Abin na yi ne

Gwanayen magana na cewa, ma-so-abinka ya fi ka dabara. Wannan batu haka yake, domin kuwa ga shi nan miyagun mutanen da suka hana jama’ar kasar nan sakat, musamman ma na yankin Arewacin kasar  nan, kuma a  Shiyyar Arewa-maso-Yamma, sun sake dabarun ganin cewa jami’an tsaro na kuntata musu, sun hana su walawa da kuma cin […]

Abin na yi ne
Abin na yi ne

Gwanayen magana na cewa, ma-so-abinka ya fi ka dabara. Wannan batu haka yake, domin kuwa ga shi nan miyagun mutanen da suka hana jama’ar kasar nan sakat, musamman ma na yankin Arewacin kasar  nan, kuma a  Shiyyar Arewa-maso-Yamma, sun sake dabarun ganin cewa jami’an tsaro na kuntata musu, sun hana su walawa da kuma cin karensu babu babbaka. A yanzu haka mutanen babban birnin Jihar kaduna na zaman dar-dar ne saboda yadda miyagu ke kukkutsawa cikin gidajensu da tsakar dare su tattashe su firgigi, sa’anan su aikata dukkan kaba’iran da suke  so a cikin gidajen, ba tare da wani daga waje ya kawo masu dauki ba. Haka nan kuma  barayi na sheke ayarsu yadda suka ga dama idan sun firfito don gudanar da muguwar sana’arsu. Sukan sassari wanda duk suka ci karo da shi da tsakar dare, walau mutumiun kirki ne shi ko kuma tafiyarsu guda da shi. Abin mamaki game da haka shi ne yadda suke samun sukuni, suna kukutawa, suna aiwatar da waccan muguwar manufa ta su, duk kuwa da cewa jami’an tsaro na iyakar kokarinsu na yin sintiri a lunguna da sako-sakon  birane da kauyukan jihar.
Ko a  ‘yan makwannin da suka gabata ma sai da barayin bil-adama suka shiga rugagen Fulani a wasu yankunan karkarar Jihar Kaduna,  amma ba domin su sak shanunsu ba, sai dai don su aikata ta’asar da za ta  ba su damar samun kudi cikin ruwan sanyi, ta hanyar cafke ardon garken, a kuma tafi da shi don zuriya da danginsa su sayar da shanunsa a kasuwanni hankali kwance, su biya kudin fansarsa, kafin a sako shi. A yankin kananan hukumomin Zariya da kuma Chikun,  barayin sun caccafke wasu mata masu karancin shekaru, suka yi awon gaba da su, kuma ba wanda zai iya cewa ga abin da ya biyo bayan hakan, kafin jami’an tsaro na Operation YakI su kwato su, amma ba su kamo wadanda suka kakkame su ba. Wannan al’amari ne da ya sa makiyaya da Fulanin daji ke kwana idonsu da ya a bude, da ya kuma a rufe, cike da zullumin abin da kan iya afkuwa a gare su, da kuma irin bakar wahalar da za su iya kamuwa da ita idan har an cafke su, kafin dangi su biya kudin fansa, ko jami’an tsaro su tserar da su daga halaka.
To amma  idan har za a dinga sassace magidanta da matan aure  gaban mazajensu da kuma ‘ya’yansu   cikin sauki, akwai babbar matsala, kuma hakan wata alama ce da ke tabbatar da cewa lalacewar ta kai intaha. baicin haka nan kuma hakan ya nuna mana irin kwarewar da  barayin suka yi ne wajen gudanar da muguwar sana’arsu, domin kuwa sukan fita, su aikata ta’asa  son ransu, ba tare da jami’an tsaro sun gano su ba, har sai sun kammala bidirinsu, sun kuma kai ga wurin da suke son aikata tsiyar tasu, ko ga  wanda suke son sacewa  ko da kuwa yana cikin runtsin jama’a ne, ko a tsakiyar rukukin ababen hawa, a titin da ake ta hada-hada ba kakkautawa, walau da tsakiyar dare ko tsakar rana. Babban abin da ya fi tayar da hankulan jama’a game da haka  shi ne hatta ma a lokutan da jami’an tsaro kan taimaka don ceto wanda aka sace, sai an biya kudin fansa, sa’annan daga bisani za a sako wanda aka kame, jami’an tsaron kuma su ce su ne dai suka kwato shi daga hannun miyagun.
‘Yan Najeriya dai, musamman ma na Arewa, na nuna matukar damuwarsu game da yadda barayin bil-adama ke sheke ayarsu yadda suke so a kauyuka da kuma cikin lungunan yankunan karkara, kuma ‘yan Najeriya na damuwa matuka game da yadda ake kakkame ardodin Fulani da zuriyarsu. Yanzu a ce duk da yawan kayayyakin sadarwa irin na zamani da kuma yawan kamfanonin da ke wannan aikin a kasar nan amma sai ga shi sun gaza wajen taimakawa jami’an tsaro iya gano sawun barayin bil-adama ta yadda za su iya kai wa ga maboyarsu? Ya dai kamata jami’an tsaro su tashi haikan wajen saukake wa jama’an da suke aiki domin su wadannan wahalhalu da matsalolin da barayin shanu da na bil-adama da kuma masu farfafsa gidaje ke haifarwa.
Baicin haka nan kuma sai a waiwayi al’ummomi da shugabanninsu da su matsa kwarai wajen tona asirin wadannan barayin, domin kuwa ba fatale ne ba, kuma ba daga sama ne suke fadowa ba, a cikin jama’a suke zaune, kuma da su ake kwana, ake tashi. Tun da kuwa har ka fara da satar shanu da kuma kakkame ardodin Fulani da matansu, ana karbar kudin fansa kafin a sako su, to sai a guji yiwuwar kasaitar wannan dabi’a ta yadda cikin dan kankanen lokaci za ta buwayi kowa da kowa, harkokin arziki su tsaya cik, zumunci ya gagara, sa’annan kuma uwa-uba ibada a masallatai da mujamu’u ta faskara. Wajibi ne fa jama’a su san cewa su ma suna da hakki wajen kawo karshen wadannan fitintinun, kuma tilas ne su dinga fitowa fili suna tona asirin wanda duk ke da hannu wajen haddasa wadannan masifun.
Su kuma gwamnatocin da ke fadi-tashin ganin an shawo kan wadannan munanan al’amurran sai su dage wajen daukar matakan hana afkuwarsu maimakon  hankoron magancewa a banza, a lokacin da abubuwan suka kasara, suka nemi buwayar kowa. Abubuwan da ke haddasa  wadannan miyagun dabi’un kuwa ba su wuce rashin aikin yi da ke janyo bakar fatara da mayata ba, kuma  wadannan ne hujjojin da miyagun mutane ke dogaro da su yayin aikata munanan aikace-aikacensu. A yanzu dai ana iya cewa abin na yi ne game da yakin da ake yi da barayin bil-adama tun da dai  tura ta kai bango game da  satar jama’a,  ganin yadda  mutanen banza da ke hana kowa zama lafiya a kasar nan. A yanzu dai masu hali da attajirai, ko wadanda ke rike da wani mukami ba su iya watayawa, ko su saki jiki su gudanar da sha’aninsu na zumunci ko na kashin kansu a wuraren da suka kamata, kowa na dari-dari da  tsoron kada ya ji an cafke shi, an yi awon gaba da shi, an cusa shi cikin ukuba ba shiri ko sanannen ciki, har sai an fitar da wasu muliyoyin Nairori kafin ya samu kansa, hankulan ‘yanuwa da na  abokan arzikinsa kuma su kwanta. Mafita daga wannan mummunar dabi’ar ita ce ta kakkame ma’abotanta ba wai biyan kudin fansa don sako wanda aka kama ba, Idan kuwa haka ne, to ba ta yadda za a yi a kawo karshenta, domin kuwa barayin shanu da na  bil-adama sun huda, sun kuma ga jini.