Abin da zan sa a gaba wa’adi na biyu — Tinubu
Ya ce, batutuwan da suka mamaye ayyukan gwamnatinsa a halin yanzu su ne: tattalin arziki da tsaro, inda ya jaddada cewa waɗannan abubuwa ne masu matuƙar muhimmanci
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zai mayar da hankali ne kan matsalolin siyasa da suka rage a ƙasar idan ya kai wa’adinsa na biyu na mulki.
Ya ce, batutuwan da suka mamaye ayyukan gwamnatinsa a halin yanzu su ne: tattalin arziki da tsaro, inda ya jaddada cewa waɗannan abubuwa ne masu matuƙar muhimmanci ga ɗorewar ƙasar.
- Rikicin Gado: Sarkin Zazzau ya gargadi hakimai kan cin zalin talakawa
- Tinubu zai naɗa ɗan shekara 40 a matsayin Shugaban JAMB
Shugaba Tinubu ya bayana hakan ne a birnin Legas lokacin taron ƙaddamar da littafi da kuma miƙa lambobin yabo ga masu fafutuka da abokan hulɗarsu, wanda ƙungiyar tabbatar da miƙa mulki ga farar hula ta ƙasa NADECO ta shirya ta hannun Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Ayo Opadokun.
Shugaban, wanda tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba ya wakilta, ya ce wasu marasa kishin ƙasa da ke adawa da kyawawan manufofinsa da shirye-shiryensa ne ke haddasa ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.
Yayin da yake yaba wa ƙungiyar NADECO saboda fafutukar da take yi, da ba zai taɓa zama shugaban ƙasar nan ba idan ba a dawo da tsarin dimokuraɗiyya ba.
Osoba, wanda ya isar da saƙon shugaban ga mahalarta taron a cibiyar Muson da ke Onikan a Legas, ya ce za a magance manyan ƙalubalen siyasar da ke fuskantar ƙasar a wa’adin mulki na biyu na shugaban.
Ya ce: “Shugaban ya buƙace ni da in shaida muku cewa zai aiwatar da manufofin siyasa a wa’adinsa na biyu. A halin yanzu yana maida hankali ne kan batutuwan tattalin arziki da tsaro.
“Akwai gangancin da wasu mutane ke yi na ganin sun dagula zaman lafiyar ƙasar nan, musamman waɗanda ke jin haushin manufofinsa na janye tallafin man fetur da kuma kawo ƙarshen harƙallar canjin kuɗi.”
Osoba, wanda ya tuna yadda ya kusan rasa ransa ta hanyar yunƙurin kisa da aka yi masa lokacin gwagwarmayar, ya bayyana cewa ba a kafa NADECO a gidan marigayi Manjo Janar Adeyinka Adebayo da ke Ikeja don batun zaɓen 12 ga watan Yuni ba, a’a, an kafa ta ne domin fafutukar dawo da dimokuraɗiyya.
Ya jaddada cewa: “Ba mu kafa NADECO saboda zaɓen Yuni 12 ba, mun kafa ta ne don fafutukar ganin an dawo da dimokuraɗiyya. Lokacin da Abiola ya fara tasa gwagwarmayar ne aka kawo shi cikin ƙungiyar NADECO.”