Abin haushi ba ya karewa a Sakkwato!
A ranar Talata 25/06/2019 da misalin karfe 2:00 na rana na yi kacibis da wani mummunan labari daga bbchausa.com mai taken: ’Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Sakkwato. Kuma suka kara da cewa wannan lamarin ya faru ne tun ranar Litinin 24/06/2019 a cikin dare a kauyen Malafaru da ke Karamar Hukumar Goronyo.Wannan lamarin […]
A ranar Talata 25/06/2019 da misalin karfe 2:00 na rana na yi kacibis da wani mummunan labari daga bbchausa.com mai taken: ’Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Sakkwato. Kuma suka kara da cewa wannan lamarin ya faru ne tun ranar Litinin 24/06/2019 a cikin dare a kauyen Malafaru da ke Karamar Hukumar Goronyo.Wannan lamarin ya razana ni sosai, ya kada hankulan masu kallo, sannan ya girgiza al’ummar Jihar Sakkwato. Ina zaune tare da wadansu abokanina muna jimamin faruwar lamari, sai muka ji ana hayaniya a waje, mutane suna ta cewa ga gawawwakin nan an kawo. Ko da na fito sai na ga mutanen a cikin motoci da yawansu suna rike da bindigogi harba ruga da gani sun galabaita kuma suna neman taimako. Da suka iso Fadar Sarkin Musulmi sai suka nemi ganinsa domin su gwada masa abin da ya faru da su tun a daren jiya, sannan su gaya masa cewa har lokacin da suka taso ba wani jami’in tsaro da aka tura musu domin ya duba bala’in da ya faru da su.
Wadannan mutane sun yi wa wadansu jama’ar gari bayanin cewa sun zo da gawarwakin ’yan uwansu Sakkwato ne don duniya ta ga abin da ya faru da su kuma gwamnati ba ta dauki matakin tura ko da ’yan jarida ba domin su dauko abin da ya faru su yada wa duniya. Mutanen sun kwashe akalla awa daya a kofar fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi ba tare da samun nasarar ganinsa, saboda ba ya gari. Amma fa abin da ganau suke fada, ‘Ba su ga fitowar ko da dogari ba daga gidan da niyyar yin magana da su.’ Bayan sun gaji da jiran gawon shanu sai suka yanke shawarar isa Gidan Gwamna ko za su samu damar ganawa da shi. Kuma su nuna masa gawarwakin ’yan uwansu da aka kashe ko zai dauki matakin kare faruwar haka a gaba.Wannan shi ne iyakacin abin da nake da hakikani a kai game da shigowar mutanen garin kauyen Malafaru da ke Karamar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato.
Tambayoyina ga al’ummar Jihar Sakkwato
- Shin mutanen nan sun samu isa Gidan Gwamnatin Jihar Sakkwato?
- In sun samu isa, me ya faru a can?
- Shin sun samu ganin Gwamna Aminu Tambuwal ko wani babban mukarrabinsa?
- In ba su gan shi ba me ya sa?
- Shin wane mataki gwamnati ke shirin dauka game da wannan lamari?
- Ko akwai wani tallafi da gwamnati ke da kudirin badawa ga iyalan mamatan?
- Shin ina ’yan siyasar Karamar Hukumar Goronyo? Ban ga ko dayansu a cikin ayarin ba. Ko suna nufin ba su da labarin lamarin ne?
- Ina ’yan boko da ’yan kasuwa da malaman addini da sarakunan yankin Goronyo?
- Me ya sa ba mu ganku kun zo rakiyar iyalan wadannan mutane zuwa Sakkwato ba?
- Ko don ba Gwamna yana rabon kaso ko mukaman gwamnati ba ne?
- Ko mamatan ba su da gata ne a gare ku?
Har zuwa lokacin da nake wannan rubutun (misalin karfe 10:50 na daren Talata), ban ga wannan labarin a shafukan facebook na masu yi wa gwamnati shelar ayukkanta ba, kamar su: Aisha Maina, Nuradden Harande Mahe, Hon. Shamsu Buhari Madunka, Kwamared Hussaini Muhammed, Shamsudeen Umar Mai Akwai, Bilya Yariman Barebari, Abdulkadeer Yari (AK Yari), Buhari Maigwandu, Uncle Anas Dakura, Sirajo Abdullahi (Swallow), Abubakar Abdullahi Jikan Liman, Mudassir Buhari Binanchi da sauransu.
Shin ba ku ne na ga kuna yada labarai da hotunan rashe – rashen da ake yi a masu gidajenku ba, har kuna manna hotunan sallolin gawarwaki da hotunan masu zuwa yi wa iyayen gidajenku gaisuwa ba? Amma yau ga shi wannan lamarin ya faru a Sakkwato a daren Litinin amma har zuwa Alhamis 27/06/2019 da misalin karfe 11:30 na dare ba ko mutum daya daga cikinku da ya tura yi wannan labari a shafinsa. Amma na ga kuna taya sababbin kwamishinonin Jihar Sakkwato murna. Shin ko kuna nufin labaran bukukuwa da kuke kawowa a halin yanzu da hotunan ’yan siyasar da kuke talla don mutane su gani sun fi muhimmanci bisa ga labarin wannan bala’i? Sanin kowa ne da wadannan bayin Allah da aka kashe suna da alaka da wadansu ’yan siyasa ko attajirai da tuni duniyar Intanet ta kosa da tofin Allah tsine da za ku rika yadawa. Akwai da yawa cikin marubuta a kafafen sada zumunta wadanda na san ba ’yan koren siyasa ba ne kuma na yi tunanin ganin wannan labarin a shafukansu, amma su kansu har lokacin da na ambata a sama sabon labarin da suke dauke da shi shi ne labarin daliban Sakkwato masu karatu a kasar waje. Haba jama’a! Shin ko don wadannan bayin Allah da aka kashe ba su yi karatun zamani ba ne ya sa kuka mance ku yi rubutu a kansu, domin ku janyo hankalin gwamnati game da wannan lamari?.
Ina kungiyoyin fararen hula masu rajin kare hakkin dan Adam kamar:
- Kungiyar Muryar Talaka ta Jihar Sakkwato? Ku kanku ban ga kun buga wannan labarin ba?
- Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam.
iii. Sauran kungiyoyi masu ikirarin kishin Jihar Sakkwato kamar su: ‘Patriotic Youth Forum Sakkwato,
- ib. SPYFO, Hausa Fulani Initiatibe, Sakkwato,
- b. Kungiyar kiran kafafen yada labarai da sauransu.
Shin ko kuna nufin wadannan bayin Allah da aka kashe ba a keta hakkinsu ba? Shin ko don wadannan mutanen da aka kashe talakawa ne?,
A karshe, ina fata duk wanda ya karanta wannan rubutun ya yi nazari a kansa, ya dube shi da idon basira, ya yada shi in yana da hali domin sauran mutane su gani ko gwamntin za ta dauki mataki. Allah Ya sa mu dace.
Muhammad Buhari Abubakar
imel:[email protected]