Abin da ’yan Najeriya suke cewa kan Harin Mauludin Kaduna

Hare-haren jiragen soji 16 da sojoji suka ce na kuskure ne, sun auku ne a yankin Arewac, inda aka kashe mutum sama da 400

Abin da ’yan Najeriya suke cewa kan Harin Mauludin Kaduna

Kabarin mamatan harin kuskuren jirigin soji a yankin Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.

A yayin da shugabanni da kasashen duniya ke nuna alhini game da rasuwar mutum kimanin 100 da jirgin sojin Najeriya ya jefa wa bom a taron Mauludi a Kaduna, al’ummar kasar na ci gaba da yin tsokaci kan al’amarin.

Harin da jirgi mara matuki ya kai ’yankin Tudun Biri a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, shi ne irinsa na 16 da jiragen sojojin Najeriya suka kai kan fararen hula daga shekarar 2014 zuwa yanzu.

Duk wadanan hare-hare, da sojoji suka bayyana a matsayin na kuskure, sun auku ne a yankin Arewacin kasar, inda suka yi ajalin mutum sama da 400.

Hakan ya sa bayan aukuwar na garin Tudun Biri, inda akalla mutum 66 suka samu rauni bayan wasu kimanin 100 da suka rasu, ’yan Najeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu.

Ga abin da suke cewa bayan karanta rahotannin da Aminiya ta wallafa kan lamarin a shafinta na Facebook:

Ahmed Philip  a tsokacinsa kan fitaccen malami, Alkali Ustaz, da ke cewa a Arewa abia da ya kira ganganci ke faruwa, ya ce “Wallahi inda Kudu ne wanna abun ya faru, da kasar nan yanzu ta yi shut down.”

Shi kuwa Auwal Salisu, ce ya yi, “Ya kamata masu manyan riguna su yi magana tun da an yi a katsina, ga kaduna. Shi ke nan haka za a tafi rana zafi inuwa kuna?”

A tsokaincinsa kan kan bayanin Mininstan Tsaro, Badaru Abubakar da ya ce gwamnati za ta biya diyyar wadanda suka rasu, ya ce, Idris Sa’idu ya ce, “Ba diyya kadai ne muke bukata ba, a yi bincike don a gano dalilin da ya sa [sojoji] suke yin haka, sanan kuma a hukunta su da su da wayanda suke taimaka musu.”

Abubakar Baffa, ya ce, “kun ji sun fara maganar diya ko, Allah Sarki talaka, za a fidda kudin sai a neme shi a rasa.”

Nura Ibrahim Chadi ya kara da cewa, “E. Amma a yi maganin faruwar haka shi ne matsalar. Kuma ku magance matsalar tsaro a Arewa”

Shi ko Muhammad Sambo Imti’az, lissafa kiyasin kudin diyyar a Musulunce ya yi, inda ya rubuta, “128,212,000 × 100 = 12,821,200,000. Allah Ya ba da Ikon biya.”

“Kyau ayiwa jami’an ritaya daga aikin nasu ko an rage irin wannan gangancin da suke yi wa ’yan Arewa. Babbar matsalar wasunsu ke dawowa suna zama ’yan ta’adda saboda suna da ilimi a kan al-amurran. Kawai a dauki kwakkwaran mataki a kansu tun da wasunsu kamar dabbobi suke a kan kudi.”

Shi kuwa Abdull Abdulhmeed Agwai, cewa ya yi, Mu ba diyya kadai muke bukata ba, indai jama’a ne ake musu aiki to muna da bukatar wadanda suka aikata wannam laifin su ma a hukunta su daidai da doka da kuma adalci.”

“Mufa ba ta’aziya muke so ba, adalci muke so ayi. A zakulo wadanda suka yi wannan danyen aikin a hukuntasu bisa rashin kwarewarsu a aikinsu. Sannan Gwamnati ta gaggauta biyan diyar mutanen da suka rasa rayukansu tun da ba ita ta ba su ba,” in ji Mohd Salisu Shafi’u.

Muhd Kasim Nadabo ya ce, “An yi sakaci ana kashe mutanen Arewacin Najeriya, yanzu kuma an hada da kashe su da bomb na sojoji… Ya Allah Ka yi mana maganin wadannan musibu da zaluncin da aka yi ma bayinKa, a musamman Arewacin Najeriya da Palestine.

 

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume