Abin fata daga sabuwar gwamnati: Magance matsalar tsaro

Gwamnatin Muhammadu Buhari da za ta fara aiki a yau ta gaji dimbin matsalolin da suka shafi rayuwa da tattalin arziki ga rashin kayan inganta rayuwa, amma babbar matsalar da ta fi bukatar daukin gaggawa a tsakanin matsalolin ita ce ta rashin zaman lafiya a Arewa maso Gabas. Hare-haren Boko Haram da suka barke a […]

Abin fata daga sabuwar gwamnati: Magance matsalar tsaro
Abin fata daga sabuwar gwamnati: Magance matsalar tsaro

Gwamnatin Muhammadu Buhari da za ta fara aiki a yau ta gaji dimbin matsalolin da suka shafi rayuwa da tattalin arziki ga rashin kayan inganta rayuwa, amma babbar matsalar da ta fi bukatar daukin gaggawa a tsakanin matsalolin ita ce ta rashin zaman lafiya a Arewa maso Gabas.

Hare-haren Boko Haram da suka barke a kasar nan a shekarar 2009 sun shafe duk matsalolin tsaro da kasar nan ta fuskanta a shekarun da suka gabata bayan Yakin Basasa.
Sai dai hare-haren soji da ke gudana a Arewa maso Gabas tun watan Maris da hadin gwiwar kasashen Chadi da Kamaru da Nijar sun yi matukar raunana karfin mayakan tare da kwato galibin garuruwan da suka koma karkashinsu. Yakin da ke gudana a dajin Sambisa a yanzu na dada karya karfin yakin maharan. Sai dai hare-haren bam na bayan nan a Jihar Yobe da hare-haren da Boko Haram ta kai a Maiduguri da wasu garuruwa na nuna ba a cimma nasarar kawar da su ba. Kuma mashayin jinin shugabansu Shekau, har yanzu bai shiga hannu ba, kuma fiye da daliban makarantar Chibok 200 har yanzu ba a ceto su ba duk da cewa sojoji sun ceto daruruwan mata da yara daga sansanonin Boko Haram.
Wajibi ne kawar da Boko Haram baki daya ya zama babban abin da gwamnatin Buhari za ta mayar da hankali a kai. Sabon Shugaban kasar ya fadi a wata tattaunawa da editocin Media Trust a Daura kwanan nan, cewa magance matsalar tsaro zai kasance abu na farko da gwamnatinsa za ta ba muhimmanci. Akwai batutuwa biyu da suke da alaka da wannan batu. Na daya tsoma sojojin kasashen waje wanda ya taimaka sosai wajen takura wa Boko Haram tare da toshe hanyoyin kai musu kayayyaki tare da samun galaba a kansu. Sai tsoma “mashawarta da kwararru’ na kasashen waje. A bayan nan Buhari ya koka da tsoma kashi na biyu a yakin, amma muna kira gare shi kada ya yi gaggawar daukar mataki, ya tsaya ya nazarci lamarin idan ya karbi ragamar mulki. Yana da matukar muhimmanci a ci gaba da dorawa kan nasarar baya-bayan nan da sojojin suka samu wadda ta ceto dubban rayuka a yankin da wajensa.
Akwai miliyoyin mutanen da maharan suka raba da muhallinsu da suke neman a tsugunar da su tare da sake gina musu garuruwansu. Wannan na da matukar muhimmanci kafin shuka wani sabon rikici wajen yin haka. Gwamnatin Buhari ta sanya batun sake tsugunar da su cikin manyan abubuwan da za ta ba fiffiko, tana iya bukatar tallafin kasashen duniya wajen sake gina gidaje da makarantu da asibitoci da wuraren samun abincinsu da aka ruguza.
Bayan an ci nasarar kawar da Boko Haram, Buhari ya bullo da wani shiri na kasa na gyaran halaye don tabbatar da an dakile guluwi a cikin harkokin addini. Kuma a yi kokarin kawar da barace-baracen kananan yara a kan tituna. Buhari ya tsara wani shiri na dogon lokaci don dawo da karfi da martabar rundunar sojin kasar nan da sauran hukumomin tsaro ta yadda za su iya murkushe duk wata kungiyar tayar da kayar baya idan ta kunno kai a kasar nan.
Kwanan nan mashawarcin Shugaban kasa mai barin gado kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki ya yi gargadin cewa ta’addanci a yankin Neja-Delta na iya sake farfadowa. Don haka wajibi ne Buhari ya yi aiki wurjanjan cikin hikima don kauce wa hakan. Wasu daga cikin tsofaffin ’yan ta’addan yankin a kwanaki sun bukaci a ci gaba da shirin afuwar da aka yi musu da kuma ci gaba da Hukumar Raya Yankin Neja-Delta da Ma’aikatar Neja-Delta. Bukatun ba wadanda ba za a iya biya musu ba ne. Abin da ba za mu bada shawara ba, shi ne a ci gaba da bayar da hanci biliyoyin Naira ga tsofaffin ’yan ta’addan ta hanyar kwangilar bogi kamar yadda ake yi a shekarun nan.
Fada a tsakanin manoma da makiyaya ma ya zama wani yaki a Jihar Benuwai a bara. Sannan a wasu jihohi kamar Zamfara da Kaduna da Filato da Nasarawa satar shanu ta zama matsalar da galibi take jawo kai hare-haren ramuwar gayya a kauyuka da garuruwa inda ake rasa rayuka.
Wajibi ne Buhari ya bullo da tsari na dogon lokaci don hana aukuwar wannan matsala da karuwar jama’a da karancin filaye ke haifarwa. Yayin da fashi da makami a kan manyan tituna hanyoyi ke raguwa a shekarun nan, sakamakon ingantar sintirin ’yan sanda da kayan sadarwa da samar musu makamai, wani abu da ya mafi muni da ya bayyana shi ne satar mutane. Matasa a sassan kasar nan yanzu sun dauki satar mutane a matsayin hanya mafi sauki ta kudancewa a dare daya. A karkashin Buhari ya wajaba a sanya ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro ta yadda za a magance satar mutane don samun kudi. Wata matsala mai alaka da wadannan ita ce ta yaduwar kananan makamai (bindigogi) da suke taimakawa wajen gudanar da wadancan miyagun ayyuka. Kuma karuwar manyan laifuffuka a al’ummarmu na da alaka da halin da tattalin arziki ke ciki. Kuma na iya ta’azzara idan Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi ba su biyan albashi. Duk da cewa Buhari zai bukaci lokaci kafin ya tafiyar da tattalin arziki yadda ya kamata, wajibi ne ya magance rashin tsaro cikin gaggawa in ba haka ba, za a dauki lokaci tattalin arzikin bai farfado ba.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna