Abin da za mu yi Allah Ya so mu (2)

Mu sake tambayar kanmu, “Shin Allah Yana sonmu?” Idan har muna ji a jikinmu cewa Allah ba Ya son mu saboda ba mu aikata abin da ya dace, to ’yan uwa mu yi wa kanmu kiyamul laili, mu tuna da karashen wannan Hadisi da muka fara kawowa, mu guje wa abin da zai fusata Allah. […]

Abin da za mu yi Allah Ya so mu (2)

Mu sake tambayar kanmu, “Shin Allah Yana sonmu?” Idan har muna ji a jikinmu cewa Allah ba Ya son mu saboda ba mu aikata abin da ya dace, to ’yan uwa mu yi wa kanmu kiyamul laili, mu tuna da karashen wannan Hadisi da muka fara kawowa, mu guje wa abin da zai fusata Allah. Mu guji mutanen da suke aikata ayyukan da suke fusata Allah. 

Domin Manzon Allah (SAW) ya fadi a karshen Hadisin cewa: “Idan kuma Allah Ya ki mutum (saboda saba maSa), zai kira Mala’ika Jibril (AS) Ya ce masa: “Ya Jibrilu! BawaNa wane dan wane yana ci gaba da fusata Ni, don haka fushiNa ya tabbata a gare shi.”  

Ke nan samun so daga Allah yana ta’allaka ne da bin abin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na daga ayyukan da’a.

Kuma Allah Yana daukar duk wanda ya yi maSa biyayya a matsayin masoyinSa. Shi ya sa za mu ga Alkur’ani da Sunnah cike suke da darussan da suke nuni kan yadda za mu samu soyayya daga Allah Subhanahu Wa Ta’ala. 

Babban ginshikin samun soyayya a tsakanin bawa da Ubangijinsa, shi ne yin imani da yin aiki nagari. “Lallai wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai (nagari), wadannan su ne mafifita alherin halitta. Sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shi ne gidajen Aljanna koramu na gudana a karkashinsu, suna madauwama a cikinsu har abada. Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa.” (k:98:8).

 Ibnu kayyim (Rahimahullah) ya rubuta hanyoyi da dama da za mu bi, mu samu son Allah Subhanahu Wa Ta’ala kamar haka: 

Na daya: Mu rika amfani da sulusin karshe na dare wajen yin nafilfili da karatun Alkur’ani da zikiri da hailala da sauran ibadoji na gabbai. Domin Annabi (SAW) ya ce a irin wannan lokaci: “Allah Madaukaki Yana sauka zuwa saman duniya, Ya rika kiran mutane: “Ko akwai masu addu’a, in amsa musu! Ko akwai masu neman gafara in gafarta musu!” Don haka mu ci moriyar wannan lokaci ta wajen nafilar kiyamul Laili.

Na biyu: Mu rika ambaton Allah (zikiri) a kowane lokaci. Ko a wurin aiki ko sana’a ko muna tsaye ko a zaune, mu rika amfani da wannan lokaci mu rika ambaton Allah. Mu rika tuna Allah a cikin duk abin da za mu aikata, ko za mu ci, ko za mu sha. Domin Allah Ya ce: “Saboda haka ku tuna Ni, In tuna ku.” (k:2:152).  Wane ne ba ya son Allah Ya rika tunawa da shi?

Na uku: Wajibi ne mu rika karanta Alkur’ani tare da fahimtar ma’anarsa. Mu karanta abin da Allah Ya saukar mana domin rayuwarmu da mutuwarmu. Allah Madaukaki Ya ce: “Shin ba za su yi tadabburi (nazari ko kula) da Alkur’ani ba.” (k: 4: 82).

Kuma Allah (SWT) Ya sake cewa: “(Wannan) Littafi ne Mun saukar da shi zuwa gare ka yana mai albarka, domin su lura da ayoyinsa, don masu hankali su rika yin tunani.” (k:38:29).  

Na hudu: Mu zauna tare da mutanen da suke son Allah (SWT), so na gaskiya, mu tafiyar da lokacinmu a wurinsu. Domin a cikin Surar Khafi, Allah (SWT) Ya ce: “Za su ce, “Uku ne da na hudunsu karensu. Kuma suna cewa, “Biyar ne da na shidansu karensu,” a kan jifa cikin duhu. Kuma suna cewa, “Bakwai ne da na takwas dinsu karensu.” Ka ce, “Ubangijina ne Mafi sani ga kidayarsu, babu wanda ya san su face kadan.” (k:18:22).

A wannan aya Allah Madaukaki Ya ambaci karen Mutanen Kogo sau da dama. Don me? Saboda abokan tafiya da karen yake da su mutanen kirki ne, shi ya sa aka ambace shi sau da dama. To idan za a ambaci kare a Alkur’ani sau da dama saboda wadanda yake tare da su mutanen kirki ne, to ka ji mamakin yadda Allah zai so mutumin da ya zabi ya tafiyar da lokacinsa ta zama tare da mutanen da Allah Madaukaki Yake so.  

Annabi (SAW) ya koya mana cewa misalin abokin zama nagari kamar mai sayar da turare ne. Koda bai ba ka turaren ba, za ka sha kanshi.

Na biyar: Wajibi ne mu so haduwa da Allah (SWT), Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda Yake son haduwa da Allah, (lami lafiya) to, Allah ma Yana son haduwa da shi.”

Ko shakka babu idan mutum yana son haduwa da Allah Madaukaki lami lafiya, zai rika yin ayyuka nagari don haduwa da Shi, zai yi tattalin wannan haduwa. Wanda kuma ba ya son haduwa da Allah zai tafiyar da rayuwarsa cikin sabon Allah. Ba zai so haduwa da Allah (SWT) ba, kuma Allah ba zai so haduwa da wannan bawa ba.

Na shida: Mu kawar da duk wani abu da zai shiga tsakaninmu da Allah Madaukaki. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya umarce mu, cewa mu yi dubi da idon basira kan kowane al’amari da muke yi, mu guji duk abin da ya saba wa Allah. 

Na bakwai: Kullum mu sanya Annabi (SAW) a gaba wajen koyi da shi. Mu sanya bukatunsa a kan bukatunmu. Domin Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce: “Idan kun kasance kuna son Allah, to, ku bi ni, Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku.” (k:3:31). 

Na takwas: Wajibi ne mu rika yin hakuri a cikin al’amuranmu. Masu iya magana sun ce hakuri ba ya baci. Sannan malamai sun ce idan mutum ya rika yin hakuri a mu’amalarsa da mutanen gidansa da makwabtansa da abokan aikinsa, sai ya zama As-sabiru (mai yawan hakuri). Allah Madaukaki kuma Ya gaya mana game da masu hakuri cewa: “Kuma Allah Yana son masu hakuri.” (k:3:146).

Na tara: Wajibi ne mu sani cewa Allah Madaukaki Yana da sunaye da siffofi masu kyau (asma’ullahil husna was-sifat). Don haka a duk lokacin da muke karanta Alkur’ani Mai girma muka ci karo da kalmar Ar-Rahman wajibi, ne mu fahimci hakikanin ma’ana da manufarta kuma mu sa ran Allah Madaukaki Ya yi mana rahama. Sannan idan muka ci karo da kalmar Assami’u da Albasiru wato Mai ji, Mai gani, wajibi ne mu fahimci cewa Allah Yana ji da ganinmu a kowane lokaci. Kuma idan muka hadu da kalmar Shadidul ikabi, Mai tsananin ukuba, to mu sani Allah Ya fi kowa yin ukuba, don haka mu tsaya mu yi tunani kafin mu saba wa Allah, don mu kaurace wa wannan aiki.

 Na goma: Mu ci gaba da yin nafilfili, wato ayyukan ibada da ba na farilla ba. Ya zo a cikin Hadisin kudusi cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Madaukaki Ya ce:  “Bawa ba zai gushe ba yana kusantaTa ta yin nafilfili har sai Na so shi…”

A sharhin Hadisin malamai sun ce wadannan ayyuka na nafila kowane nau’i ne. Ya alla nafila ta harshe kamar zikiri da karatun Alkur’ani da hailala da fadin magana mai kyau da sauransu, ko kuma nafila ta gabbai kamar Sallah da Azumi da makamantansu.

Wani mawaki ya ce: “Ta yaya za ka saba wa Allah, sannan ka ce kana son Allah?”

Wannan ’yar nasiha wata hanya ce ta fahimtar wannan so da Allah Yake yi maka ko kai kake yi maSa. Domin idan soyayyarka ga Allah ta gaskiya ce, wajibi ne ka yi masa biyayya. Kuma hakika duk wanda yake son wani ba zai yi abin da zai bata masa rai ba, sai dai wanda yake so, wanda kuma zai dadada masa. To haka lamarin ya wajaba ya kasance a tsakanin bawa da Ubangiji. 

Allah Ya sa mu dace. Wasallallahu alan Nabiyil karim wa alihi wasallim.