Abin dariya ne cewa Najeriya ce ta fi karfin arziki a Afirka – Kwankwaso

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na jihar Kano ya bayyana sakamakon da aka fitar game da karfin arzikin Najeriya wanda aka fi sani da Gross Domestic Product (GDP) inda aka nuna cewa Najeriya ce kasar da ta fi kowace karfin arziki a nahiyar Afrika da cewa yaudara ce da kuma shaci fadi.  Ya bayyana haka ne […]

Abin dariya ne cewa Najeriya ce ta fi karfin arziki a Afirka – Kwankwaso

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na jihar Kano ya bayyana sakamakon da aka fitar game da karfin arzikin Najeriya wanda aka fi sani da Gross Domestic Product (GDP) inda aka nuna cewa Najeriya ce kasar da ta fi kowace karfin arziki a nahiyar Afrika da cewa yaudara ce da kuma shaci fadi.
 Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar Shugabannin Jam’iyyar ADC (African Democratic Congress) a gidan gwamnati a ranar Talatar da ta gabata.
Gwamna Kwankwaso ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kula tare da mayar da hankali ga abin da yake faruwa a zahiri fiye da abubuwa na shaci fadi. “Tatatlin arzikin da suke tinkaho yana habaka tattalin arzikin Abuja ne. Duk wani masanin tattalin arziki ya san cewa lissafin da aka bayar bai yi daidai da abin da yake faruwa a zahiri ba. Ka tafi  kan titunanmu ka ga yadda mutane ke yawo cikin yunwa da talauci . Babu wuta, ba ruwa, ba tsaro, ga talauci duk ya baibaye jama’a. Ba za ka iya cewa komai game da tatalin arziki ba a kasar da ake kashe-kashe, kasar da mutanen cikinta ke barci da ido daya. Babu yadda za a ce kasar da babu zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikinta ce ta fi kowace kasa karfin arziki a Afrika.”  Inji Kwankwaso.
Gwamna Kwankwaso ya kara da cewa,”Idan ka je ka samu mutane a kan titi ka gaya musu cewa karfin arzikin kasar nan yana bunkasa dariya za su yi maka, idan ka yi sa’a ba ka sha dukan tsiya ba.”
  Har ila yau Gwamnan ya bayyana cewa, mutanen  kasar nan a ko’ina suke a bangarorin kasar nan suna cike da fushi game da yadda abubuwa suke tafiyar hawainiya a kasar nan, sakamakon abin da ya kira,” handama da babakere na wadansu ‘yan tsirarun mutane a kasar nan wadanda ba su son ganin talaka ya ji dadi.”
Gwamnan sai ya yi kira ga jam’iyyar ADC da ta hada kai da jam’iyyarsa ta APC wajen fidda jaki daga duma, ta hanyar yakar irin wannan rashin adalcin a shekarar 2015, a cewarsa, kamata ya yi jam’iyyun biyu su yi kokarin ciyar da kasar nan gaba.
Tunda farko kakakin Jam’iyyar Alhaji Manu Ibrahim Ahmed ya bayyana cewa sun kai wanann ziyara ne don karfaf zumunci a tsakanin jamiyyarsu da gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Kwankwaso, wanda manufofin gwamnatinsa suka yi daidai da na jam’iyyarsu wajen ayyukan ci gaban kasa.