Abin kunya (Blacky)
Wani saurayi ne Bazazzagi yake neman wata yarinya, sai rannan babanta ya ce mata ta gaya masa yana son ganin sa. Yamma na yi saurayi ya shirya tsaf, shi da abokinsa suka tafi. Ashe saurayin nan wake ya ci da rana. Suna isa bayan sun gaishe da iyayen yarinyar, sai maigidan ya ce: “Ai sai […]
Wani saurayi ne Bazazzagi yake neman wata yarinya, sai rannan babanta ya ce mata ta gaya masa yana son ganin sa. Yamma na yi saurayi ya shirya tsaf, shi da abokinsa suka tafi. Ashe saurayin nan wake ya ci da rana. Suna isa bayan sun gaishe da iyayen yarinyar, sai maigidan ya ce: “Ai sai mu ci abinci kafin mu tattauna ko?” (Da ma kuwa maigidan dan boko ne).
Saurayin nan da abokinsa da sauran ’yan gida aka hau teburin abinci, karen masu gida da suke kira ‘Blacky’ ya zo daf da kafar saurayin ya kwanta. Bayan an ba kowa abinci, sai cikin saurayin ya murda, kululululu! Saurayin ya matsu iya matsuwa, sai ya fakaici idon kowa
ya saki wata ’yar tusa ‘fut.’ Baban yarinya ya kalli karen nan yace, “Blacky!” Sai saurayin ya yi dan murmushi, a zuciyarsa yana cewa, ‘ba su gane ni ne na yi tusar ba. Sai ya kara sakin wadda ta dan fi waccan kara,’burrr.’ Maigidan ya ce, “Kai, haba Blacky!!” Saurayin ba sai ya saki jikinsa ba, ya sake sakin wata iyaka karfinsa, ji kake,’burutututu…!’ Wannan karon sai maigidan ya daka wa karen tsawa, ya ce: “Kai Blacky, ba za ka tashi ba sai ya kashe ka da wannan gubar?”
Daga nan saurayin ya yi tsuru-tsuru, yanzu ya gane ashe an gano shi tun farko.
Daga Shehu Mustapha Chaji