Abin tsoro dangane da daminar bana

Masana sun ce idan aka ci gaba a haka, akwai babbar barazana

Abin tsoro dangane da daminar bana

Manoma

Zuwa wannan lokaci da muke mako na karshe a watan Yuli, wanda ke cikin watannin ruwa, har yanzu daminar bana ba ta kankama ba a wurare da dama a wasu sassan Arewa.

Wannan wani abu ne da yake da matukar ban-tsoro da firgitarwa. Fiye da kashi biyu cikin uku na manoma a Najeriya sun dogara da ruwan damina ne wajen noma amfanin gona musamman hatsi wanda shi ne abincin galibin mutanen Arewa da Najeriya baki daya.

Garuruwa da dama musamman wadanda suke Gabashin Arewa sun yi shuka amma shukar ta gaza mikewa saboda rashin isasshen ruwan da shukar take bukata. Wannan rashin ruwa, ya sa masu martaba sarakunan Borno da Bauchi da Gombe cikin kankan da kai ga Allah sun fita bayan gari rokon ruwa.

Za mu iya cewa abin ya ta’azzara sosai a wadancan jihohin, haka mun ji Mai martaba Sarkin Kano ma yana kira ga malamai da limamai su dukufa da addu’a a kan Allah Ya ba mu damina mai albarka Ya kuma shayar da gomakan manomanmu ruwa wadatacce kuma mai albarka.

A shekarun bayan lokaci irin wannan, za ka samu damina ta yi harshe, tun kafin zuwan watan Agusta, wanda Bahaushe ke masa lakabi da watan marka-marka. Amma a bana abin ba haka yake ba, muna watan Yuli amma da yawa manoma suna tsoron amfanin gonarsu ba lallai ya kai ba idan ruwa bai wadata ba.

Haka kuma, karin abin tsoro shi ne kada ruwan ya sauko da yawan da zai cinye gonaki da amfanin gona da garuruwa da dama, kamar yadda hasashe ya nuna cewa za ayi mamakon ruwan sama a daminar bana, kuma zai ci garuruwa da yawa a fiye da jihohi 20 na Najeriya. Wannan babban abin fargaba ne da tashin hankali idan ruwan ya zo lokaci guda kuma da yawa, wanda hakan zai sa a iya asarar amfanin gona.

A bara, mun ga yadda aka samu asarar amfanin gona a jihohi da dama musamman a jihohin Kebbi da Neja da Jigawa da sauran jihohin Arewa da dama da suka yi fice wajen samar da amfanin gona.

Masana da dama suna ta bayanin yadda daminar bana za ta zo da mamakon ruwa a kusan daukacin jihohin Najeriya har ma suna kira mutane su kaurace wa yankunan da suke zaune zuwa tudu musamman a jihohin Nasarawa da Neja da Binuwai da Kwara da kuma Kogi.

Dama dai sanin kowa ne jihohi irin su Kogi sun shahara da samun ambaliyar ruwa duk shekara, inda ruwa ke kusan shanye babban birnin jihar Lakwaja da sauran garuruwan kusa da birnin. Sauyin yanayi da dumamar yanayi da ake samu musamman daga manyan kasashen duniya da suke da arzikin masana’antu, an ce su ne suke sabbaba sauyin yanayin da kan kawo ambaliyar ruwa da samun tsananin zafin rana a wasu sassan duniya.

A wannan lokaci an ce wasu daga cikin kasashen Turai suna fuskantar yanayin zafi wanda ba su taba gani ba a tarihi. kasashen Spain da Italiya na daga cikin kasashen da suke fuskantar matsanancin zafin rana a wannan lokaci, lamarin da ya kai hatta hukumomi sun bayar da hutun makaranta saboda zafin.

Haka a kasar Indiya an ce mutane na cikin tafiya sai su yanke jiki su fad saboda tsananin zafin rana. Hatta a kasa Mai tsarki akwai lokacin da malamai suka yi fatawar kada mutane su fito Sallar Juma’a kuma su tsaya a cikin rana. An yi ta jan hankalin alhazai su kaurace wa shiga rana a lokacin zawali su zauna a gidajensu har zuwa lokacin da zafin rana zai yi sauki.

Dama sanannen ne cewa kasashen Gabas ta Tsakiya suna fama da matsanancin zafin rana a irin wannan lokaci, amma abin da ya fi ba da mamaki shi ne kasashen Turai da suke fama da tsananin sanyi na fiye da wata bakwai a shekara amma a bana an samu tsananin zafin rana.

Wannan duk yana faruwa ne sakamakon sauyin yanayi da ake samu, wanda a cewar masana yana da alaka da dumamar yanayi da ake samu daga hayakin masana’antu na kasashen da suka ci gaba ta fuskar tattalin arziki musamman kasashen guda takwas ko 20 in an fadada, wadanda su ne suka fi sauran kasashe ci gaba ta fuskar masana’antu da fitar da hayaki zuwa sararin samaniya wanda yake illa ga ‘Ozone layer’ wani bargo da aka ce ya lullube duniya.

Wannan hayakin masana’antu bayanan kimiyya sun tabbatar da cewa yana huda wancan bargo na ozone layer wanda a sanadinsa ake samun tsananin zafin rana da ke sauko da cututtuka da sauyawar yanayin da kan shafi damina a kasashen duniya. Mu Najeriya ba mu daga cikin manyan kasashen da suke samar da irin wancan hayaki da ke gurbata yanayi.

Sai dai gurbatar yanayin da wasu kasashe suke samarwa na shafarmu kai-tsaye kamar yadda ake fada a kimiyyance. Amma mu Musulmi mun yi imani cewa akwai abubuwa da yawa da suke faruwa a duniyar yau wadanda yawan sabon Allah ya kawo su, kuma samun warakarsu na bukatar mutane su koma zuwa ga Allah a yi ta neman gafara da sauyawa daga munanan ayyukan da bayi suke yi zuwa ga kyawawan ayyukan alheri da neman yardar Allah a kansu.

Babbar barazanar da wannan damina take tafe da ita ita ce, za a samu karancin abinci, wanda kuma shi ne zai dada jefa al’umma a cikin bala’in yunwa da fatara. Dama ga shi muna fama da wani irin lokaci na tsadar kayayyaki da tsadar man fetur ta dada, inda kusan dukkan kayan masarufi suka kara kudi wasu ma suka ninka ninkin-ba-ninkin.

Lallai akwai bukatar al’umma gaba daya a tashi a dage da rokon ruwa mai albarka, a kuma nemi duk amfani da hanyoyin kariya daga ambaliyar ruwa. Kuma a bana musamman a jihohin Kebbi da Jigawa da wasu jihohi an samu annobar wasu tsuntsayen jam-baki wadanda suke cinye amfanin gona.

Muna fata Allah Ya yaye mana wadannan masifu Ya kuma ba mu damina mai albarka. Muna kuma fata sauran sarakuna za su bi sahun sarakunan Borno da Bauchi da Gombe wajen fita rokon ruwa tare da neman Allah Ya shayar da mu ruwa mai albarka, Ya sa daminar bana ta yi harce, mu yi ta addu’a laifuffukan da muke yi Allah Ya yafe mana su Ya kuma tausaya mana Ya shayar da mu ruwa mai albarka a wannan damina. Allah Ka yaye mana firgici da damuwa, Allah Ka wadata mu da arziki mara yankewa. Amin.

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025

Za a rataye shi saboda kisan jariri

Kirsimeti: Gwamnati ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa