Abin lura ga masu jefa kuri’a
Daga danjuma Katsina Wani Aboki na, wanda ya yi shekaru 14 yana aikin soja kwatsam ya ajiye ba shiri, ya kuma fice daga gidan da yake na soja tun kafin a maido masa da amsar takardarsa ta ajiye aiki. Ya shaida mana cewa, abin da ya sa ya ajiye aikin, shi ne, wata rana yana […]
Daga danjuma Katsina
Wani Aboki na, wanda ya yi shekaru 14 yana aikin soja kwatsam ya ajiye ba shiri, ya kuma fice daga gidan da yake na soja tun kafin a maido masa da amsar takardarsa ta ajiye aiki. Ya shaida mana cewa, abin da ya sa ya ajiye aikin, shi ne, wata rana yana zaune aka zo da jadawalin wadanda za a tura fagen daga a fadan da ake yi a yankin Maiduguri da Yobe. Duk sojan da aka dauka sun san fada, sun kuma halarci yaki a wasu kasashe karkashin Majalisar dinkin Duniya da kuma Tarayyar Afrika (AU). Don haka ko lokacin da aka ce za a tura su da zumudi da karfin gwiwa suka tafi.
‘Ni’ inji sojan na ji haushin da ba ni a ciki. Domin don kishi na shiga aikin, ba domin albashi ba. Kwatsam wadannan abokan nawa sai suka rika aiko mana da sakon waya, cewa, sun rasa gano hakikanin matsalar d ake tattare da wannan yaki. Ya rika kawo man wasu tsare-tsare da kalmomin soja, wadanda ni ban sansu ba. A takaice dai zan ce kawai sun je aiki, amma akwai matsala.
Mai ba ni labara, ya ce wadannan jaruman wasu gawarwaki ne aka kawo, wasu kuma har zuwa lokacin rubuta labarin nan suna amsar magani a asibiti. Abin takaici asibitin ma maganin wani lokaci sai an yarfe gumi.
Sojan ya ci gaba da cewa, daga cikin sojan wadanda aka kashe, akwai wanda na fi kusa da shi. Mutum ne mai son addini, kuma mai kula da iyalinsa. Iyalinsa abin misali ne a duk barikin wajen tarbiyya da tsafta da kwanciyar hankali.
Wani abin takaici da na ji, matar nan ta marigayi tana bin maza don ta iya rike gidan. Don babu abin da hukumar soja ta yi musu. Wata rana na dawo sai na ga daya daga cikin ’ya’yan marigayin wanda lokacin da marigayin na da rai abin sha’awa ne, ga kowa, amma ya yi baki kudaje na bin hancinsa da bakinsa. Yana gani na ya rugo wajena.ya ce don Allah in biyo ka mu ci abinci? Na hau sama a dakina da shi, na sanya aka yi masa wanka, aka canza
masa kaya, aka kuma ba shi ya ci, ya koshi.
Sai tunani ya fara shiga ta, a cewar sojan nan, ‘shin sojojin kasar nan ragwaye ne? Amsa ‘a’a, su ne suka karfi a Yammacin Afirka, don suna daga cikin wadanda suka taka rawar samar da zaman lafiyar duniya. Kullum suna akan manyan tituna don kare rayukan al’umma .
Duk martabar da wadannnan soja suke da ita an ja ta kasa an walakan tata. An maida rayuwarsu kamar ta kiyashi, an watsar da kwarjininsu; an wofintar da izzarsu. Mai ba ni labari ya ce ban san lokacin da idona ya cika da kwalla ba.
Na kalli yadda yaron da aka kashe mahaifinsa rayuwarsa ta koma. Ban san lokacin da na dauko biro da takarda na rubuta takardar aje aikina da niyyar zan dawo duk ranar da martabar soja ta dawo.
Ga wanda zai jefa kuri’a yana da kyau ya dauko hoton yadda sojojinmu suka koma a yanzu. Sannan ya jefa, inda zai tambayi kansa ko a haka za a cigaba?
Wasu gungun jami’an tsaro da aka yi wa kisan gilla a Jihar Nasarwa a hanyarsu ta zuwa kamo wani da ake zargi kwanton bauna aka yi musu, aka yi musu kisan wulakanci, inda rahotani, suka nuna adduna da barandami aka yi ta sassabarsu, har suka mutu kamar yadda ake sassaben ita ce, har yanzu ba wanda aka kama. Ba wanda aka kai kotu bisa tuhuma. Iyalansu sun zama gwagware ’ya’yansu sun zama marayu. Alkawuran da aka yi wa iyalansu har yanzu suna ta jeka- ka dawo ba labari. Hakkin mazajen su kullum sai ba suke. Ana ku dawo gobe. Idan za ka jefa kuri’arka ka tuna da wannan. Da a irin haka wa zai sadaukar da ransa ga kasarsa?
Ka tuna da yadda wajen tsare motocinmu domin bincike suka zama asusu; ada idan za a amshi wani abu a boye ake yi, yanzu kuwa kai tsaye ake yi. Kusan kowace karamar hukuma sai ’yan sanda sun fito don samun na sawa bakin salati. Ka tuna wannan in za ka jefa kuri‘arka. Yayin da jami’an tsaron kasar Martabarsu ke tsiyayaya kamar indararo. Sai su kuma ‘jami’an tsaron’ suke ganin ya kamata su bi da daukar matakai don rike ‘’darajarsu’’?
Don haka sai suka ga kawai dole su bude ma fararen hula ido su nuna masu cewa lallai fa sune ke da iznin rike makami suke da ikon kamawa da daurewa. Dama kashewa suce wani dalili ya kawo mutuwar.
Da wannan duguzum din rayuka da yawa sun salwanta wanda yawansu ya nunnunka na jami’an tsaron da aka kashe a wajen cika ayyukansu. Ya yan[wadanda jami’an tsaro suka kashe] sun zama marayu ba kudin inshora ko na ajiye aiki. Matansu sun zama gwagware.
Idan zaka jefa kuri’a, ka tuna yadda kasar ta koma babu tsaro da ke da tabbas ko dai mai tsaron kowanda ke tsaron. Ko tsaron koma tsarewar. Idan za ka jefa kuri’arka ka tuna labarin wasu yara guda uku dake karatu a kasashen ketare karatun nan zai amfani kasar su da cigabansu amma aka kama su da cikin fararen kaya ranar jumma a.da su da yan uwansu mutum talatin duk aka bindige yaran ukkun ’ya‘yan mutum daya ne; uwa daya uba, ’ya’yan Shiek Ibrahim El-Zak-zaky da sauran ’yan gidaje daban-daban, wadanda har yanzu babu bincike, ba wanda aka kama.
Idan za ka jefa kuri’arka ka sani shi girgijen zalunci yawo yake yi. Idan ba ka yi maganinsa ba wata rana bisa kanka zai zubar da ruwansa. Idan za ka jefa kuri’arka, ka yi tunani kada a yi maka romon baka ko wani dadin baki. Domin dagulewar al’amuran kasa ne abin lura ga masu jefa kuri’a.
Danjuma Katsina. Danjarida ne, marubucin za a iya tuntubarsa ta [email protected] 08035904408.