Abinci Ya Yi Ajalin Mutum 1 Wasu 75 Na Asibiti A Saudiyya
Wani mutum ya gamu da ajalinsa wasu 75 kuma an kai su asibiti bayan cin wani abinci da ake zargin gurbatacce ne a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya. Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta fitar da sanarwar iftila’in sai dai bata fitar da sunan wurin da mutanen da abin ya shafa suka ci abincin ba. Rahotanni […]
Wani mutum ya gamu da ajalinsa wasu 75 kuma an kai su asibiti bayan cin wani abinci da ake zargin gurbatacce ne a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya.
Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta fitar da sanarwar iftila’in sai dai bata fitar da sunan wurin da mutanen da abin ya shafa suka ci abincin ba.
Rahotanni daga kafafen sada zumunta na cewa mutanen sun ci wata waina ce daga wani babban Kantin da ke Riyadh.
Kawo yanzu dai ma’aikatar ta bayyana cewa, ‘yan kasar Saudiyya 69 ne abin ya shafa, sai kuma wasu baki guda shida wadanda ba ‘yan asalin kasar Saudiyya ba ne ke fama karbar magani sakamakon cin abincin da ake zargin akwai kwayoyin cuta Clostridium botulinum a ciki.
- Dagacin Abuja ya mutu a hannun ’yan bindiga
- Bankuna za su fara cirar 0.5% daga masu tura kudi ta intanet
An ce, akalla mutane 43 daga cikin waɗanda suka ci abincin sun samu sauki kuma an sallame su daga asibiti, yayin da wasu 11 ke jinya a halin yanzu.
A halin da ake ciki, akwai wasu mutane 20 da ke cikin mawuyacin hali a sashin kulawa ta musamman a asibiti sakamakon gubar abincin.
Sakamakon binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa daga gidan abinci guda ne duk wadanda abin ya shafa suka sayi abincin.
Hukumar birnin Riyadh ta kulle gidan abincin da ake zargi, sai dai ba su bata tabbacin yaushe za a bude shi ba.
Amma sun tabbatar da cewa za su bi dukkan ka’idojin da suka dace wurin tsaftace wuraren cin abinci mallakar wanannan kamfanin kafin a bude shi; Kamar yadda kafar yada labarai taAl-Arabiyya ta ruwaito.