Abin lura game da matan aure a makarantu
Assalamu Alaikum. A wannan makon zan yi rubutu ne a kan mata wadanda sukan yi amfani da damarsu ta zuwa makaratun kwana ko jami’a wajen aikata abin da suka so. A hakikanin gaskiya ilimi wani sinadari ne na zaman duniya wanda idan mutum bai da shi, ake ganinsa kamar dabba. Na zauna na yi nazari […]
Assalamu Alaikum. A wannan makon zan yi rubutu ne a kan mata wadanda sukan yi amfani da damarsu ta zuwa makaratun kwana ko jami’a wajen aikata abin da suka so. A hakikanin gaskiya ilimi wani sinadari ne na zaman duniya wanda idan mutum bai da shi, ake ganinsa kamar dabba.
Na zauna na yi nazari a kan yadda mata suke lalata a mkaarantu. Irin wannan lalatan shi ne dalilin da ya kansa iyaye da dama hana yaransun zuwa makarantu. Amma duk da irrin wadannan abubuwa, akwai mata na gari wadanda duk irin abubuwan da yake faruwa ba zai hana a barsu zuwa makaranta ba.
A bayanina akwai matsala guda biyu da nake son tattaunawa a kai, ta farko shi ne matsalar matan aure na biyu kuma shi ne mata marasa aure.
Shi dai a kan yi aure tsakanin namiji da mace, wadda bayan auren akwai abubuwan da mace ya kamata ta daina bayan auren. A hakikanin gaskiya idan mutum ya tsinci kansa a makaranta na karatu ko koyon aiki, zai ga abubuwan al’ajabi a gurin mata. Matan aure sukan kulla alaka da mazaje a makarantu da sunan ’yan aji amma a gaskiya ba haka abin yake ba. Matan aure sukan kulla alaka da kawaye wadanda sukan koya masu halayen banza. Halin farko da sukan tsince kansu a ciki shi ne maganar yin madigo. Duk da yake a wasu kasashen duniya yin hakan ba laifi ba ne. Amma a kasarmu yin hakan laifi ne kari da cewa addinan mu manya guda biyu ba za su yarda da yin hakan ba. Akwai dalilai da dama wadanda ke sa su fada wa irin wanan abubuwan. Na daga ciki akwai dalilin samun abubuwan duniya kamar gida, kudi, harma da mota. Wasu kuma sukan yi hakan ne saboda su nuna kamar sun waye wanda ba haka abin yake ba. Na biyu shi ne bin mazaje a wajen ‘mora rayuwa’ ko ince ‘karuwanci’. Sanannan abu ne karuwanci ba abu ba ne mai kyau ballantana a ce ma ga matar aure. A addinin musulunci idan mace mai aure ta yi zina tofa hukuncinta kisa ne ta hanyar jifa. Kun ga ko wannan ba karamin abu bane. Irin wadannan matan ba ma sa tsayawa karatun a wasu lokutan, domin yau suna Abuja gobe kuma Dubai da sauransu, haka kawai za ka ga suna tafiya yawo. Macen da ba ta da atamfar Naira dubu daya da farko, sai ka ga har gwal take sawa a makaranta. Irin matan za ka ga cewa daga karshe ma raba auren ake yi saboda mazajen su na aure ba za su iya masu abin da suke so ba. Na uku kuma shi ne biye wa dalibai maza irinsu a makaranta. A wannan matsalar za ku ga sukan maida kansu kamar ba mata aure ba. Daga shigarsu ko mu’amalarsu ba za a iya gane wa idan matan aure ce ko kuma ba hakan ba. Wasu matan ma har za ka ga samari suke yi a makaranta, kaga suna ta mu’amala kamar ba matan aure ba. Irin wannan hadakar ba abu ba ne mai kyau da matan aure ya kamata su rika yi.
A karshe ina mai ba matan aure masu daya daga cikin wadannan halin da su ji tsoron Allah su daina. Domin irin wannan abun ya janyo ma wasu matan matsala. Ba ma matan aure ba kawai harda wadanda ba su yi auren ba.
Wannan matsalar ta jawo iyyaye da mazaje sun tsoron barin yaransu mata zuwa karatu matukar za su bar gida. Irin wannan matsalolin ya raba aure da dama kuma ya sa iyaye sun rasa iko da yaransu sannan ya sanya iyaye jin kunya a kan abubuwan da yaransu suke yi. Da fata za mu gyara halayenmu wadanda ba masu kyau ba. Kuma za mu tuna cewa duk abin da muka yi yaranmu suna kallo kuma za su so kwaikwayon abin da muke yi. Allah muke roko da Ya shiryar da mu.
Aliyu Khalid, Kaduna 08038597907