Abin misali daga rayuwar Sa’adu bin Abu Wakkas (6)

Ganimar kadisiyya da Al-Madd’in: Musulmi sun samu ganima mai dimbin yawa a dukan yakukuwan biyu na kadisiyya da Madd’in. Sa’adu kuma ya samu shiga babbar fadar Kisrah Sarkin Farisa har inda gadon mulkinsa yake. Yana shiga sai ya karanta ayar Alkur’anin nan da ke cikin Suratu Dukhan, aya ta 25 zuwa 27 inda Allah Yake […]

Abin misali daga rayuwar Sa’adu bin Abu Wakkas (6)

Ganimar kadisiyya da Al-Madd’in:

Musulmi sun samu ganima mai dimbin yawa a dukan yakukuwan biyu na kadisiyya da Madd’in. Sa’adu kuma ya samu shiga babbar fadar Kisrah Sarkin Farisa har inda gadon mulkinsa yake. Yana shiga sai ya karanta ayar Alkur’anin nan da ke cikin Suratu Dukhan, aya ta 25 zuwa 27 inda Allah Yake cewa:

“Da yawa suka bar gonaki da mare-mari. Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. Da wata ni’ima da suka kasance a cikinta suna masu raha.” (Dukhan: 25-27).

Bayan kammala wannan yaki ne, Sa’adu (RA) ya fahimci cewa lallai Musulmi sun samu dimbin kayan ganima masu alfarma, amma babu wanda ya yi kokarin rike komai a hannu, kowa kokarinsa kawai ya mika abin da ya samu ga shugabansa. Lokacin da Sayyidina Aliyu bin Abu dalib (RA) ya ji wannan labari sai ya ce wannan bai ba shi mamaki ba, domin abin da ake tsammani ke nan daga runduna ta amintattun mutane da shugaban tsayayye. Domin haka Aliyu bin Abu dalib (RA) ya shawarci dukan Musulmi kan su yi koyi da halin wannan runduna. Wannan shi ne karshen gidan Kisrah Sarkin Farisa da ake kira da Farin Gida (Baitul Abyadh ko White House). Kuma da ma a cikin Hadisi Annabi (SAW) ya ce: “Za a samu wadansu daga cikin al’ummata za su yi budi ga gidan Kisrah (Farin Gida): Ahmad da Muslim suka ruwaito.

Sa’adu ya tsara birnin Kufa:

Sa’adu (RA) bai tsaya kawai a matsayin mayaki ba, ya tabbata kwararre a wajen tsara gine-gine. An ruwaito cewa Sa’adu ne da kansa ya zayyana tsarin birnin Kufa saboda irin tsarin da Musulmi suka tarar da Kufa bayan cin birnin da yaki bai dace da zamantakewarsu ba. Don haka ne Sa’adu (RA) ya jagoranci tsara garin da gina shi a kan dacewa da ka’idojin addinin Musulunci. Aka gina masllaci a tsakiyar birnin, sai kuma gidan shugaban a daura da masallacin. Sauran gidajen Musulmi suna kewaye da su. An tanadi tituna masu fadi da filaye isassu don wurin taruwar yara da kuma koyar da dabarun yaki.

An kawo karar Sa’adu:

Wadansu daga mutane Kufa cikin masu batanci ga Sa’adu (RA) sai suka kai kararsa ga Sayyidina Umar bin Khaddabi (RA) a Madina cewa, Sa’adu (RA) ba ya kyautata Sallah gare su. Sa’adu ya bayar da amsa cewa ya Amirul Muminina ina yi musu Sallah ce irin ta Annabi (SAW). Umar (RA) ya ce haka nake (kyautata) zato gare ka. Amma duk da haka Umar ya kafa kwamiti don bincika abin da ake zargin Sa’adu (RA) da shi. Babu wani masallaci da masu bincike suka je suna tambaya game da Sa’adu (RA) face sun fadi alheri game da shi, har suka zo Masallacin Banu Abbas, sai wani mai suna Usmah bin kattada Abu Sa’adatu ya ce za mu ba da shaida don Allah, ai Sa’adu ba ya yi mana adalci a cikin hukunci, ba ya daidaita mu a cikin kaso, sannan ba ya fita yaki.

Sai Sa’adu (RA) ya ce: “Ya Allah! Idan karya yake yi Ka makantar da idanunsa, Ka tsawaita masa rai, Ka jarrabe shi da fitina.”

Abdulmalik ya ce, tabbas na gan shi (wato Abu Sa’adatu) yana lalube don makanta, yana bara don talauci, in an tambaye shi, sai ya ce ni tsoho ne, wanda nake cikin fitina saboda addu’ar Sa’adu. (Domin sai da gashin girar idonsa ya cire saboda tsananin tsufa).” Buhari da Muslim ne suka ruwaito.

Umar ya janye Sa’adu:

Umar bin Khaddabi (RA) yana da wata al’ada  ta hikimar shugabanci, wato kiran shugabannin rundunar Musulmi da suka yi nasara a wajen yaki su koma Madina. Dalilin wannan shi ne domin gudun kada wani shugaba ya dauki wannan nasara a matsayin tasa ko wani kokari nasa har ya kai shi ga girman kai. Don haka sai Umar (RA) ya aike wa Khalid bin Walid da Almusanna bin Haris da Sa’adu bin Abu Wakkas (Allah Ya yarda da su) cewa duk su ajiye aikinsu. Wani dalili na yin haka, shi ne domin gudun kada mutane su rika daukar shugabanninsu na fagen daga a matsayin ababen daukakawa har a wuce gona-da-iri. Umar (RA) ba ya zaton Sa’adu zai fada cikin wannan tarko na Shaidan, amma dai wannan shi ne tsarinsa domin kare al’ummar da yake shugabanta daga fadawa tarkon Shaidan. Kuma saboda girmamawar da Umar (RA) ke yi ga Sa’adu (RA) ne har ya sanya shi a cikin mutum shida da za su iya gadon Khalifancinsa. Umar (RA) ya ce: “Idan kuka zabi Sa’adu, to lallai ya cancanta.” Wannan shi ne kasancewarsa daya daga cikin Ahlus Shura.

Sa’adu ya koma Kufa a zamanin Usman (RA):

A lokacin Khalifancin Usman (RA), Khalifa Usman (RA) ya fahimci cewa Sa’adu bin Abu Wakkas shi ne ya fi dacewa da shugabancin Iraki, domin ya lakanci halayyarsu. Domin haka sai ya nada shi a matsayin Shugaban (Gwamnan) Kufa a kasar Iraki ta yau. Amma a lokacin da rashin fahimtar da ta shiga tsakanin ’yan uwa Musulmi ta yi tsanani a karshen zamanin Khalifancin Usman (RA), sai Sa’adu ya janye jikinsa. Kuma a lokacin da aka kashe Sayyidina Usman (RA), rigima ta kara tsanani a tsakanin magoya bayan Sayyidina Aliyu bin Abu dalib (RA) da Mu’awiyya (Gwamnan Sham), sai Sa’adu ya koma gefe ya ki goyon bayan kowane bangare. Har ma ya rubuta takarda zuwa wurin Sayyadina Aliyu yana ba shi hakuri saboda rashin shiga ayarin magoya bayansa don yaki da Mu’awiyya yana cewa: “Ka ba ni takobin da ian na yi amfani da shi don yakar Musulmi zai fada ga muhallinsa. Idan har zan samu wannan makami to nan take zan shiga fadan!”

Akwai wani dan uwansa mai suna Hashim bin Utbah bin Abu Wakkas wanda ya yi ta neman Sa’adu ya shiga cikin wannan rigima. Ya rika cewa: “Ya Sa’adu! Akwai kimanin mutum 100 da suke goyon bayan ka shiga neman Khalifanci domin cancantarka.” Sai Sa’adu ya amsa da cewa: “Ni ba na bukatar duk abin da zai jawo zubar da jinin Musulmi!”

Nasihohin Sa’adu ga ’ya’yansa:

Sa’adu (RA) ya yi nasihohi da dama ga ’ya’yansa daga ciki akwai: “Ya ku ’ya’yana! Duk abin da za ku nema a wurina ya zamo daidai da abin da ya kamata ne, domin Allah ba zai yi farin ciki da wanda ya ki amsa neman taimakon mai bukatar taimako ba. Ya ’ya’yana! Kada guji jiji da kai, ku rika tunanin yadda rayuwarku ta fara da yadda za ku kasance bayan mutuwa. Duk mai girman kai Allah zai nuna masa iyakarsa. Ya ’ya’yana! Ku guji hadama, domin ita ce babbar talauci a wannan rayuwa ta duniya.” 

Sa’adu ya koma ga Allah:

Sa’adu bin Abu Wakkas (RA) ya koma ga Allah ne a shekara ta 54 Bayan Hijira yana da shekara 86. A’isha (RA) ta ce: “A lokacin da Sa’adu ya rasu matan Annabi (SAW) sun aika a shigo da gawarsa ta cikin masallaci don su sallace shi, sai aka yi hakan su ma suka sallace shi, aka fitar da shi ta kofar Jana’ina da take a Maka’id. Da labari ya isa ga mutane sai suka yi suka da maganganu game da hakan, (suka ce wannan bidi’a ce), don ba a shigar da gawa cikin masallaci. Sai Nana A’isha (RA) ta ce: “Ta ji mamakin mutane da suke saurin zargin abin da ba su sani ba, sun zarge mu don shigo da gawa ta cikin masallaci. Na rantse da Allah, Manzon Allah (SAW) bai sallaci Sulhu dan Baida’u da dan uwansa ba, face a cikin masallaci.” Muslim ya ruwaito.

Kafin rasuwar Sa’adu ya ba da umarnin a bude wani akwatinsa da ya dade a rufe inda aka samu wata tsohuwar riga a ciki, ya bayar da wasiyyar a lullube shi da rigar idan ya rasu domin rig ace da ya sanya a fagen jihadi, ya yaki mushirikai a Ranar Badar, kamar yadda dabarani ya ruwaito.

A n binne shi a Baki’a da ke Madina birnin Manzo (SAW).

Wannan shi ne kadan daga abin da muka tsamo daga dogon tarihin rayuwar Sayyidina Sa’adu bin Abu Wakkas.  


Za a iya samun Ustaz Aliyu Gamawa ta tarho: 08023893141, 08035829071

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos