‘’Yan gida daya sun mutu bayan cin abinci’
Ana zaman zullumi a garin Benin na Jihar Edo game da mutuwar mutum bakwai ’yan gida bayan sun ci abinci. Mazauna sun ce iyalan da ke zaune a Layin Masaka a Unguwar Ogida, sun ci abin ne da dare kafin su kwanta amma ba a wayi gari da su ba. Wakilinmu ya ziyarci gidan amma […]
Ana zaman zullumi a garin Benin na Jihar Edo game da mutuwar mutum bakwai ’yan gida bayan sun ci abinci.
Mazauna sun ce iyalan da ke zaune a Layin Masaka a Unguwar Ogida, sun ci abin ne da dare kafin su kwanta amma ba a wayi gari da su ba.
Wakilinmu ya ziyarci gidan amma ya iske babu kowa sai masu ta’aziyya daga wajen gidan, inda wata daga cikinsu, Rachel Anyanwu, ta ce sai da aka balla gidan kafin a kai wa mutanen dauki kuma ana tunanin sun ci guba ne a abinci.
“Matar mai gidan ta rasu ranar Lahadi, yau kwana biyar ke nan. Wadanda ke asibiti ’ya’yansa ne da masu zaman makoki”, inji ta.
- Za a rataye mai yaudarar mata yana kashe su
- An rufe hanya saboda zaben Gwamnan Ondo
- Cincirindon masu kallon Sarkin Zazzau
Makwabciyar gidan, Christy Igbinadolor, ta ce ta ji labarin lamarin ne bayan wani mutum ya tambaye ta abin da ke fauwa.
Ta ce mutumin ya shaida mata cewa wansu ne daga Fatakwal ya kira shi ta waya cewa ya je gidan ya gani ko lafiya saboda yana ta kiran su a waya ba sa dauka.
Christy ta ce daga nan sai suka shawarci bakon da ya kwankwasa kofar gidan, idan ya ji shiru sai ya sanar da ’yan sanda.
Ta ce ko da ’yan sanda suka balla gidan sun tarar da ’yan gidan ba sa motsi amma suka garzaya da su zuwa asibiti.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Chidi Nwanbuzor, ya ce ba shi da cikakken bayanin abin da ya auku.
Wata majiyar ’yan sanda a Jihar da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce hayakin janareton da mutanen suka kunna ne ya yi sanadiyar hakan.
Majiyar ta ce mutum daya ne ya rasu sauran kuma na samun sauki a asibitin da aka kai su.