Abin da zai kawo karshen rikicin APC a Jihar Bauchi – MA Tukur

Alhaji Muhammad Aminu Tukur shi ne dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Lere/Bula a karamar Hukumar Tafawa balewa, ya shaida Aminiya dalilan da suka sa har yanzu ba a warware rikicin jam’iyyarsa ta APC a karamar hukumar da jihar ba. Kuma ya ce fatan da suke da shi daga uwar jam’iyyar ta kasa, shi […]

Abin da zai kawo karshen rikicin APC a Jihar Bauchi – MA Tukur

Alhaji Muhammad Aminu Tukur shi ne dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Lere/Bula a karamar Hukumar Tafawa balewa, ya shaida Aminiya dalilan da suka sa har yanzu ba a warware rikicin jam’iyyarsa ta APC a karamar hukumar da jihar ba. Kuma ya ce fatan da suke da shi daga uwar jam’iyyar ta kasa, shi ne a bi ka’ida da dokokin jam’iyyar wajen warware takaddamar: 

 

Me ake ciki game da rikicin shugabancin jam’iyyarku ta APC a karamar hukumarku?

Sama da shekara guda bayan kafa gwamnatin Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi da kasa baki daya, muke dan samun rashin fahimta a tsakaninmu da Mai girma Gwamna (Muhammad Abdullahi Abubakar), kuma rashin fahimtar ya faru ne saboda karyar alkawarin da ya yi ba daya ba, ba biyu ba ba uku ba, wanda ta dalilin haka ya sa yanzu jam’iyyar a karamar Hukumar Tafawa balewa ta dare gida biyu.

Gida biyun nan da ta dare, shi ne shugabanci na karamar hukuma wadda ke da mutum 26, mutum biyar suka bi Gwamna mutum 21 muna tare da su. A cikin biyar da suka bi Gwamnan nan akwai ciyaman, amma daga sakatarensa da ma’ajinsa da ’yan kwamitin gudanarwa biyu ne daga cikin su tara suka bijire mana, shi da Odita, saura muna tare.

Haka ya kai ga gabar da gibin ya rika karuwa, mu mun tsaya ne a kan dole a cika alkawarin da aka yi, su kuma sun dage wajen karya alkawarin da cin zarafin al’umma. To haka ake ta tafiya har ya kai ga mun fahimci rashin mutunci da fitsara ya shiga ciki har ya kai ga muna zaune an je gundumar mai girma Sanata (Sanatan Bauchi ta Kudu, Malam Ali Wakili) an zo da wadansu mutane da ba mu san da su ba, aka kawo su Bauchi suka zauna suka rubuta takarda suka ce an dakatar da Malam Ali Wakili daga kasancewarsa dan Jam’iyyar APC a gundumarsa ta Lere ta Arewa. Ganin haka muka kira taro na gaggawa, muka zo da shugabannin zartarwar jam’iyyar ta gundumarsa da na karamar hukuma rubuta takardu muka kai wa uwar jam’iyya ta jiha muka kai wa hukumar zabe ta kasa (INEC) da Kwamishinan ’Yan sanda da Darakatan Hukumar SSS, kuma muka yi hira da manema labarai muka ce wannan abin da aka fada karya ne.

A matsayinmu na zababbu, tsammaninmu shugaban jam’iyya ta jiha zai kwatanta gaskiya da adalci, amma sai muka ga babu wannan tare da shi, domin babu abin da ya yi a kai, kuma mun kai wannan kwafe ga uwar jam’iyya ta kasa, kuma a zuwan da muka yi na baya-bayan nan a Abuja, duk takardun an nuna mana su kuma sun amince cewa abin da muka yi daidai ne.

To muna cikin haka, ni kaina da shugaban jam’iyya ta gundumata wanda shi ne shugaban ciyamomin jam’iyyar na gundumomin karamar Hukumar Tafawa balewa aka ce an dakatar da mu. Wajen bin ka’idoji gara na Sanata an jingina abin da gundumarsa, ni nawa ba ma gundumata ba ce, wani abu ne ake kira jaririyar gunduma (baby ward) ta yi zama wadda ba gunduma ce mai shugabannin zartarwa ba, saboda babu ita a tsarin mulkin jam’iyya balle na kasa, haka aka kawo wadansu mutane suka ce sun dakatar da ni da shugabana. 

Ganin abin da fadi sai shugaban jam’iyya ta jiha, Alhaji Uba Ahmed Nana ya kira shugaban jam’iyya ta gundumata washegarin ranar da abin ya faru, ya ce masa shi bai yarda da duk abin da ake yi a Tafawa balewa ba, shi babu ruwansa. Amma ni bai kira ni ba, ya kira shugaban jam’iyya na gundumata ya shaida masa babu ruwansa. Kuma duk da ya fada masa haka, sai ga shi kakakin jam’iyyar ta jiha yana shiga rediyo yana ba da sanawar amincewa da dakatar da Sanata Ali Wakili da dakatar da Aminu da dakatar da shugaban jam’iyya ta gundumata.

Abin da ke faruwa shi ne kundin tsarin mulkin Jam’iyyar APC ya nuna matakan da ake bi a dakatar da mutum. Na farko sai an samu amincewar gundumarsa, sannan ba amincewa za ta yi karan kanta ba, sai ta rubuta masa takarda ta gayyata ta nuna masa laifuffukansa ya bukaci ya zo ya kare kansa, in bai yi haka ba sannan ta zauna ta ladabtar da shi, tare da mika bukatar haka ga kwamitin zartarwa na jam’iyya na karamar hukuma ya amince da abin da ta yi, kwamitin zartarwa na karamar hukuma zai zauna ne bisa rinjaye sannan ya tura wa jiha, musamman ga zababbe irina zuwa sama, sannan kwamitin zartarwa na jiha shi ma ya zauna  bisa rinjaye ya tura wa kwamitin zartarwa na kasa, shi yake da ikon ya yanke hukunci a kai, wannan shi ne abin da dokar jam’iyya ta fada, wanda babu inda aka yi haka. 

Alhaji Mijinyawa Ardo ne wanda mun dakatar da shi tare da hadin bakin shugabanci na jiha suke aiwatar da abu ba tare da bin dokar da jam’iyya ta zayyana ba.

Ganin abin ya kai ga haka, muka zauna a matsayinmu na wadanda muke da hurumi muka bukaci shi Mijinyawa Ardo ya bayyana a gabanmu, inda ya ki, sannan muka zauna muka dakatar da shi, muka rubuta wa uwar jam’iyya ta jiha, muka kai wa Hukumar Zabe muka kai wa Daraktan SSS, muka kai wa Kwamishinan ’Yan sanda, muka yi hira da ’yan jarida, muka kai wa uwar jam’iyya ta kasa wadda mun je mun gani an kai musu. Kuma bisa kalaman da aka gaya mana a hukumar zabe ko gobe idan Mijinyawa Ardo zai sa hannu a takarda a matsayinsa na shugaban jam’iyya ta karamar Hukumar Tafawa balewa ba za su amince ba, domin ba shi ne shugaba, saboda mun  bi ka’idojin da suka dace wajen dakatar da shi. 

Da ka ce abin kamar ya shafi Gwamna ne, shin akwai wata matsala ta kashin kai ne a tsakaninku da shi, ko jam’iyya ta shigo ciki ne saboda kasancewarsa Gwamna?

Eh, ita jam’iyya ta shigo ciki ne saboda makwadaita ne, wadanda suna tsoron talauci za su iya karya alkawari na tsakaninsu da jama’a, za su iya karya alkawari wanda Allah Shi ne shaida, gara su yi bambadako a kan su tsaya su yi gaskiya don su samu abin duniya. Mai girma Gwamna ya sani mu ba bayinsa ba ne, ba yaransa ba ne.

Shin an taba yunkuri na a sasanta wannan takaddama?

Yunkuri, wani iri ne ba a yi ba. Misali in fara da ni kaina, bara a watan Yuni, daren bakwai ga azumin bara, mun zauna da Mai girma Gwamna da ’yan majalisar jiha. Kowa ya yi magana, daga baya na kawo maganganuna, da kansa Mai girma Gwamna ya tashi duk ’yan majalisar suna zaune ya ce, don girmnan Allah in yafe shi, saboda ya sani mun yi masa.

Na fada da gori a gaban ’yan majalisar Dokokin Jihar Bauchi cewa babu dan majalisar da ya yi masa abin da na yi masa. Ni ne Daraktansa na Harkar Siyasa, ya san irin mutanen da na kawo masa, ya san cin amanata da ya yi, kuma ya amince da cewa tabbas ya saba alkawari a gaban dukan ’yan majalisarmu, inda ya ba ni dama ranar (wata) Asabar in je in same shi da safe. Kuma na je na same shi da shugaban jam’iyyarmu da muka dakatar da kwamishinanmu wanda aka ba shi daga Tafawa balewa da wanda ake so a lokacin ya zama shugaban riko na karamar Hukumar Tafawa balewa, muka zauna ya gaya musu cewa ya yi sulhu da ni ya ba ni hakuri su yi min biyayya, a ranar Asabar din. Amma a ranar Talata sai ga shi ya saba alkawari a kasa da mako daya, ya saba alkwarin da aka yi akan teburinsa na Gwamna.

Ta yaya ya saba alkawarin?

Saba alkawari shi ne abin da ya sa mu muka je muka rubuta aka dawo daga kan abin da ya ginu a kai, a rubuce muka yi na sa hannu da kwamishinan kananan hukumomi bai aikata ba. Mun yi irin wannan zama kafin wannan don a samu maslaha tsakaninsa da Mai girma Shugaban Majalisar Tarayya, wanda ni da shugaban ma’aikatansa da Iya Kwamanda Tijjani Baba Gamawa da dan uwansa li’abbinsa da sakataren watsa labaransa, aka yi zama a kan maslaha, ya karya wannan alkawarin zama. An yi irin wannan zama tsakanin ’yan Majalisar Dokoki ta kasa da iyayen kasa a karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Misau da masu martaba sarakunan Ningi da Dass, ana wannan zaman (a Abuja) yana cin zarafin mutane a Gidan Gwamnatin Bauchi, wanda mutane suna da shi a cikin kaset har a Intanet da sauransu, inda ake nuna mu ba komai ba ne ba kowa ba ne.

An yi ta yunkurin sulhu ba a samu nasara ba, ko kana ganin akwai wadanda suke cin gajiyar haka daga wajen Jam’iyyar APC ne?

Ai dama duk lokacin da bango ya tsage ne kadangare yakan samun wurin shiga. Akwai wadanda suka tabbatar idan komai yana tafiya daidai ba za su samu kafar da za su yi sata da barna da almubazzaranci da farraka jama’a ba, kullum ba za su so a samu kafa ta sasantawa ba. Mu abin da muke so a sani shi ne daga ni karamin har zuwa na sama, babu wanda yake neman kwabon Gwamna, babu wanda yake nema Gwamna ya azurta shi, babu wanda Gwamna ya samu matalauci fakiri ba ya iya ciyar da gidansa ko biyan kudin karatun ’ya’yansa. Abin da ke tsakaninmu da shi, shi ne alkawari na zai yi mana abin da muka zayyana masa don ci gaban al’ummarmu wanda sabanin haka ake a kai.

Kamar wadansu abubuwa kuka zayyana masa?

Na farko ba mu amince da shi a matsayin dan takara ba, sai da muka yi ka’idoji da shi cewa, mu muka san yankinmu muka san matsalar yankinmu. Ya je kamfe a wurinmu sau daya tak, abin da ya kashe Naira miliyan daya da dubu 200 a mazabar dan Majalisar Tarayyar, iya gudunmawarsa ke nan. Ko gundumata ba za ka kashe iya wanna kudi ba a irin siyasa ta yau, shi ya sani iya jarinsa ke nan a kananan hukumomin Tafawa balewa da bogoro da Dass. Mu muka yi masa komai, mu muka san wadanda suka wahala, muka tara bayanai na komai na wannan yanki muka ba shi a rubuce da wadanda suka yi hidima. Kuma ya yi mana alkawari cewa ba zai taba nada ko da masinja in ana nada masinja a siyasance, sai ya yi shawari da mu. Amma babu abu daya da ya yi shawara da mu. Daidai da kansila na riko da ya yi alkawarin zai bai wa shugabannin jam’iyya na gundumomi da shugabannin kananan hukumomi da ya yi musu alkawari a matsayina na Daraktan Siyasar bai cika ba. Alkawuran da ya yi zai ba kowane dan majalisar jiha kujerar kansiloli biyu a karamar hukumarsa, sanatoci za a ba su, babu daya da ya cika. Alkawarin da ya yi cewa ga wanda zai zamo mana kwamishina a cikin ’yan gwagwarmayarmu bai cika ba. Alkawura na ayyuka misali na zai yi hanya daga Bununu zuwa dull zuwa Gwaranga zuwa Sum, bai yi ba, alkawarin zai yi hanya a gindin dutsen Sara bai yi ba, alkawarin da ya yi na zai yi hanya a  Burgel zuwa Gore zuwa Kundun Zari zuwa boto babu ita babu alamarta. Tunda aka kafa wannan gwamnati a karamar hukumata ta Tafawa balewa wadda cibiyar siyasa ce ba jihar nan kadai ba a Najeriya, babu aiki da wannan gwamnati ta yi wanda za a ce ya kai na Naira miliyan 100.

Uwar Jam’iyyar APC ta kasa ta kafa kwamitin sulhu a karkashin Minista Chris Ngige, wanda ya zo nan Bauchi, shin ya zauna da ku, kuma me aka cimma?

Alhamdulillahi, na ga rahoton kwamitin Ngige, amma zan ce ba a yi mana adalci ba. Kalma daya da wannan kwamitin ya yi amfani da ita a kan Sanata Malam Ali Wakili ta sa mun fahimci cewa, sayayyu ne a wurin gwamnatin Jihar Bauchi. Babu kamala a cikin kalaman da kwamitin ya yi na cewa, bayanan da Sanata Ali Wakili ya yi karya ne. Kalma daya da suka yi amfani da ita ta cewa abin da ya fada untrue wato ba gaskiya ba ne wannan kawai ya nuna cewa babu adalci a cikin abin da kwamitin ya yi. Sannan abin da muka fadi tabbas sun rubuta wasu daga ciki, misali sun rubuta abin da na fadi, amma ba su fadi ainihin abin da na fadi na me ya kawo wannan rikici ba. Na yarda na ce ni ne dakaraktansa na siyasa sun rubuta na ce yana yin gwamnatinsa ba tare da mu ba, na fadi wariyar da yake yi mana, duk sun fada. Amma ba su magana a kan alkawura zaunannu da cin amana da muka lissafo wadanda ya yi wa al’umma ba.

Wannan yana nufin ba ku amince da rahoton kwamitin Ngigen ba ke nan?

Insha Allahu za mu zauna da wadanda suka damu da hidimar Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi don mu nazarci wannan rahoto na Ngige mu fitar da matsayarmu a kai. Wannan na fadi abin da ni na gani ne a rahoton, kalma daya da aka fadi a kan Sanata Ali Wakili, ya sa mun fahimci cewa wannan son zuciya ne kawai.

Wane sako kake da shi ga uwar jam’iyyar ganin cewa kun yi kokarin ganawa da ita kan wannan matsala?

Alhamdulillah, a matsayinmu na wadanda muka jima a cikin wannan harka abin da muke so shi ne adalci. Za a iya bi ciki tarihin abubuwan da muka yi za a ga ba mu taba samun kanmu a cikin hidima wadda take ta zalunci ba. Babu al’ummar da za ta ginu ta bunkasa a kan zalunci. Iya abin da muke bukata shi ne adalci, a yi mana adalci. Adalcin nan shi ne muke nema. Na ji dadin kalmar da rahoton da kwamitin Ngige ya yi amfani da ita a kan kalmar da fada ta cewa a bi dokokin jam’iyya yadda suke a cikin tsarin mulkin jam’iyya. Kawai mu abin da muke nema ke nan, a bi dokokin jam’iyya, yadda suke a tsarin mulkin jam’iyya. Wannan shi ne muke bukata.