Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan rashin ganin wata

Ina cikin masu azumin yau, amma lamarin sai an sake dubawa.

Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan rashin ganin wata

Wata

Al’ummar musulmi musamman ma a Najeriya na ta bayyana ra’ayinsu kan sanrwar da ta fita daga fadar Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar III dangane da batun rashin ganin watan sallah a ranar Asabar.

Wannan batu dai ba a bana ne aka fara samun hatsaniya kansa ba, domin kuwa duk shekara wasu daga cikin al’umma kan koka kan sanarwar fadar sarkin muslumi na ganin watan ko akasinsa.

To sai dai abin ya fi tsamari a baya-bayan nan da aka fi yin azumin watan Ramadan din 30, inda wasu dai na ganin kwaikwayon kasar Saudiya ne ya sanya hakan ke faruwa.

A shafukan sada zumunta ma dai lamarin na kara daukar hankali musamman bayan bullar batun Jagoran Darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi na cewa a ajiye azumi amma sallar idi sai ranar Litinin.

Hujjar malamin dai ita ce ya amince da wadanda suka ba shi rahoton ganin wata a yankunansu.

A Jihar Sakkwato da ke zama mahaifar sarkin Musulmin, an samu limamin da ya jagoranci sallar idi, inda a yanzu bidiyonsa ya karade dandalin sada zumunta na Facebook.

Haka ce ta sa Aminiya ta garzaya shafin Facebook inda ake ta muhawara kan wannan batu, muka kuma zakulo muku wadannan ra’ayoyi na wasu daga cikin ’yan Najeriyar.

“Ina cikin masu azumin yau, amma lamarin sai an sake dubawa” in ji  fitacciya a Dandalin Sada Zumunta, kuma marubuciya wato Rahama Abdulmajid.

Shi kuwa Lauya kuma fitacce a duniyar Facebook, Barr Abba Hikima cewa yayi: “Ni matsala ta da harkar ganin watan nan daya ce: ko dai ayi amfani da science [kimiyya] zalla wurin duban watan a hutar da jama’a masu dubawa tunda science [kimiyyar] ta yanke hukunci, ko kuma a bar jama’a su duba yadda aka saba yi tun zamanin Annabi SAW.”

Shi ma dai wani mai suna Aliyu Dahiru Aliyu wanda aka fi sani da Sufi cewa yayi”: Maganar ganin wata Ijtihadi ne muddin da Ikhlasi a ciki”

Muslim Muhammad Yusuf cewa yayi “in banda rashin kunya na mutanen mu ‘yan arewa kai ka taba jin Alaafin of Oyo, ko Ooni of Ife ko wani Oba ya yi magana ko da akan kuskure ne al’ummarsa sun nuna rashin da’a ko da wasa?”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos