Abin da ’yan Shi’a suka yi a Zariya ba daidai ba ne sai dai – Sheikh dahiru Bauchi
Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce matakin da mabiya Shi’a suka dauka na toshe hanya a garin Zariya ba daidai ba ne. Sannan matakin da hukumomin tsaro suka dauka a kansu na bude musu wuta, shi ma ba daidai ba ne. A cewarsa, hanya ta gwamnati ce kuma gwamnati tana […]
Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce matakin da mabiya Shi’a suka dauka na toshe hanya a garin Zariya ba daidai ba ne. Sannan matakin da hukumomin tsaro suka dauka a kansu na bude musu wuta, shi ma ba daidai ba ne.
A cewarsa, hanya ta gwamnati ce kuma gwamnati tana da izinin rushe gidan mutum ta maida shi hanya in ta ga dama ta biyashi diyya, ya karbi kudin ko kada ya karba ruwansa.
“Kowa ya san cewa hanya a kowace kasa take a duniya, ta gwamnati ce, saboda haka mutum ya toshe hanyar gwamnati laifi ne. Amma da abin da ya kamata hukumomi su yi a lokacin shi ne, su fesa musu barkonon tsohuwa ko ruwan zafi ko su yi amfani da harsashin roba maimakon harbi da bindiga,” inji malamin.
Ya ce: “Allah Ya ce duk wanda ya yi muku ta’addanci, ku rama amma su wanda aka toshe musu hanya da suka zo ramawa sai suka rama fiye da abin da aka yi musu.”
Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Bauchi a ranar Talatar da ta gabata. Ya ce Allah ba Ya son a rika zubar da jinin dan Adam saboda haka ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Daga karshe ya yi amfani da wannan dama, inda ya shawarci almajiran Sheikh Ibrahim Zakkaky cewa su yi hakuri game da abin da ya faru a Zariya. “Idan mutum ya yi hakuri Allah zai ba shi lada babu lissafi. Kada su rama, domin yin haka ba zai haifar da alheri ba ga kasar nan,” inji Shehin.