda ke neman gurbata tunanin mutane saboda ba su fahimci yadda al’amarin yake ba, kuma kamata ya yi a cire son rai da siyasa a yi abin da zai kawo cigaba da inganta rayuwar al’umma.
Wane sauyi kake tunanin za ka iya kawowa ?
Zan kafa gidauniya domin inganta rayuwar al’ummata, amma fa ba zan bayyana komai ba sai lokacin ya yi saboda kowa yana da tsare tsarensa saboda kada na ba wani satar amsa.
Kuma zan bude cibiya a masarautu uku na yankin da nake wakilta kuma duk inda suke da wasu ma’adanai zan yi iyakacin kokarina na ganin cewa irin wadannan ma’adinai talakawa sun fara cin moriyarsu ta hanyar samar da kamfanin da ’yan kasa za su amfana da su.
Kana ganin za ka iya bugawa da wadannan sanatocin?
Ai sha’anin siyasa ba kudi bane kawai, kuma ita siyasar kudi idan ta kazanta ba ta da dadi, Shugaba Buhari yana bakin kokarinsa wajen saita kasarnan akan tafarki na gari na hana siyasar kudi, wannan zai taimaka wajen dakile rashawa.