Abin misali daga rayuwar Sa’adu bin Abu Wakkas (2)
’Ya’ya da shekarun Sa’adu: Sa’adu, Allah Ya kara masa yarda a farkon rayuwarsa ba ya da ’ya’ya masu yawa, ’yarsa daya ce mace, kamar yadda ya bayyana wa Annabi (SAW) yayin da ya je gaishe shi cikin wata jinya da ya yi. Abu Is’hak Sa’adu bin Abu Wakkas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya […]
’Ya’ya da shekarun Sa’adu:
Sa’adu, Allah Ya kara masa yarda a farkon rayuwarsa ba ya da ’ya’ya masu yawa, ’yarsa daya ce mace, kamar yadda ya bayyana wa Annabi (SAW) yayin da ya je gaishe shi cikin wata jinya da ya yi. Abu Is’hak Sa’adu bin Abu Wakkas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya zo duba ni a shekarar Hajjin Ban-Kwana saboda wata jinya da na yi fama da ita. Sai na ce: “Ya Manzon Allah! Ka ga dai ga irin halin da nake ciki na tsananin ciwo, ni mai dukiya ce amma ba ni da magaji da namiji sai ’yata (mace). Shin ya halatta in yi sadaka da kashi biyu daga cikin uku na dukiyata?” Sai (Annabi SAW) ya ce: “A’a.” Sai na ce: “To rabi fa ya Rasulullahi? Ya ce: “a’a” Sai na ce “To sulusi fa (daya bisa uku)” Sai ya ce: “Sulusi? Sulusi ya yi yawa. Ai ka bar ’ya’yanka cikin wadata shi ya fi kyau da ka bar su cikin talauci su rika neman sadaka a wurin mutane. Kuma lallai duk abin da ka ciyar don neman yardar Allah za a saka maka a kai, hatta abin da za ka ba matarka.” Sai na ce: “Ya Rasulullahi za a bar ni a Makka bayan kun koma Madina kai da sahabbanka?” Sai ya ce: “Lallai ko an bar ka (a Makka) sannan ka aikata wani aiki domin Allah, Allah zai kara maka daraja da daukaka, saboda wannan aikin. Kuma ina fatan za ka rayu, domin rayuwarka ta amfani wadansu kuma ta cutar da wadansu.” Sannan ya yi addu’a da cewa: “Ya Ubangiji! Ka sa hijirar sahabbaina ta zama tsarkakkiya kada Ka mayar da su bisa duga-dugansu.” Buhari da Muslim suka ruwaito shi.
Daga baya Allah Ya azurta Sa’adu (RA) da ’ya’ya maza goma sha bakwai (17), har Sa’adu (RA) ya roki Allah Ya tsawaita rayuwarsa har ’ya’yansa su girma. Kuma ya rayu shekara 20 bayan haka, ya rasu a shekara ta 54 Bayan Hijira, kuma shi ne mutum na karshe da Allah Ya yi wa rasuwa a cikin Muhajirai (mutanen Makka) da suka yi hijira zuwa Madina tare da Annabi (SAW).
Sa’adu bin Abu Wakkas (RA) ya ruwaito Hadisai masu yawa da suka kai 271, wannan ya sa ake kirga shi a cikin shahararun maruwaita Hadisi. Haka ’ya’yansa sun ruwaito Hadisi daga gare shi da kuma Uwar Muminai A’isha (RA) da Abdullahi Ibn Abbas da Sa’id bin Musayyib da Al-Ahanaf bin kais (Allah Ya yarda da su) da sauransu, kuma ruwaya daga gare shi tabbatacciya ce.
Wata rana Abdullahi dan Umar (RA) ya ji ruwaya daga Sa’adu cewa Annabi (SAW) yakan shafa ruwa a kan tufafinsa a lokacin alwala. Sai Abdullahi (RA) ya tambayi mahaifinsa Umar bin Khaddabi (RA) cewa ko wannan ruwaya ce ingantacciya? Sai Umar (RA) ya ce da Abdullahi in dai daga Sa’adu ka ji, to dole ka yi amanna da ita, kada ka yi wata shakka. Wannan na gwada kimar Sa’adu a wurin manyan sahabbai.
Sa’adu (RA) mutum ne mai tsoron Allah, kuma yakan yi ta kuka saboda tsoron Allah. Akan ga idanuwansa cike da hawaye duk lokacin da yake sauraron Manzon Allah (SAW) saboda tsananin tsoron Allah. Wannan dabi’a ta Sa’adu (RA) ta dace da Hadisin da Abu Huraira (RA) ya ruwaito inda ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi kuka saboda tsoron Allah, ba zai shiga wuta ba, sai dai idan nono zai iya komawa cikin hantsa, kuma kurar da aka tayar (a fagen yaki) saboda daukaka kalmar Allah ba za ta taba haduwa da hayakin Jahannama ba.” Tirmizi ya ruwaito. Haka nan Abdullahi dan Amru bin Al-As (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya taba cewa: “Duk wanda ya fara shigowa ta wannan kofa dan Aljanna ne. Sai Sa’adu ya shigo ta kofar.”
Sa’adu yana daga cikin mutane goma da aka yi wa bushara da Aljanna tun suna duniya, yana cikin wadanda suka fara karbar Musulunci (Sabikunal awwaluna). Sa’adu ya halarci Yakin Badar da Uhudu kuma ya je Hudaibiyya, yana daga cikin mutum shida da Amirul Muminina Umar bin Khaddabi (RA) ya nada a kwamiti ko Majalisar Shura domin yanke shawarwari kuma su iya zaben Khalifa a cikinsu a bayansa. Kamar yadda ya gabata shi ne wanda ya fara zubar da jinin kafiri domin kare addini. Sa’adu shi ya fara harbi da kibiya yana tare da Manzon Allah (SAW) domin kare addini. (Bazzar da dabarani suka ruwaito). Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Ka amshi addu’ar Sa’adu idan ya roke Ka.” (Ibn Hibban ya ruwaito). Sa’adu bin Abu Wakkas (RA) ya ce, akwai wata aya a cikin Alkur’ani ta sauka ne saboda mu shida, wato ayar nan da ke cikin Suratul An’am da Allah Madaukaki Yake cewa: “Kuma kada ko kori wadanda suke kiran Ubangijinsu safe da maraice, suna nufin yardarSa, babu wani abu daga hisabinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisabinka a kansu, har ka kore su, ka kasance daga azzulumai.” (An’am aya ta 52)” Muslim ne ya ruwaito.
Wata rana Sa’adu (RA) ya shiga masallaci a lokacin Manzon Allah (SAW), kuma ya tarar a cikin masallacin akwai Salmanul Farisi da Bilal bin Rabah da Shuhaibir Rumi, lokacin da ya fara Sallah sai ya ji wani yana maganganu yana cewa ga baki sun gauraya da Larabawa, sai ka ce ’ya’yan kabilun Ausu da Khazraj. Wannan magana ta bata ran Sa’adu domin haka ya yi sauri kammala sallarsa. Yana kammalawa ya yi wa mutumin nan tsawa yana cewa yaya za ka yi irin wannan magana ga sahabban Manzon Allah (SAW) bayan Musulunci ya daidaita mutane?
Don haka ya yi barazanar zai fille kan wannan mutum, sannan ya ja wannan mutum zuwa gaban Manzon Allah (SAW). Wannan magana ta bata ran Manzon Allah (SAW) har ya tara al’ummar Musulmi ya yi musu huduba ya ja hankalinsu da cewa: “Ya ku mutane! Lallai Allah daya ne, addinimu daya ne, kuma mahaifinmu daya ne (wato Annabi Adam AS). Wanda duk ya shiga Aljanna to kyawawan ayyukansa ne suka shigar da shi amma ba domin zuriyar da ya fito ba. Wanda kuwa munanan ayyukansa suka hana shi shiga Aljanna, to kabila da zuriyarsa ba za su sanya shi a Aljanna ba.”
Manzon Allah (SAW) ya taba cewa, Sa’adu shi kadai yana daidai da mayaka dubu. Kuma an ruwaito cewa a wasu filayen yaki Sa’adu da dalha (RA) su ne suka bai wa Manzon Allah (SAW) kariya, kuma Sa’adu har ya taba ganin Mala’ika Jibrilu da Mala’ika Mika’ilu (AS) a filin yaki. Akwai wata rana Manzon Allah (SAW) yana zaune a wani wuri can nesa, tamkar yana karbar wahayi. Bayan wani lokaci sai ya juyo zuwa ga sahabbansa sannan ya ce musu:
“Wanda duk ya fara isowa nana yana daga cikin ’yan Aljanna.”
Nan take sahabbai suka zuba ido su ga wane ne zai fara isowa, can sai ga Sa’adu bin Abu Wakkas (RA) ya iso wurin. Don haka Abdullahi dan Amru bin Al-As ya tambayi Sa’adu (RA) game da ayyukan da yake yi wadanda suke kusantar da shi ga Allah (SWT). Shi kuma Sa’adu (RA), ya amsa da cewa babu wasu ayyuka na musamman fiye da abin da Musulunci ya tanada, abin da kawai ya sani ba ya kiyayya ko gaba da dan uwansa Musulmi, (wato koda wani ya bata masa rai, to ba ya kwana da shi a zuciya face ya yafe masa).
Za a iya samun Ustaz Aliyu Gamawa ta tarho: 08023893141, 08035829071.