Abin da ’yan fim suka ce kan harin jirgin kasa na Kaduna
Saura kiris hari ya rutsa da ni.
A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan ta’adda suka kai wani mummunan hari wa jirgin kasa da ke jigila a tsakanin Kaduna zuwa Abuja, wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 9, ya jikkata da dama, tare da sace wadansu.
Lamarin ya jawo maganganu daga bangarori da dama, ciki har da Kannywood.
Darakta Falalu Dorayi ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa, “An kashe wasu, an debi wasu, wasu sun bata.
“Ya Ubangiji! Ka jikan wadanda suka rasu, wadanda aka dauka Allah Ka tsare mutuncinsu Ka ba su sauki da mafita. Ka ba wa iyalai da ’yan uwansu hakuri.”
Falalu ya kara da cewa, “Jiya (Litinin) har karfe 3:00 muna waya da wanda abin ya rutsa da su kafin a kawo su Kaduna.
“An yi rashin imani, Allah Ya tsare gaba, Ya kare mu da iyalanmu da al’umma baki daya.
“Allah Ya tona asirin wadannan ’yan ta’adda. “Su kuma shugabanni Allah Ya tayar da su daga barcin da suke su dubi al’umma. Amin.”
Ali Nuhu ya yada rubutun na Falalu Dorayi a shafinsa, sannan shi ma furodusa Alhaji Sheshe ya yada rutubun.
Rashin addini ne ke damunmu —Naziru Ahmad
A nasa bangaren, Naziru Ahmad, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Waka ya yi dogon rubutu, inda ya ce akwai rashin addini a tattare da mutane da har suke tunanin za a samu sauki, alhali su ba canja ba.
“Duk rashin addini ne ya sa da yawanmu muka kasa gano me ke jawo wannan abu.
“Ku sani fa, Allah ba zai tashi alkawarinSa ba a kan wadanda ba su yarda su bi Shi ba, alhali suna amasa sunan Musulunci.
“Duk irin shugaban da za mu zaba, mu zaba mu gani. Manyanmu ba za su iya hada kansu ba, sai mun hada kanmu.
“Ba za mu iya zabar shugaba nagari ba, har sai mun zama mutane nagari. Allah Ya sa mu dace, amin.”
Saura kiris hari ya rutsa da ni —Rahama Sadau
Da take bayani kan harin, jaruma Rahama Sadau ta bukaci ’yan Najeriya su zabi shugabanni nagari domin samun maslaha.
Ta ce, “Yanayin jami’an tsaron da suka je filin wasan kwallon Najeriya da Ghana alama ce da ke nuna Najeriya za ta iya dakile matsalar tsaron nan, amma aka ki.
“Ya kamata a ce ni da kanwata muna cikin jirgin nan da aka kai wa farmaki, amma sai ba mu samu shiga ba.
“Watakila da harin ya rutsa da ni. Amma ya shafe mu tunda muna da ’yan uwa da abokan arziki a ciki.
“Wai yaushe za a kawo karshen wannan matsalar? Kuma ganin zabe yana karatowa, watakila lamarin ya zafafa.
“Kuma Arewa ke shan wahala. Ina kira ga mutane da mu nemi katin zabenmu mu zabi mutanen kirki.”