Abin takaicin da ke faruwa a Sudan Ta Kudu
A ’yan kwanakin nan ne rikice-rikice suka barke a kasar Sudan Ta Kudu, kasar da dududu shekararta biyu da samun ’yancin kai. Kafin barkewar rikice-rikicen, an jiwo Shugaban kasar, Salba Kiir yana bayanin cewa mataimakinsa, Riek Machar ya yi yunkurin yi masa juyin mulki.Ya zuwa yanzu dai, rikice-rikicen sun koma na kabilanci, inda aka samu […]
A ’yan kwanakin nan ne rikice-rikice suka barke a kasar Sudan Ta Kudu, kasar da dududu shekararta biyu da samun ’yancin kai. Kafin barkewar rikice-rikicen, an jiwo Shugaban kasar, Salba Kiir yana bayanin cewa mataimakinsa, Riek Machar ya yi yunkurin yi masa juyin mulki.
Ya zuwa yanzu dai, rikice-rikicen sun koma na kabilanci, inda aka samu rahoton kisan mutane sama da 500. Akwai ma labarin da ya tabbatar da cewa an kai hari wani gida mallakar Majalisar dinkin Duniya da ke Juba, inda aka kashe Indiyoyi biyu ’yan aikin ceto, tare da dozin-dozin na sauran mutane da ake ba kariya a gidan. Rikicin dai yana da alaka da adawar da ke tsakanin rundunar sojojin kasar ’yan kabilar Dinka da Nuer, a karkashin mulkin jami’iyyar SPLM. Rikicin ne ya warwatsu zuwa sauran jihohin kasar, inda ma babu wadannan kabilun biyu.
Rikicin dai kamar yadda ya fito sarari, ya samo asali ne daga furucin Machar, wanda ya shata daga, ya ce ba zai kara yin mubaya’a ga mulkin Kiir ba. A yayin da zabe ke karatowa a 2015, hadin kan kasar na kara rarrabuwa, inda tuni shi Machar ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a tutar jam’iyyar SPLM.
A watan Yulin da ya gabata ne Shugaba Kiir ya kori mataimakinsa da wasu ministocinsa da kuma Sakatare-Janar na SPLM. Haka kuma ya kori gwamnonin jihohin Lake da na Unity, wadanda ke goyon bayan Machar.
Tun da farko dai, Machar ya bayyana gazawar mulkin Kiir ta bangare hudu, wanda dalili ke nan ya nemi ya sauka, kafin a sake sabon zabe. Laifukan sun hada da gazawar shugaban wajen yaki da almundahana da dukiyar kasa, gazawarsa wajen magance talauci, gazawarsa wajen magance matsalar tsaro da kuma yadda ya kasance mai mulkin kama-karya waje zartar da al’amuran kasa.
Kiir dai ya yi ikirarin cewa ya kwato Dala biliyan 40 daga barayin ma’aikatan gwamnati, inda su kuma wadanda aka tuhuma suka dauki batun cewa ana yaki ne da kabilarsu, domin kawar da ita daga cikin gwamnati.
A garin Bor, a yayin da jirgin helkwafta na Majalisar dinkin Duniya ke sauka da nufin ceto ’yan Amurka, sai aka bude masa wuta, aka lalata shi. Hakan ya kara ruruta wutar rikicin, ake kallonsa a matsayin na kabilanci, kamar kuma yadda ya kara nuna cewa gwamnatin ta gaza wajen magance matsalar tsaro a kasar baki daya.
Wannan abin takaici ne da ke faruwa a jaririyar kasa kamar Sudan Ta Kudu, inda ba a dade ba da kafa gwamnatin dimokradiyya. Wannan ya nuna cewa gina kasa a siyasance abu ne mai wahala, kamar kuma yadda gina kasa bayan shudewar shekaru na yakin basasa yake da matukar wahala. Ga shi kuma yanzu rikice-rikice sun kaure a kasar, wanda haka ke nuna cewa al’amarin gina kasar zai zama mai matukar wahala, kamar yadda Majalisar dinkin Duniya da kungiyar Hadin Kan Afrika za su fuskanci matukar wahala wajen sasanci da samar da zaman lafiya.
Yukurin nan da gwamnatoci suka kaddamar na samar da zaman lafiya a AfrikaTa Gabas, abin a yi marhabin da shi ne, musamman ga bangarorin biyu. kasashe kamar Najeriya da Senegal da Kenya da Uganda da Afrika Ta Kudu, wadanda suka tsaro shirye-shirye masu tasiri na samar da zaman lafiya, ya kamata su taimaka wa Sudan Ta Kudu, domin ta gina shika-shikan gina kasarta da dimokradiyya mai karfi, ta hanyar hada kan dinbin kabilu da dinbin mabiya mabambantan addinai daban-daban, kamar kuma yadda za ta samu daidaito wajen bunkasa tattalin arzikinta, wanda ya bambanta daga shiyya zuwa shiyya.
Ya dace a ba jam’iyyar SPLM goyon baya, a yunkurinta na gudanar da babban taron hada kan kasa da kuma yunkurinta na samar da sabon kundin tsarin mulki ga kasar; domin kuwa bai kamata wadannan yunkure-yunkure su zama kafofin kawo baraka da tashin hankali ba. Gwamnatin Sudan Ta Kudu ta tabbatar da ta ba da kariya ga dukkan kabilun kasar, bisa doka.
Ya kamata kada a sake a ji wani batu na jiyin mulki. Idan ma har akwai wannan yunkuri kamar yadda ake batu, to lallai kam al’amari ne da ya kamata a yi Allah-wadai da shi da kakkausar murya.
Burin samar da kasa mai hadin kai da zaman lafiya shi ne ya kamata ya zama burin kowa a Sudan Ta Kudu. Shugaba Kiir ya dauki matakin da ya dace, lokacin da ya ce a shirye yake ya tattauna da Mista Marchar, domin ganin an magance dukkan rikice-rikicen da suka mamaye kasar. Ya dace Mista Marchar ya ba da hadin kai, kada ya zama karkataccen gora, da zai kawo matsala ga samar da zaman lafiya.