Abin sa’a ne, jifan kuda da gatari

Tsokaci, game da nasarar da dan takarar jam’iyyar hamayya wato Janar Muhammadu Buhari ya samu, a zabukan da suka gudana a kasata Nijeriya.Hakika wannan abin alfahari ne, ganin yadda ya shafe shekaru goma sha biyu yana neman dare kujerar mulkin Nijeriya, wanda sai a karo na hudu da ikon Allah, ya samu nasarar hakan.Kirana ga […]

Abin sa’a ne, jifan kuda da gatari
Abin sa’a ne, jifan kuda da gatari

Tsokaci, game da nasarar da dan takarar jam’iyyar hamayya wato Janar Muhammadu Buhari ya samu, a zabukan da suka gudana a kasata Nijeriya.Hakika wannan abin alfahari ne,

ganin yadda ya shafe shekaru goma sha biyu yana neman dare kujerar mulkin Nijeriya, wanda sai a karo na hudu da ikon Allah, ya samu nasarar hakan.Kirana ga al’ummar kasata baki daya shi ne, mu dage wajen addu’ar Allah ya taya shi rikon wannan babban nauyi na al’ummar kasa da ya rataya a wuyansa, shi da maitaimakinsa wato Farfesa Yemi Osinbajo.Ganin cewa mu talakawan Nijeriya mun shafe sama da shekaru goma muna addu’ar Allah ya kawo mana karshen jam’iyyar PDP da ta gallaza mana bakar azaba a matakan gwamnati daban -daban, nake kara shawartar ‘yan kasa da kada mu gajiya wajen yi wa sabuwar gwamnati addu’ar Allah ya sa ta jikan talaka ta share wa ‘yan Nijeriya hawayensu.Haka kuma, mu yi wa Baba Buhari addu’ar Allah ya hada shi da wakilai mutanen kirki a duk matakan ci gaban kasar nan.
Daga karshe nake kara jinjina ga al’ummar Nijeriya musamman talakawa ganin yadda suka jajirce wajen kada gwamnatin da ba talakawa ne suke gabanta ba, nake kuma jinjina ga wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar APC wadanda suka yi kokari na ganin an samu canjin gwamnatin PDP mai gana wa talakawa azaba, irinsu Ahmadu Bola Tinibu, Bisi Akande, Rochas Okorocha, John Oyegun, Rotimi Amechi, Rabi’u Kwankwaso, Faruk Adamu Aliyu, Hakim Baba Ahmad, da daukacin gwamnonin APC na kasa baki daya.
Haka kuma ina yaba wa shugaba mai barin gado wato Goodluck Jonathan saboda kokarin taya murna da ya yi wa Baba Buhari don tabbatar da dimokuradiyya da ci gaban kasa.Ina kuma jinjina ta karshe ga hukunar zaben Nijeriya mai zaman kanta wato INEC da shugabanta Farfesa Attahiru Jega saboda kokarin kamanta adalci da da suka yi, wanda mu ‘yan kasa da dukkan duniya mun yi na’am da sabon takun nasu.

Aliyu Ibrahim Shariff
Gashuwa, Yobe
08136153181
07014256996

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu