Saura kwana 4 a rasa abinci a Gaza —MDD
Ofishin Shirin Abinci ta Duniya (WFP) ya ce abincin da ya rage shaguna da sauran wurare a Zirin Gaza bai wuci na amfanin kwanaki hudu zuwa biyar ba
Majalisar Dinkin Duniya ta ce nan da kwana biyar Falasdinawa da ke Zirin Gaza za su rasa abinci gaba daya.
Ofishin Shirin Abinci ta Duniya (WFP) ya sanar cewa a halin da ake ciki yanzu, abincin da ya rage shaguna da sauran wurare a Zirin Gaza bai wuci na amfanin kwanaki hudu zuwa biyar ba.
“Shaguna sun fara rufewa saboda kaya sun kare, yanzu abin da ya rage musu ba zai wuce kwana biyar ba,” in ji kakakin WFP a yankin Gabas ta Tsakiya, Abeer Etefa.
Sanarwar tana zuwa ne a yayin da Isra’ila ta tsafe kwanaki takwas tana luguden wuta a Gaza, yankin da ta hana shiga da fitar abinci, ta kuma yanke ruwan sha da wutar lantarki da man fetur da sauransu.
Kungiyar kasashen Larabawa ta yi kira ga Isra’ila da ta gaggauta ficewa daga Gaza, inda sojojin Isra’ila suka kashe Falasdinwa kimanin 2,000.
Kungiyar Falasdinawa ta Hamas dai ta bayyana cewa babu abin da zai girgiza ta da barazanar da Isra’ila ke yi na shiga Gaza da dakarun kasa, inda kungiyar ta ce a shirye take ta lallasa sojojin yahudun.