Abincin masu ciwon siga (Alalen Zogale)

Assalamu alaikum Uwargida, yaya yara? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Ciwon siga na daya daga cututtukan dake samun mafi yawancin mutane wadda idan ciwon ta kama mutum sai an kayade masa irin abincin da zai iya ci, domin samun waraka daga wannan cutar. Ganin yadda masu karatu ke korafin cewa ya kamata suma […]

Abincin masu ciwon siga (Alalen Zogale)

Assalamu alaikum Uwargida, yaya yara? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Ciwon siga na daya daga cututtukan dake samun mafi yawancin mutane wadda idan ciwon ta kama mutum sai an kayade masa irin abincin da zai iya ci, domin samun waraka daga wannan cutar. Ganin yadda masu karatu ke korafin cewa ya kamata suma a rika rubuto musu irin nasu abincin, domin ba komai suke ci ba, shi ya sa a yau na kawo muku yadda ake yin Alalen zogale. Wadanda ba su da ciwon suga ma za su iya cin wannan alalen domin samun sinadaran da girkin ke dauke da su ko  sun bi lafiyar  jiki.

Abubuwan da ake bukata

• Wake

• Zogale

• Albasa

•Tafarnuwa

• Attarugu

•Tattasai 

•Magi

•Kori

•Man ja

Hadi

A wanke wake sannan a zuba tattasai da attarugu kadan da albasa da kuma danyar tafarnuwa, sannan a kai a markada a injin din markade. Bayan an nika, sai a soya manja da albasa a zuba a cikin kullun waken sai a zuba magi a cikin ruwan zafi a jira ya narke sannan a zuba a kullun. 

A dauko zogale danyensa ba busassa ba, sannan a tsinka a wanke sai a zuba a cikin kullun. Ganyen zogalen ya kasance isasshe. A gauraya a dan zuba ruwa kadan sai a sake gaurayawa, sannan a samu kwano a shafeta da manja a zuba kullun.

A daura ruwa a wuta idan ta tafasa, sai a zuba wannan kwanukan da aka zuba kullun a cikin tukunyan ruwan zafi sannan a rufe. A jira na tsawon mintuna arba’in kafin a sauke.

Za’a iya cin wannan alalen zogalen da yaji da manja. A ci dadi lafiya.