Abin da ya sa zan yi takarar Majalisar Dattawa – Bala Banted

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Mista Barnabas Bala Banted ya ce ya tsaya takarar dan Majalisar Dattawa ce, duk da yana Mataimakin Gwamna, ba don komai ba sai don irin halin da wadansu marasa kishi suka jefa yankin cikin wani hali na rashin alkibla. Ya ce ba kamar yadda wadansu ke yadawa ba ne cewa Gwamnatin […]

Abin da ya sa zan yi takarar Majalisar Dattawa – Bala Banted
Abin da ya sa zan yi takarar Majalisar Dattawa – Bala Banted

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Mista Barnabas Bala Banted ya ce ya tsaya takarar dan Majalisar Dattawa ce, duk da yana Mataimakin Gwamna, ba don komai ba sai don irin halin da wadansu marasa kishi suka jefa yankin cikin wani hali na rashin alkibla.

Ya ce ba kamar yadda wadansu ke yadawa ba ne cewa Gwamnatin Malam Nasir El-Rufa’i ta yi tutsu da shi, don haka ta ingiza shi zuwa ga kamun gafiyar baidu ta yadda a karshe zai zama ba ya ga tsuntsu ba ya ga farko, inda ya musanta wannan zargin tare da bayyana cewa shi ne da kansa ya ga ya kamata ya yi wa Kudancin Kaduna kyakkyawan wakilci a Majalisar Dokoki ta kasa ganin yadda aka yi mata nisa a fannoni da dama.

Shugaban APC na karamar Hukumar Jama’a, Ibrahim Koli ya yi kira ga jama’ar Kudancin Jiha su shafa wa kansu ruwa su dawo su rungumi jam’iyyar don samun ci gaban yankin musamman a zabubbukan da ake tunkara a badi.

Shugaban ya yi kiran ne a Kafanchan yayin ganawa da shugabanni da sauran masu ruwa- da-tsaki na jam’iyyar da kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Barnabas Bala Banted. Da yake nasa bayanin, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kaduna, Paul Manya Dogo ya ce wannan tafiya ce wacce ke cike da alheri ga mutanen Kudancin Jihar don haka ya yi kira ga jama’a su fito su kada masa kuri’a don cin moriyar dimokradiyya.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa