Abin da ya sa na binne jikana da rai
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta kama wani tsoho dan shekara 50, bisa zagin binne jikansa da rai. Mai magana da yawunta, DSP Ahmed Wakil, ya ce mutumin ya aikata laifin ne bayan diyarsa mai shekara 17 ta haifi jaririn sakamakon fyaden da wani ya yi mata cikin watan Janairu, 2020. Tarihi da rayuwar […]
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta kama wani tsoho dan shekara 50, bisa zagin binne jikansa da rai.
Mai magana da yawunta, DSP Ahmed Wakil, ya ce mutumin ya aikata laifin ne bayan diyarsa mai shekara 17 ta haifi jaririn sakamakon fyaden da wani ya yi mata cikin watan Janairu, 2020.
- Tarihi da rayuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris (1937-2020)
- An kama uwar riko tana azabtar da karamin yaro
“Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta kawo yarinya ’yar shekara 17 ofishin ’yan sanda na Toro, bayan ta haifi jariri a ranar 14 ga watan Satumba, a Rimin Zayam na Karamar Hukumar Toro, Jihar Bauchi.
“Suka ce mahaifinta, Bawada Audu, ya kwace jaririn ya binne shi a bayan gidansu”, kamar yadda ya ce.
Jami’in ya ce daga nan jami’an rundunar suka dunguma tare da kungiyar zuwa gidan mutumin aka tono jaririn aka kai shi asibiti inda likitoci suka tabbatar ya mutu.
A bayanin mahaifin yarinyar, ya shaida wa ’yan sanda cewa wani mutum ne ya yi wa yarinyar fyade ya gudu, kafin daga baya ciki ya bayyana.
“An ba mai garin Rimin Ziyam gawar jaririn domin a binne ta kuma mahaifin yarinyar ya amsa laifinsa”, inji jami’in tsaron.